Sashe 48
Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Har akai İshak bata fitoba tanajin hiransu da muryan su Amali akasa but bata fitowa, kawai she don’t feel belong ne at all, bayan magrib Nura yashigo gidan Hajiya tace “kirawo Hadiza muyi dinner” baiyi musuba yaje sama bude dakinta yayi tana zaune tana aiki da laptop yace “sauko muje muyi dinner, Hajiya tace nazo nakiraki” yatsine fuska Hadiza tayi tace “nariga naci abinci basai na saukoba” tsayawa yayi yana kallonta kafin yahade rai yace “sauka muje” wani kallo tamai kaman ta baro bakan magana ta gayamai tadai daure tayi shiru ta danne tace “please Nuri nayi dinner nagaya maka, over feeding kakeso nayi or is it by force mutum yaci abinci?”? Kallon fuskanta yake ganin she’s in that her not so good mood yasa yace “suit yourself” yajuya yawuce yatafi tabishi da mugun kallo tace “tunda masu zugaka sunzo ai daman dole kayi haka, all along i was right daga zuwansu last time ka chanza sukasa ka auromin yar aiki, ai wlh da mahaifiyarka da Meena bazan taba yafemusu ba nothing can ever make me like this those humans da Ummi, I can never mtswwww” taja tsaki wound na heart nata nadawowa sabo, wayanta Hadiza ta dauka tasauka dagakan gadon tana dialing number Anty Jams tawuce kofa tayi locking kofan da key daidai Anty Jams ta dauka tawuce bayi zama tayi kan matsan dayake arufe cikin sanyin murya tace “Anty Jams Hajiya takara dawowa gidan” jin muryanta yasa Anty Jams tace “saikuma akayi yaya dan Hajiya tazo”? Shiru Hadiza tayi tana lumshe idanu kafin chan tace “Anty Jams bawai i hate Hajiya bane but I hate living da ita at the same space Anty Jams, akwai wani vibe da energy danake getting from Nura idan yana tareda maman shi kaman irin baya bukatana dinnan am noting, yanzun nan danace bazanyi dinner ba bai damuba yayi tafiyanshi da dane daya lallasheni na yarda nabishi, he feels stronger idan Mamanshi na gidan nan, remember duk abinda nakeyi baya komi but the last time datazo ai sabida ita yasakeni yakoreni ban kwana agidana ba, Anty Ja……” takasa maganan ta hanyar rufe bakinta datayı jin kuka yazo mata Anty Jams tace “ina jinki” deep breath tayi taking tace “I feel suffocated idan Hajiya na gidan nan the atmosphere is toxic for me kaman inta kurma ihu, nasan yanzu datazo she’s cooking something ne so ake ahademini kai da Hajiyan da Ummi da Meena harda babban munafukin Nura da saiyau dasafe yake sanardani zata dawo gidanmu, Anty Jams from abinda nake gani Hajiya is not even ready to leave my house for me, yanzu haka zanta zama da Mamanshi agidan nan? Ina sharing gıdana with my mother Inlaw? Ita lokacin datai aure haka tayi zama da surukanta? Fisabillillahi kinzo kin wani tare gidan yaro sabida kawai ahanani sakat, ko Allah yasan fadan dakikamin yasa bance komiba to amman Allah yasan i hate her staying agidana wlh and Allah ma yasan ba lallai na iya keeping up da wannan pretense dinba dan nasan munafinci tazo tayi da sunan ciwon karya” “Hadiza! Hadiza! Hadiza!!” Anty Jams takirata sau uku tace “Hadiza kinji sau uku nakiraki ko”? Hadiza tace “uhm” Anty Jams tace “Hadiza wlh nagaji da unnecessary complains dinki tell me tunda kuke Hajiya tataba miki wani abu”? Ahankali Hadiza tace “directly no but indirectly ai ita tasa aka sakeni, tana cikin gidan tana ganin komi, kuma ita takira Nura yadawo ta surfafamai karya akan fadana da Meena da baima tsaya yaji tabakina ba yasakeni dan haka yes tamin laifi” wani dan murmushi Anty Jams tayi maidan sauti tace “let’s assume Hajiya cema tasa askeki which zan iya ransuwa ba itabace, idanma itace ai ta isane, tana matar data tsugunna ta haifo mijin dakika aure, build this Nura of today that’s so gently and sweet ki dauko mata police bazata ce asakeki ba yo konine zance ai ballema ba itabace” cikin korafi kaman zata fashe da kuka Hadiza tace “nidai ko ba itabace ta tattara ta barmin gidana i hate her staying in my house Anty Jams wlh babu wani ciwon datake bakinta rass the whole treatment yakawota nan Abuja is just a strategy ni kawai ta barmin gidana, banason zama da ita, I hate staying with her, spirit dina baison zama aduk inda take i called you ne nake gayamiki sabida ki bani better way dazan fada wa Nura yasa mamanshi tabar gidan nan dan banso namai magana yaga kaman na tsaneta ne” “kaico!” Anty Jams tafadi asanyaye tace “Hadiza on a serious note yaushe kika dawo mara imanı haka? Hadiza a known diabetic patient, hypertensive patient kike cewa lafiyan ta kalau? Hadiza old age kadai cutane, old woman dakeda yaron shekara kusan hamsin kike cewa lafiyanta kalau ciwonta karyane and is strategy? Must one be in coma kafin ki yarda that person is sick? Ohh Innalillahi” Hadiza tace “Anty Jams kona miki karya bazanma Allah ba, ni kawai na tsani Maman Mijina Hajiya agidan nan shine kawai maganan, har cikin raina wlh na tsani ganinta acıkın gıdana, I hate staying with her I can’t stand her sight” Iska Anty Jams ta fuzar azafafe cus tafara gajiya tace “Hadiza kinga Allah yasani nabaki duka shawaran dayakamata nabaki, amatsayina na yayanki na sauke hakkinki dake kaina na nuna miki gaskiya nakuma nunamiki kuskuren ki tunda kinki ji kije kiyi DUK ABINDA KIKAGA DAMA yes I said it duk abinda kikaga dama kiyi, do things your way ke kika sani but kisani duk tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa zaija” azafafe Hadiza tace “baki kikemin Anty Jams daga nagaya miki matsalata? Kin bani shawara naji nabi I am still managing, wait ma Anty Jams da ace ina abu my way da yanzu wlh na hurama Nura wuta a tsuliya nasa ya saketa itama yarinyar na korata kauyensu danshi kanshi Nura knows how stubborn i am, but still na saurareki sabida kar yazamto ban saurari shawaran yar uwata ba, Anty Jams barikiji u can ask liman Mata daban uwarmiji daban, kowacce tanada hakkı kan mijinta, I have hakki akan mijina which dole ya sauke itama Hajiya haka, I know he’s trying taga good doctor agarin nan must he bring her to my house eh?? Nura ya gina estate daban daban agarin nan bai rasa gida sabo fil dazai saka mamanshi da kanwarsa ba why my house eh? Kawai anzo an dauramin jaraba ga mata makira taitayin maka faram faram afuska buts she’s a devil in disguise” dasauri Anty Jams tace “A’uzubillahi Hadiza, how will you feel idan Matan Aman takira ki Makira devil”? Dasauri cikin tsiwa tace “wow Anty Jams kin karamin baki kuma well bari nabaki amsa bazan taba da girmana da tsufana natashi naje natare agidan Aman ba natakuramai da matar shi nahanasu sakat wlh bazan tabayiba ko da ko am on my deathbed” murmushi Anty Jams tayi tace “babu ta yanda rayuwa bata kasancewa just pray, itama Hajiyan ba ason ranta take gidanki ba, tunda kukai aire ta taba takowa gidan ki banda yanzu” cikin dan ihu Hadiza tace “wat are you saying Anty Jams? Don’t forget matan nan nada yara mata guda uku dasukai aure maisa bataje wajensu ba su mata ai sunfi dadi zama da iya kula da mamansu sai gidan danta namiji zatazo, bayan Aisha na Egypt, Egypt ma da akwai manyan hospital inda zataje taga specialist, banda sauran yaranta dake nan Nigeria nagaya miki duk makirci ne and well executed plans gashinan ai daga zuwa ta na farko sunsa an sakeni suka zugashi ya auremin yar aiki how can I love her? Taya zan dinga zama da irin matan nan bayan ta cutardani? Wlh I hate her, I hate all family Nura, i hate them with passion sabida duk dasa hannunsu Nura yamin abinda yamin, da inada wani iko dasaina rabashi dasu wlh Muga karyan tsiya mugaye kawai kuma sai Allah yasakamin” Anty Jams tace “kinga saida safe nagaji dajin haukanki” cikeda bakinciki Hadiza tace “eh saida safe from now on I will be doing things my way and watch zakiga yanda zan gyara komi wlh in no time, bazan Kara daukan shawaranki ba dan it’s sucks, kissa da kisisina to hell with it I can’t pretend and I will never pretend because of a man if I hate you I hate you if I like you I like you that’s Hadiza, bazan kara kiranki for my issues ba saida safe” ta katse wayan Anty Jams na kokarin magana ta tashi ta kunna tap na washhand basin ta wa ke fuskanta tana kallon madubi tana fusar da iska kirjinta yamata nauyi sosai she feels alone.
***
***