Sashe 9
Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Fess yagama cin abinci yakai komi kitchen dakanshi yafito yaje sama fitowa yayi da paracetamol, bottle water yadauka mara sanyi yaba Aman yace “kaima Anty Ummi kace nace tasha” gyadamai kai tayi yawuce da gudu yatafi dakinta Amal na binshi yakoma falo yazauna yana saka news duk yanda yaso yama gane meke faruwa a news din kasawa yayi yawuce sama fuuu, bude kofan dakin Hadizan yayi ranshi abace tana zaune gaban dressing mirror daure da towel tana shafe shafen ta na night routine batare da tajuyo ba tace “ki ijiye abincin kiwuce kifita dakikiya kawai next time try this nonsense kinbar gidana kenan jaka kawai yar kauy…..” “Hadiza!” Nura yakirata da kakkausan murya saida gabanta yafadi dan baitaba kiranta da zafi haka ba juyowa tayi da sauri ta kalleshi ganinshi tsaye a tsakiyar dakin yana kallonta ranshi abace, haderai itama tayi tace “badai kahana yarinyar nan dafamin abinci ba dan idan kayi haka u will see the other side of me Nura” wani kallo yamata yace “inason naga other side of you din today are you crazy? Ke wace kalan senseless mata ce? Kissan kai kike kokarin yi agidana? Are you trying to kill that girl?” Hannu ta dagamai tace “please lower your tone ni matarka ne ba some yan aiki dazaka dinga dagama murya ba Nuri, I’m your wife not slave so keeep muryanka down by now kasan I don’t take that shit, namiji yazo yana wani mini ihu akai saikace ubana kuma ma idan na kasheta sai me? Eh? Ba yar aiki bace, yarinya mara galihu duk irinsu ne irin yaran da akauyen su akekai yara maza almajiranci mata kuma akaisu aikatau kota mutu sai me mezai faru? Almajirai nawa suka mutu wani abu yataba faruwa? Ai yara da iyayensu suka nuna basu da gata mutane ma basa gatanta su so bakaina farau ba dan yar aiki ta mutu agidana ehe” Sosai Nura ke kallon Hadiza shi baimasan tayi nisa haka ba sai yau wato tanada answer for anything, at this point baimaso maganan nasu yayi nisa dan kar zuciya ya debe shi yadauketa da mari hakan yasa cikin kakkausan murya yace “duk randa kika sake trying nonsense din nan wlh saikin bar gidane duk wani abu dake gidan nan fara tundaga kan gateman suna karkashina ne, hakki na ne nakare kowa na tsaresu dan haka don’t ever try hurting mutanen dakemin aiki inba hakaba u will leave this house!” dudda maganan ya mugun mugun sosama Hadiza rai amman daurewa tayi dan bataso yagane tai wani kalan shewa. “Ahayyeeee nanaye ance dama idan baka mutu ba bakagama sanin halin maza ba, Nuri ni kakema gorin zaka kora daga this rat hole dakake kira gida”? Ta nuna dakinta da ko’ina da hannu, tsaki kawai Nura yayi yajuya yafita tabishi da sauri dan idan bata bashi amsan maganan nan ba hankalinta bazai kwanta ba kai zazzabi ma zai iya kamata, tana biye dashi yana tafiya tace “zan iya gina gidan dayafi nakan nan sau dubu a kyau dakuma girma Nura kada kayi kuskuren yimini gorin gida, duka duka yaushe kayi kudin lokacin dana aureka kagama masters akan architecture kanama wani building agency aiki har kazo kabude naka kampanin na harkan filaye da gine ginen estate anan Abuja, who do you think you are dazaka min gorin gida nixaka kora Nuri, au ina maka magana ka maidani mahaukaciya kayi tafiyan ka wlh wlh yanda ka batamin rai dinnan saina huce akan mahaifiyark…….” Chak Nura ya tsayar da tafiyan dayakeyi akan staircase yajuyo ahankali yakalleta itama daidai tana tsayawa dab da shi tana kara rike gaban towel nata da kyau tana kallonshi tace “da ilimina da sana’ata da darajata har ka isa kazo kana gayamin na kara dukan wata yar aiki sainabar maka gidan ka, sabida yar aiki Nuri zakace zaka koreni, what on earth do you take yourself for? Are you God? Sabida kaganni mace kadauka I am weak ne I can’t defend myself? Zakace zaka korini daga gidanka u think bazanyi speaking up ba, Listen Nuri, me and you are two equal people! Baka fini da komi ba, duk inda kasa kafa nima zan iya saka kafan, nasan kimata nasan daraja ta and my worth u cannot downgrade me or downgrade my status and for batamin rai din nan dakayi this night wlh saina batama mamank…….” Azuciye Nura yadaga hannu zaikai mata mari kaman daga sama sukaji Aman yace “Daddy!” Chak Nura ya tsaya da hannunshi batare dayakai marin ba, he don’t ever wants yaranshi to have a memory of him yana dukan mahaifiyar su, dunkule hannunshi yayi tareda saukewa kasa ahankali yajuyo yakalli Aman din, dasauri Aman yazo ya rungumeshi tsamtsam yana kuka sosai yace “Daddy sorry kayakuri Mommy is sooo baddd but don’t slap her okay Dady, beating girls is not good katuna ranan dana daki Amal haka kagayamin” daukan yaron Nura yayi ya rungume ahankali tareda mannamai kiss akai yama kasa magana yashiga tafiya dashi yana sauka, Hadiza dake kallonsu tace “ai naso ka maren wlh danai suining naka for domestic violence, try that next time kagani I will mess you up Nura” sauka yashiga yi kasa yana dauke da Aman a hannunshi gaban dakin Ummi yakaishi yace “shiga” shiga yayi sannan yajuya yawuce yafita daga gidan yashiga motanshi yamabar estate din gabaki daya zuciyanshi daci takemai da gaske idan Allah yabaka mata nagari wlh ka gode kama kara godemai dan shaidanun mata azaba ne, they will so push you to the wall kaji kaman zaka kashesu, yayi tafiya mai nisa sannan yayi parking yakalli wayanshi yadade yana kallo kafin yasauke ijiyan zuciya yakai hannunshi yadauka yabude yaciro wani lomba yakira wayan na gab da katsewa aka dauka daga dayan bangaren wata yar dattijuwan manyantaccen murya ne tai magana. “Nura barka da dare ya wurinku yasu Amalily?” Ahankali yace “lafiya lau” saikuma yayi shiru all this years baitaba daga waya yakai karan matanshi ba sai yau jin yanda baiyi magana ba yasa tace “lafiya Nura Maiya faru? Ina ganin wayan nasan da wani abu duba da lokacin dakama kirani, what happened?” Ahankali yace “Hadiza bansan menene damuwanta ba, tunda na auri Hadiza Anty Jamila for once bantaba kokarin takata ba ko shut her up, ni mutum ne dana tsani takurama mata ko basu damuwa I have 4 sisters dukansu mata nataso da sanin yanda ake girmama mace kare mace dakuma daraja mace” Anty Jamila tace “kwarai Nura wannan haka yake zan shaideka ako’ina” ahankali yace “the whole idea da concept na feminism ya shiga kanta, I’m not saying feminism is wrong no, ko Allah yasani inaso naga matata tacigaba, banki duk matakin dazan taka aduniyan nan matata ta takashi ba, I empower her nabata jari tafara business nakaita su dubai oman Egypt dasauran kasashe alokacin sabida ta saro abayoyi tafara, bansan gobeba I believe empowering matata will go a long way for yaranmu incase of gobe dabata da tabbas, bantaba ma Hadiza kallon wata baiwa ko yar aiki ba rather I see her as life partner dina wacce nakeson to go through every phase na Rayuwa together mu tsufa together but ita bahaka take ganin komi ba, gani take anything daya kamata tayi agida nima yakamata nayi nida ita we are equal, yimin girki gaidani bani abinci is not her duty duka abubuwan nima nayi we are equal afterall, gaidani akan me zata gaidani nima na gaidata…” dasauri Anty Jamila tace “subhanallahi” dan ijiyan zuciya yasauke yace “Anty Jamila the whole feminism din nata haukane kawai, rashin kunya menene menene babu wanda bata mini nakasa gane kanta balle kafanta, i can’t even talk to her kafin nayi magana daya tayi dari, Anty Jamila I am tireddddd nagaji, I want peace of mind at this my age” yanda yayi maganan saida yabama Anty Jamila tausayi tasan yanda Nura keda hakuri tasan for Nura yadauki waya yakirata takaishi bango anatse tace “Nura kayakuri kayakuri shikenan abinda zan iya fadi kaga wannan halin shine dalilin dayasa maza da yawa basason bama matayensu freedom har subarsu suyi sana’a dan wasu matan dazaran sun soma taba kudi shikenan sai sudinga jin kansu kaman giwaye suma yanzu sun faso, amman kabarni da ita zan kirata zan kira Mama kuma” ahankali yace “please kada ki sanarda Mama tana fama da hawan jini saisa nakiraki ban kirata ba” murmushi tayi tace “to shikenan amman dan Allah kayakuri” ahankali yace “to saida safe agaida yara” yakatse wayan yadade ahaka yau bacin ran yasa he wanna be alone ma inda bahaka ba zai iya kiran abokan shi yaji inda suke yaje yasamesu, yayi kusan 3hrs awajen sannan yatada mota yabar wajen.
Domin magana dani M shakur koso nasaki a group dina chat me up tanan wa.me/+2347012181461
Domin magana dani M shakur koso nasaki a group dina chat me up tanan wa.me/+2347012181461