← Book details Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 24

Sashe 14

Mijin Ta Ce Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

89
abin dai kawai a wurina shi ne duk kokarin Mama ta
kasa shiga tsakanin Kawu Ado da Innata ta 6ata.
Tayi-tayi abin ya gagara, tayi juyin duniya ta rasa
yanda zata yi, bata ma kara tsinkewa da al'amarin ba
ta kara tsorata dashi sai a lokacin da Adon ya
zartarwa Sa'a hukuncin aurar da ita ga babban
amininshi Barrister Tukur Usman.
Wanda yasan Sa adatu tana da saurayin da take
So bai ma tsaya wajen yin shawara da kowa ba, izini
kawai yaje ya nema a wurin Baba.
Sai kaWai ya fadi daurin auren kowa yaji, Mama
tayi bakin ciki kanar zata mutu ta tasa shi a gaba
tana kuka ga Suwaiba shekara da shekaru babu aure,
ka samo mutumn mai muhimmanci irin wannan ka
dauki wata Sa'a ka bashi don dai kai sun shanye ka
ba ka ganin kowa ba ka son kowa sai su?
Ya ce ba samo shi nayi ba Manma Aminina ne yya
kuma yi min kukan matsalolin gidanshi ne ya roke ni
in ina da wata "yar da na san me tarbiya ce in yi
mishi hanayrta yana so.
Kin ga kuma yana cikin damuwa ba zan kara
mishi damuwarshi ba, ban yi mishi adalci ba in nayi
mishi hakan.
Yanzu ita Sa'a ba damuwa bace sai Suwaiba?
Yarinyar da bata son auren ban ganta tana yin kuka a
gabanka ba, yayi murmushi ya ce ai iyakar dai abinda
zata yin kenan Mama.

90

Ba za a kai ta gidanshi ta ki bin umarninshi ba,
be za te je tayi mishi rashin kunya ko wulakanci ba,
ba za taje ya ce mata yi ta ki yi ko bari ta ki bari ba,
sabods du a dakinsu uwarsu tana da tasiri mai karfi
akan 'ya'yanta.
Tana kuma da halin girma nayi wa surnıki adalci,
ni kadai nasan irin taimakon da tayi min akan aurena,
su Suwaiba kuwa ba haka suke ba Mama, ina jin ta
rannan tana gaya miki ko taje gida bata gaida
Babansu ko kallonshi bata yi, saboda bata da
lokacinshi.
Shiru kawai nayi muku, to yaushe zan dauke ta
in baiwa wani? In dai ba so nake in taje tana
w&stsakewa daga halin rashin mijin da take ciki ba ta
Soma cin mutuncinmu ni dashi.
Shi yasa na barta ta kawo shi ita da kanta, kayan
dakin dai zan bayar.
Hidima ta ban mamaki Ado ya yi wa Sa'adatu, a
lokacin auren nata irin hidimar da ko auren su
Umahmah ya tashi yi in yayi haka ya ci a yaba mishi.
Magana guda daya da ya gayawa Sa'adatu a
ranar da za'a kaita gidan mijin nata kuma ita ce dai ta
gamsar da ita tayi amfani da ita aka samu zaman
lafiya da kwanciyar hankalin da ake nema bai taba
kawo karanta wurin Adon ba balle maganar ta wuce
ta kai ga Innarmnu.
Maganar kuwa ita ce hukunci na zartar miki Sa'a

91
irin wanda uba ne kadai ke da ikon yiwa 'yarshi
hakan in har anyi mata tarbiyar da ta dace da ita duk
kuwa da ni din ba mahaifinki ba ne, na kuma san
hakan sai dai nasan ke din yarinya ce da aka yi wa
tarbiyar sanin darajar na gaba.
Na kua san ina da gira da mutunci a wunnki sai
nake ganin kamar ba zan yi iko dakc kiyi sanadin da
zan tozarta wurin mutuin da nake da kima a wurinshi
ba, don haka in kin ji ku zauna lafiya.
Shekaru biyu kenan da yin auren Sa'a ta haifi
danta Adam, har sun yi aikin Haji ita da Inna tare ya
biya musu suka tafi babu wanda ya taba jin wata
magana surukuta mai dadi suke yi shi da Ado.
Ire-ircn irin wadannan al'amuran sune suke kara
sanya ni hakuri da kokarin danne zuciyata a kan
al amura masu yawa ina kawar da ido akansu.
Amma duk da haka wani abin kure hakuri ake yi,
saboda a hali irin nawa halin da kullum Inna ke yi
min kirarin rashin hakuri a kan shi sai in rinka ganin
bai dace in yi hakuri da dole in kuma yi da abinda bai
zame tnin dole ba.
Dawowan Mama gidan Ado yayi dalilin da itama
Suwaiba ta dawo gidan da zama don ta ce ba za ta iya
ZAInan gidan ubanmu ba, in kuma da mutumin da ke
taimakon Mama kina a zahiri to Suwaiba ce.
Kan ya' yana a hade yake, don ko da sun yi
wayon sanin 1yayensu tun kan mu taso to a zaman da

92

ake yi dai kansu a hade yake, don ba a bambanta su
da komai ba, komai tare ake musu, suma duk abin da
zasu yi tare suke yi ba su da wata matsala ko wata
damuwa.
Amma zuwan Suwaiba sai ta tasa min su a gaba
da iya shege iri-iri, dan kankanin abu ne na yara zasu
yi sai ta ce uhun, wai su masu gida ko?
Saboda ita gidan ubanta ne yasa take yi muku
haka, ta bugi Umahmah ko Mama ta buge ta bai taba
damuna ba, don nasan duk tsiyarsu ba za su gana
mata %50 din abin da suka gana min ba.
Don haka ko a jikina saboda na riga nayi ilimin
sanin cewar zaluntar yaro bai cutar dashi da komai
sai dai ma ya zamo mishi wani alheri a rayuwarshi ta
gaba.
To amma neman da take yi na ta rinka 'shiga
tsakanin Umahmah da dan uwanta tana batawa shi ne
abin da naji ba zan lamunta ba, tunda abin da ke
afruwa a tsakaninsu din hali ne kawai na kuruciya.
Suna mata tana musu kamar yanda take yi
tsakaninta da kanmenta, da ni ce na haife su, gara
wadancan ma duk sun fi karfinta in dam be za'ayi
dukanta zasu yi.
A duk lokacin da maganarsu tazo gabana kuma
na kan yi hukunci ne bisa cewar ta basu hakuri don
ita ce karama duk da mafi girman da aka yi mata na
kwana bakwai ne.

93

Ba kuma don komai nake yi hakan ba sai don in
hada kansu su zama abu daya, su sani su kuma yarda
da cewar yancin da ita take dashi a gidan bai wuce
wanda suke da shi ba.
Don haka rannan da na sake jin Suwaiba tana
shiga naganar Su tana cewa ai tunda kuka zo zaman
maula a gidan ubanta sai kuyi jayin bakuri da ita sai
na gangara daga inda nake.
Naje na shiga wurin nasu Suwaiba tana ciki na
tambayi yaran abin da ya faru suka mayar min na
kalli, Suwaiba na ce mata a wannan bayanin ne ki ke,
fadin wannan maganar wa wadaanan yan yaran
ya'yan cikinki?
Sau nawa ki ka haifi wadannan? To bana so kar
in sake ganin ki a wurinsu bana son ganin kina shiga
min harkar yara, ta ce har da taki ma na daina, na ce
to da yafi miki daidai.
Tun daga ranar ta daina gaishe ni, in na gaishe
tan ma ta amsa a laiace ba fita tana kallona bata yi
min sallama ba ta dawo kuma a lokacin data ga
dama.
Naga zata zubarwa mijina da mutuncin da ake
ganinshi da shi tunda ba wani shiga na mutunci take
yi ba shi kuma ba zaunin gida bane balle yasa abinda
take yi.
Don haka nayi mata magana kan ta daina yawan
fita, ina take zuwa tunda ni da ita ai ba wasu dangi

94

muke da su a Dabai ba, balle ta ce min wurin 'yan
uwanmnu take Zuwa.
Sai kawai tavi min maganganun da na kalle su a
matsayin rashin kunya, gudun 6acinrai sai yasa Ado
yazo gida daga Abuja, sai na ce mishi ga abinda ake
ciki don ya sani.
Sai kawai ya ce min kai Humaira, kananan
maganganu irin wadannam rinka hutar dani kawai ki
daina gaya min su ko dai kiyi maganin abin kawai da
kanki ko kuma hanya mafi sauki shi ne ki gayawa
Mama.
Nasan zata tsawatar na ce mishi to duk da ba
dadin hakan naji ba.
Rannan sai wani abu ya sake hada ni da Suwaiba,
naje na samu Mama ina gaya mata, sai kawai ga
Suwaiba tana biye da ni tana magana har tana tafa
hannu, ni fa sai dai in za ki mutu ki mutu in za ki yi
rai kiyi rai.
Don duk tsiyarki ba zan bar gidan ba ba wurinki
na zo ba, ba kuma don ke nake zaune ba, kin ce in
daina kula 'yarki na hada na ce har kema bana
kulaki, bana shiga harkarki, ba na shiga harkar
'ya'yanki dukkansu wurin Mama nazo gida kuma
gidan Kawuna ne.
Na kalli Mama, wacce tayi shirù tana kallon
tsiwar da Suwaiba take yi min, na ce Mama kina jin
ta? Sai kawai naji taja nin tsaki ta ce min

95
Chapter 14 · 0% Book details