← Book details Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 96

Sashe 54

Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe goma family Hadiza na asibitin dan Max air suka samu na 7:30 shima dan anyi delay, da mahaifiyar Hadiza, da Anty Jams, da kannin Hadiza guda biyu dake binta Rabi da Hafsat dukansu kowa yayi aure duk jugum kowa yayi a asibitin har lokacin Hadiza bata tashiba, Mama dake kallon Nura dake rikeda hannun Hadiza tace “kaje gida kayi wanka ka kimtsa Nura” girgiza mata kai yayi yace “bazan iyaba Mama, bari saita tashi ai Dr yace nan da awa daya alluran zai saketa ta farfado” saikuma da sauri yakalli Anty Jams yace “ga car key na jeki dauko mata su Aman idan ta tashi ta gansu zataji dadi Batai musuba Anty Jams takarba key Rabi da Hafsatu sukace zamu biki bata hanasu ba duk motan Nura suka shiga ta tada Rabi tace “wlh sainaci kutumar uban yar aikin nan dan durun uwatta” wani kallo Anty Jams tamata tana tuki tace “kinsan Allah idan abinda kike shirin yi kenan zan iya kwana naje na saukeki a asibiti” cikin fushi Hafsat tace “Anty Jams waike mesa kike abu kaman Mama, inda mu Hadiza takira da tuni bamu zo mun tayata koran shedaniyan yarinyar ba takama takiraki bayan tasan u will just talk like Mama look at her yau, inda ta mutu shikenan fa mun rasa yar uwanmu Nura yacigaba da rayuwanshi like nothing happen mukuma fa? Munrasata har abada, duk yanda zaki kalli abin Nura yariga yaci amanar Hadiza daya auri yar aikinta, ai da kishiyan gida gwara ta waje, yarinyar da Ya Hadiza tadauka aiki tamata komi I remember lokacin da Ya Hadiza muna waya tana yaban yarinyar wai tanada kirki tanason su Aman saisa take biyan yarinyar 50k ni kaina saida nayi ihu nace yar aikin kike biya 50k abinda akano 5k ko 8k ake biya duk wata, tacemin yarinyar nada kirki ne but shine munafukar ta aure mata miji akanme Ya Hadiza bazata hadiyi zuciya ta nemi mutuwa ba is it easy? anty Jams are you even relating the pain Ya Hadiza is going through everyday agidan nan tana kallon yarinyan” ta share hawayen daya zubomata da sauri tace “Wlh sabida Nuran ma babba ne kuma akwai Mama awajen da bazan gaidashi ba, munafuki kawai mayaudari mugu sai yanzu dayaga takusan zuwa barzahu shine yaşan yana sonta” Rabi tace “bar munafuki ai maza! Maza! Wlh namiji ba dan goyo bane, namiji butulu! Namiji mayaudari! Maza yan duniya! Ba kunya ba tsoron Allah ba kawaici ya auremata yar aiki!!! Wlh kaman naita surfafamai zagi dana ganshi!” Anty jams kasa cemusu komi tayi dan itama bawai she’s happy bane she’s just feeling bad ganin kanwarta in that state saida sukakai gidan tayi parking tajuyo takallesu tace “Hafsat, Rabi’a na rokeku da girman Allah kada kuyi wani abu kungamai mahaifiyar Nura na gidan bawai kuma lafiya gareta ba please” da magana ciki ciki sukace “munji” duk suka sauko suka shiga cikin gidan, Hajiya ce ke zaune a falo ga Meena agefenta dake zuba mata kunu ganinsu yasa tace “a’a su Jamila ne”
Cikeda fara’a duk suka shiga gaigaisawa akayi anawa juna jaje, Anty Jams tace “ina yaran Baban su yace nazo na daukosu daganan zamu dan daukanma Hadiza kaya adaki” dasauri Hajiya tace “suna sama yanzun nan Ummi tahaura dasu dan yimusu wanka kuje kuhadama Hadiza kayan kafin nan tagama shiryasu nima ina ganin zan biku asibitin nan naje na ganota” Anty jams tace “Hajiya kina fama da kanki dakinyi zamanki agida wlh ai Alhamdulillah tunda she’s out of danger” Hajiya tace “ina kafana kafanku kuzo kuyi Kari nasan bakiyi ba” duk sukace Alhamdulillah suka wuce sama Meena tabisu da kallo zata mike Hajiya takama hannunta tace “me haka ina zaki saikace sata zasuyi agidan”? Dasauri murya chan kasa tace “wajen Ummi zani” girgiza mata kai Hajiya tayi tace “hakan zaiyi kaman munada wani manufa zuciya Jamila nada hankali ai yi zamanki anan” badan tasoba ta zauna.

Daidai Ummi tafito daga bayi dauke da Amal a hannunta Aman tariga tamai yana zaune bakin gado da towel yana jiranta tafito ta shafamai mai su Rabi suka bude kofa suka shigo chak Ummi ta tsaya dantama tsorata cikinsu Anty Jams kadai tasani da duk suke kallonta, tsayawa tayi gaban bayin ahankali tace “sannunku da zuwa ina kwana” azuciye Hafsa tataho gaban Ummi tasa hannu ta karbe Amal azuciye ta nuna Ummi da yatsa tace “kina nema ki kashe mahaifiyar su shine kuma kike nan nan da yaranta bakar munafuka” dasauri Rabi tai wajen ta nuna Ummi daga sama zuwa kasa awulakance tace “ke kina gani kin auremata miji ko hmmm je asibiti kiga menene soyayya wlh na tausayi miki dudda bakijin turenci but zan miki u mean nothing to Nura, keba komi bane awajen Nura ba, Hadiza Itace komi nashi, mata ta daukeki tabaki aiki, ta biyaki da kyau, tabaki ci sha sutura but kici amananta ta hanyar aure mata miji abinda kikama Hadiza Allah yasa ama yaranki! Ama kanninki! Ama jikokinki ke duk Wanda kika hada jini dasu Allah yasa amusu!” Dan lumshe idanu Anty Jams tayi tace “Rabi and Hafsat please ku dauki yaran nan kuzo mutafi dakin Hadiza” daukan Aman Rabi tayi suka kwashi kayansu dasuka gani akan gado wanda Ummi tafito dashi suka juya harsukai kofa Rabi tajuyo takalli Ummi da kanta ke kasa tace “kuma wlh idan kina Tuna’nın kin kwace mata miji kinyi kuskure ki rubuta ki ijiye saikin dawo abin tausayi kuma yar kallo agidan nan danko Nura kije asibiti kigani nadaman aurenki yake, mema yakaishi gashi yanzu kin zama sanadin matarshi uwar yaranshi dayakeso na neman ta mutu, duk wani addu’a da bokaye da malamanki gwara ki kirasu dan amiki addu’a Allah sa kar Nura ya koraki, tana maganan suka fice wasu hawaye masu zafi Ummi taji sun zubomata dasauri ta share tafito daga dakin tawuce ta shiga dakinta ta tafi bayi dasauri ta duka tafashe da kuka sosai.

Har suka gama abinda zasuyi sukabar gidan Hajiya har sawa Meena tayi taje takirata dantamata sallama zata bisu asibiti tace ma Meena taba bayan gida.

Ahankali take bude idanu dasuka mata nauyi sosai, dummmm kunnenta yakeyi kaman wacce ake kwalama kira daga mesa haka takeji taji ana. “Momy, Momy, Momy wake up” rawa rawa idanunta keyi dasauri jin muryan Aman and Amali daga nesa chan na gayamata ta tashi kafin tabude idanun nata a juye tana kallon sama ganin mutanen da idanunta basa gane mata su da kyau blurr blurr take gani saichan taji murya daga nesa ance “can you see me” sake runtse idanunta dasauri tayi sannan tabude su Dr tagani akanta saikuma taji an rike mata hannu da sauri takalli hannun ganin Amali da Aman suna kallonta suna kuka har lokacin suna kiran Momy yasa azabure ta taso zaune Dr yace “woo wooo calm down kada ki tashi” dasauri tasaya dayan hannunta dake rawa zata shafa kan zaman dake kuka sosai yana shesheka Dr yatayata kama hannun tadaura kan fuskan Aman rike hannun yayi yace “Momy don’t be sick again I will never be angry with you again I promise” gyadamai kai tayi Amal tace “me too Momy” ganin yanda Hadiza ke yunkurawa tanason daukan yaran nata yasa Dr yadago gadon tayi zaman kwanciya yasada yaran yasasu ko Wanne aside nata rungumeta sukayi kuka hawaye ne suka fito daga idanun Hadiza ahankali Dr yaciremata oxygen din cikin murya mara karfi tace “A…..man, Aaa….mal” “yes Momy” kankamesu tayi kafin in a very weak voice tace “I……..na…..Da…….dy….” Dasauri duk suka dago suna mata pointing Nura dake tsaye dab da bed din yana kallonsu yana murmushi wani kalan kallon Nura tayi sai lokacin ma taganshi da duka mutanen dakin sai kawai tafashe da kuka sosai tana mikamai hannu dasauri Nura yaje rungumeshi Hadiza tayi sai a lokacin karfin kukanta yakaru ta kankame Nura sosai tanajin mugun sonshi aranta tace “Nuri kayakuri kayafemin duk abinda namak……” hannunshi yadaura kan lips nata yace “shiiiii u talk too much daga tashinki just get better I love you My Didi” hawaye na bulbulowa daga idanunta tace “I love you too my Nuri” Dr yace “tunda dai love moment ake bari naje anjima madawo atafi da ita for lab investigation, yanzu have this moment” yawuce yafita Nurse tabishi sakinta yayi Ahankali tana kallon yan dakin tace “Hajiya” dasauri Hajiya taje wajen gadon tace “naam Hadiza ya jiki”? Cikin kuka tace “Hajiya kiyakuri kinji nasan namiki laifi wlh Hajiya haushinki nadinga ji gani nayi kaman kene kika sashi yamin kishiya da yar aiki na, bake kadaiba kowama haushinshi nakeji har Anty Jams dake gayamin gaskiya da ina bayi naji numfashina yana tafiya I was trying nakira Nuri like azo ataimakamin but nakasa naji wani murya nagayamin bazakizo ba sabida na cutarda ke sannan na zargeki abisa laifin da baki aikata ba kuma baki tsaneni ba, Hajiya naji dadi da Allah yatasheni nayi alkawari dan nemi gafaranki Hajiya kiyakuri kinji” share mata fuska Hajiya tayi tace “Hadiza nobody is above mistake komi yawuce awaje bantaba rikeki ba kinji”….
***

Yau kwana uku Hadiza na asibiti tun ranan Nura bai kara kiran Ummi ba ko gida baya dawowa shike kwana da Hadiza saidai akaimai kaya, yan uwanta ne ke dawowa gida kwana su shiga kitchen suyi girki saiya zamto Ummi kullum taba daki muddin zata fito tahadu da Hafsat ko Rabi saisun yada mata habaici, takira Nura sau uku bai dagaba tamai text daban daban duk ba reply Hajiya kadai da Meena ke kula da ita dudda bata nunamusu komiba Hajiya ko ankawo abinci idan sun gama girkawa ko Ummi na sama saita kirata tazo aci abincin da ita hakanan zata sauko not feeling among, idanun Ummi sun fada babu abinda yafi damunta yanda Nura bai kirata ba ba reply kullum saitai kuka kafin tayi bacci.

Yau kaman kullum wuraren 12 tana zaune ita kadai a falo Meena tashigo dakinta tace “tashi muje asibiti tare” dasauri Ummi tace “ba’ace naje ba, kinga ko Hajiya batace najeba hakama Baban Amali karnaje wani abu yasami Hadiza” Dasauri Meena tace “Hajiya takirani tace muzo tare Allah shayi akasa nahada, tashi kisa Hijabi muje bolt na kira yana waje ya iso” badan tasoba ta tashi hijab kawai taja maroon har kasa tasaka tabi Meena suka fice daman kowa na asibitin har Hajiya suka wuce.
Chapter 54 · 0% Book details