← Book details Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 96

Sashe 5

Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wajajen 10 aka sallamesu da magunguna a hannu suka dawo tunkafin sukai gate na estate dinsu ya hango Aman dinshi kan kujeran security da pajamas ajikinshi da ledan popcorn idanunshi sunyi jaa, jiyayi zuciyanshi takama da wuta parking yayi yafito dasauri security dayake zaune kusada shi yace “Yallabai barka da dawowa Madam ta ijiyeshi anan gashinan yanata kuka yace yunwa yakeji shine na saya mishi Popcorn yamai jiki”? Sabida yanda ran Nura ke daci gyadamai kai yayi Aman yarike hannunshi yakalli fuskan Baban kaman zaiyi kuka gwanin ban tausayi, kaman dan maraya yace “Daddy where’s Anty Ummi am hungry she’s the only one that gives me food and play with me, Mommy never gives me food or play with me” suppressing anger dinshi yayi yaduka ahankali ya shafa kan yaron yace “muje Anty Ummi na bayan mota da princess don’t cry again okay”murmushi yayi yay bayan mota da gudu yabude yashige shikuma ya tsaya yama security godiya tareda bashi kudi sannan yazo yabude gaban mota yashiga ya zauna yaja mota ta glass na gaba yake kallonsu duka yaran sun kankame Ummi suna hira da ita, sai biye musu take kaman yarinya itama, wlh zaka dauka itane mahaifiyar yaran kawai dan ita black beauty ne yaran kuma fararene tas su kaman turawa amman kana ganinsu kaga strong affection tsakaninsu, sunma manta dashi a motan sai hira suke Aman yarike Ummi gam yanata zuba kaman bashi yayi kaman orphan dazuba, akofar gida yayi parking duk suka sauko tana rikeda Amal, Aman shima yarike mata hannu suka wuce ciki yabisu da kallo direct kitchen suka wuce zaunar dasu Ummi tayi kan kujerunsu dake kitchen din dake gaban island, tashiga yimusu girki agurguje dan Aman yunwa yakeji tana attending to them, ta dafa lafiyayyen taliya na manza fevorite dinsu da kaza ta zuzzuba musu a plate tajuye sauran kuma a kula mai kyau takai dinning ta ijiye sannan takoma kitchen tana bama Amal abaki dantaci da kyau, koda yashigo gidan dan tuntuni yana waya awaje kamshi ne yamai sallama wani kalan yunwa yaji yanaji dinning yaje yazauna kaman wanda ke tsoron wani abu bude kulan yayi daidai Ummi tafito da tray na ruwa da fresh juice a hannu dantaji zuwanshi ta ijiye kan dinning taduka tace “ko adafa wani abune daban Alhaji” girgixa mata kai yayi yace “a’a wannan yayi” tashi tayi takoma kitchen, kaman mai tsoro yadau fork yasa yadebo kadan yakai bakinshi yatauna dadin dayaji wlh saida kunnenshi yayi siiiii, baisan sanda yadauki plate yadeba ba shi arayuwan shi yanason home made food rashi yasa almost few restaurants ne baisaniba a Abuja ba yaune rana na farko dayaci abincin yar aiki and wlh yamai dadi sosai tass yacinye yatashi ga mamakinshi rawa yaga tanama Amal tana kai abinci bakinta da wayau dantaci, ga magani dayaga ta fito dasu ta zuzzuba a marfi dan an fadamata yanda zata bata asibiti, shima Aman yataso yana tayata rawan sunama Amal rawa dukansu biyun tana dariya sosai fa tana karban abincin tabata maganin ta shanye tass ba gardama ko kakarin amai suna mata waka Aman na tafi kaman suna studio, jinshi kawai yayi yana murmushi ance some yan aiki suna faking love ko sabida parents na yaran but shi all he sees ana is genuine love, kuma yaran loves her suma dearly hakanan samin kanshi yayi yana kallon Ummi sosai, yarinyar black beauty ce tanada tsayi akalla zatai 23 ko 24, yar kauye ce from her dressing but she’s kind and tanason yaran shi kuma her smile is contagious dan gashi shima yanata yi, sannan the way she dance is annoyingly cute, kaman Ummi taji ana kallonta juyowa tayi da fuskanta ta kallo falon karaf suka hada ido da Nura dake kallonta tana rawa ma Amal.

Wanna talk to me about something??? Chat me up anan;
wa.me/+2347012181461
MATAN??? Ko MAZAN???💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 3️⃣

BONUS💃
Sosai kirjinta yabuga da sauri ta sauke hannayenta kasa tadaina rawan tasauke kanta kasa shima daga kallonshi gabanta nafaduwa dumdumdum.
Wucewa Nura yayi dasauri sama zuwa dakinshi yakasa daina ganin fuskan Ummi dana yaranshi how happy all of them were, yanda itada Aman kema Amal rawa, bayi yafada dasauri ya watso ruwa yafito yashiga shiryawa dan yafita meeting din dayake dashi is by 2, cream yadauka zai shafa saikuma ya tsaya maisa ya kalleta haka smiling ya tambayi kanshi? He was lost dayana kallonta, yar aikinsu ce fa but he was finding all abubuwan datakeyima yaranshi super cute, dan ijiyan zuciya yasauke saikuma yacigaba da shafaman.

Ummi daduk takasa natsuwa itama a kitchen ta tambayi kanta maisa yake kallonta, tun yaushe Alhaji yaganota tana rawa haka? Duk wani kalan kunya kunya da nauyi nauyi taji tanaji, IPad din Aman tadauko ta kunnamusu anan kitchen din dan bazata rabu dasu ba tashiga gyaran gidan duka tanaso tana gamawa tamusu wanka, itama taje tayi saita daura abincin dare.

Shiryawa yashigayi cikin suit dan dawasu representative na China company zai hadu dasu yanaso yabasu contract nayin titin cikin estate dayakeyi, yana cikin daura agogo wayanshi yahau ringing kallon wayan yayi ganin Sis yasa yakai hannunshi ya danna call din batare daya daga wayanba yacigaba da saka agogo daga ta dayan bangaren akace “Ya Nura ina yini” “how are you Aminatu ya jikin Hajiya kunje asibitin”? Kasa magana tayi sai bakinta yahau rawa, dasauri yasa hannunshi yadauki wayan gabanshi ya mugun fadi yakai wayan kunnenshi dasauri yace “what happen jikin Hajiya ne meya faru?” Cikin kuka tace “dazun nan tafadi abayi yanzu haka muna asibiti” bugawa kirjinshi yahauyi sosai anatse yace “Dr Tanimu ne ke ganinku”? Dasauri tace “eh shine” dan ijiyan zuciya yasauke yace “daina kuka ya isa babu abinda zai sami Hajiya kinji” kaman yana gabanta gyadamai kai tayi, cikin dan taushin murya yace “is okay, zanyi magana da Tanimu I think zan muku booking flight gobe kutaho nan Abuja taje babban asibiti anan don’t cry again hankalinta zai tashi, akwai kudi awajenki”? Dasauri tace “eh akwai” ahankali yace “to stop crying bari nai magana da Dr Tanimu” nan da nan ya katse wayan yakira Dr sunyi magana da dadewa sannan ya katse wayan dakanshi yamusu booking first flight na gobe da safe sannan yasake kiran sister nashi yace zasu biyo jirgin safe gobe suzo koya ake ciki tadinga gayamai yatashi ya idasa shiryawa duk mood nashi ya chanza sannan yafito anan falo yaga Aman da Amal suna kallon cartoon a iPad nasu duk an musu wanka sunyi kyau gwanin ban sha’awa kaman ya debesu yafita dasu Amal kaman ba itane mara lafiya ba karasawa yayi inda suke ya duka yamusu peck agoshi yace “Dady zaitafi aiki” dasauri Aman yace “Dady zan bika office” shiru yayi kaman mai tunani yana shafa kansu yace “shikenan zanje daku amman sai ranan Saturday jibi kaga gobe akwai school yau bakuje ba dukanku” Dasauri Aman yace “hadda Anty Ummi zamu itama taje taga Daddy’s bigggggg office” ya ware hannunshi biyu yana nuna how big office na babban shi is, dan murmushi yayi yana kallon Aman din kafin ahankali yace “yes Son hadda Anty Ummi” dasauri Aman yace “love you Dady u the best Dad ko Amali? Dadyn mu is the best” dasauri Amal yace “yeeeessssss Dady is the best” murmushi yayi yace “my princess and my Aman are the best nima” harzai tashi yace “ina take?” Aman yace “Anty Ummi”? Gyadamai kai yayi dasauri yace “itama taje tai wanka adakinta” jinjina kai yayi yamike yace “to natafi bye” bye sukamai yawuce yafice.
Chapter 5 · 0% Book details