← Book details Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 96

Sashe 8

Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda Ummi tafara serving tuwo a plate Hadiza ke kallonta zuciyanta na wani kalan tafarfasa kawo tray gabanta Ummi tayi ta ijiye bata idasa jaye hannunta ba Hadiza ta daga tray gabaki daya ta mike tsaye ta kwarama Ummi akai da tuwon dake a leda da miyan taushen da kwanukan da cokulan duka suka bare akanta wani kalan mahaukacin azababben mugun ihu Ummi ta kwala tafashe da kuka dayasa su Aman suka firgita dukansu suka juyo ganin Anty Ummi ta tsugunna a dinning ga miya tundaga saman dan kwalin kanta har goshinta da idanunta ta kullen gam tana ihu sosai jikinta nawani kalan rawa kaman wace ta zare tsabagen azaban zafin datakeji na miyan dakuma yajin miyan a idanunta yasa suka taho wajen da gudu Aman yace “Anty Ummi” cikeda masifa Hadiza tanunata da hannu tace “kina gidana, kinacin abinci na, nabaki makwanci, nabaki kayan sawa, nabaki sabulun wanka dana wanki, sannan ina biyanki kizo bazakimin biyayya ba, sau nawa ina gayamiki ni bancin tuwo sau nawa nake gayamiki? So kike nayi kiba nai katon ciki? Zanje sama nai wanka ki tabbata kin dafamin wani abun kin kawomin dakina kafin nagama wanka inba hakaba wlh saina koraki daga gidan nan this night” ta dauki jakanta tawuce sama fuuuuu, tsugunnawa daga Aman har Amal sukayi agaban Ummi da jikinta har bari yake sabida zafin miyan dan bata dade da gama miyanba ta juye a kulan gidan ga kulan su irin na millions din nan ne masu rike zafi kaman me, dudda Aman yaro ne amman saida yakai hannunshi yacire tuwon daga jikinta yana kuka sosai ya yar akasa yace “Anty Ummi sorry stop crying” Amal tace “Mommy is badddd mommy” sosai Ummi ke kokarin tabude idanunta takasa sai kuka take dudda kukan take na tausayin kanta tariga tai alkawari komenene zatai hakuri tana bukatan albashinta dashi Gwaggo ke zuwa asibiti dakuma shi ake tara kudin auren kanninta, dole ta jure komi itane hanyan cin abincin gidansu, so take ta mike but tama kasa hannunta Aman yakama Amal ma takama dayan yace “let’s go Anty Ummi ki wanke fuskanki” gydamusu kai tayi tana tsayar da kukan datake ta yunkura zata tashi tama kasa saita kara fashewa da kuka daidai lokacin an bude kofa da sauri su Aman suka juyo ganin Baban su shima ya shigo ya tsaya chak yana kallon daga yaranshi har Ummi dake kuka sosai kaman anyi mutuwa agidan ga jikin Ummi duk miya, fuskanta ma haka takasa bude idanu yasa yayi wajensu dasauri baima cire takalmi ba yace “Subhanallahi meya faru faduwa kikayi Ummi” Tsayar da kukan tayi dasauri muryanta na rawan sheshekan kuka tace “eh” tana yunkurawa zata tashi dasauri Aman yace “is Mommy Dady, ita ta kwara mata the whole tray na abinci akai Anty Ummi has been crying” warware handky daya ciro Nura yayi daga aljihunshi baiyi wata wata ba yakai kan fuskanta cikeda damuwa ahankali yace “tsaya” batai musu ba tsayawa tayi kwashe miyan kan idanunwanta yayi tass, miyan yayi fasha fasha awajen harda gashin idanunta, sannan ya kwashe na goshinta dana kumata batare daya taba na wuyanta ba dudda baka ce but he could see yanda fatan fuskan yayi ja, ijiye handky yayi dasauri kafin ahankali yakai hannuwanshi duka biyun yakama kafadanta dagashi har ita atare duka sukaji wani iri dasauri tayi kokari fizge kanta strictly yace “stop banson gardama, tashi muje” yanda yayi maganan ba wasa hakan yasa bata kara gardama ba, yana rikeda ita haka yayi kitchen da ita su Aman suka bisu bude kofan kitchen din yayi zuwa nan backyard gaban wani tap dasuke dashi awajen, yabude tap din yajuyo yakalli Aman yace “je bayin Anty Ummi kadauko mini sabulun wankanta” “okay Dady” Aman ya amsa yajuya da gudu shikuma yabude tap din yace “tsugunna” ahankali Ummi ta tsugunna, gently yadinga tara ruwan da hannunshi yana watsa mata a fuska har saida miyan ya fiffita duka da wayanda sukenan asaman gashin idanunta daidai Aman yakawo sabulan, ga mamakinshi sabulun vivo yagani ahankali ya karbe yakama hannunta yasa sabulun aciki yace “wanke fuskan mugani da sabulu” shafa sabulun tayi ta dirdirje da kanshi yake zuba mata ruwa tana wankewa tass ta wanke fuskan, igiyan wajen ya kalla ganin wata singlet dinshi wanda yasan itane ta wanke yajawo yabata yace “share fuskanki saiki bude idanun nagani”

Share fuskan tayi ahankali sannan tashiga bude idanun yajin dataji yasa tamaida idanun ahaukace tarufe tafashe da kuka kunsan yanda yaji ke birkita mutum tace “wlh da kwai yaji sosai Alhaji, wayyoo Gwaggo na nashiga uku” shi arayuwanshi yanada tausayi, ya tsani aga ana hurting mutane in general balle kuma yaga mace in pains, da sauri yasa hannunshi ya karbi hanky yamikama Aman yace “hold it nagani“ sabulun yadauka daga kasa yasa a hannunshi ya fara wankewa sannan ya murza sabulun a hannunshi ahankali yadan kalli fuskanta yanda ta kankame idanunta gam jikinta har lokacin rawa yake tana dan kuka, dan ijiyan zuciya yasauke sannan yakai hannunshi gently yashafa sabulun a fuskanta kaman yanda ake wankema yaro karami fuska, fuskanta is sooo soft kaman na dan yaro, almost 30sec yayi yana chuda fuskan sannan ya kunna pampoo yashiga wanke mata fuskan tass kafin yakarbi singlet din ya share fuskan da kyau ya tsane dogayen eyelash nata kafin ahankali yana tsugunne agabanta yaciro wayanshi dudda akwai haske wajen bauuu flash na wayanshi ya kunna yabama Amal yace “princess haskamin fuskanta” dasauri Amal ta karba ta haska fuskan Ummi, shima yana kallon fuskanta dake sheki yaji wanki da sabulu yace “bude idon nagani” gently tashiga bude idanun dake rawa sosai na haggu tabude tass na dama ne tabude kadan dan tanajin yaji sai yarfe hannu take ta rude sosai ganin yanda takeyi yasa ahankali yace “tsaya” tsayawa tayi ijiye singlet din yayi kan jikinshi yakai duka hannunshi ahankali yayi cupping fuskanta dasauri Ummi takalleshi tadade rabon dataji namiji dab da ita haka, ahankali babu komi aranshi yakai hannanyenshi ya ware kwayar idannun nata dake mata yaji kafin gently Ya hura iskan bakinshi ciki wani kamshi Ummi taji da sanyi daya ratsa jikinta feeling inama ace zata sami miji dazai dinga kula da ita haka kaman yanda Alhaji keyi yanz, Alhaji nada kirki gashi kyakkyawa fari dashi kaman wani balarabe ga bakin saje, tsayar da hura idanun yayi ganin tabude su rass tana kallonshi kaman yaune rana na farko datake ganinshi shima zuba mata idanu yayi yana kallon kwayar idanunta yanda suke walkiya sabida hasken flash da Amal ke hasko musu, idanun sunyi ja na kukan dataci da yanda tai looking so helpless dakuma yanda take kallonshi hakanan saiyaji kaman yasata ajikinshi ya lallasheta, there’s something about her da kawai he finds interesting baisan menene ba. “Anty Ummi yadena yajin”? Maganan Aman yadawo da dukansu daga duniyan tunani atare dukansu kowa ya janye idanunshi, Nura ya mike tsaye da sauri yawuce ciki batare daya kara kallonta ba itakuma ahankali tamike tsaye tana goge wuyanta, gyadama Aman kai tayi tace “yadena” dasauri sukazo kusa da ita suna kallon fuskan hakan yasa ta tsugunna dukansu taba fuskan nata sukayi cikeda so sukace “sorry Anty Ummi” murmushi tayi sosai cikeda kokarin cheering nasu up tawani daga hannunta sama tace “Anty Ummi jaruma ce kaman Amalili, ko Mudi da Kumurci tsorona suke menene yajin miya dashima bazai tsorata dani ba” haba zokaga yanda sukahau dariya, Aman yace “Anty Ummi yaushe zaki kaimu kauyenku muma muga Mudin nan da Kumurci” hannunta takai kan kumatunta kaman mai tunani kafin tace “wata rana zamuje” ihu sukahau yi suna tsalle Nura daya dade yana kallonsu ta window kitchen murmushi yayi yawuce yadauki mop yafice gyara dunning din yayi da kanshi.
Shigowa sukayi a kitchen din fita tayi taje dakinta ta chanzo kaya zuwa wani atampa dogon red yamata kyau sosai.

Tana fitowa hada ido sukayi da Nura dake zaune a dinning yanacin tuwo adan kunyace ta sauke kanta kasa tazo wajen ta duka har kasa tace “Nagode Alhaji, kana bukatan wani abune dazan kawo maka”? Sosai yake kallonta red yamata kyau dudda babu wani special abu game da atampan but yamata kyau, jin shiru baice komiba yasa tadago kanta ahankali hada idanu sukayi da sauri yadauke kai itama maida nata kasa tayi dasauri, ahankali yace “bana bukatan komi, thank u” mikewa tayi harta juya tafara tafiya kaman daga sama taji yace “abincin yayi dadi sosai, thank u Ummi” dadan sauri tajuyo ga mamakinta kallonta yake suka sake hada idanu sukayi, faduwa gabanta yayi dasauri tasauke kanta kasa tasake juyawa zata shiga kitchen batare datace komi ba yace “mezakiyi a kitchen”? Ahankali tace “Anty zan daurama wani abinci batacin tuwo” strictly yace “wuce kije ki kwanta kihuta” dudda bataso ba dan batasan mezai biyo bayaba kasa musu tayi tawuce takoma dakinta ta kwanta.
Chapter 8 · 0% Book details