← Book details Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 96

Sashe 3

Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Binsu da kallo Nura yayi yadan sauke ijiyan zuciya koba komi tayi shiru yanzu, komawa falo yayi yakunna wuta yazauna kan kujera, yadawo ko chanza kaya baiyiba, bai wanka ba ranshi yabaci, kunna tv yayi yana kallon news dudda hankalinshi bawai yana wajen bane dan damuwa ne cike fal aranshi. Yana zaune awajen Amal tafito da kanta rikeda karamin bowl da aka soya kwai mai kyau aciki tace “Daddyyyy Oumu Oumu” tana nunamai bowl din, dan murmushi yayi tazo kusada shi daukanta yayi yazaunar da ita saman kujera kusadashi tahauci, ruwa Ummi tabiyota dashi a water bottle nata mai kyau ta ijiye agabanta takoma chan nesa dasu wajen dinning tazauna akasa duk atakure take dan batama saba ganin mai gidan ba, kusan 1yr tana aiki agidan itada yaran sukafi zama agidan nan, sai yau ne take ganinshi hakan yasa duk takejinta atakure. Dauke kanshi Nura yayi dagakan tv ya kalleta yanda tazauna akasa kaman wata mara daraja irin yar maulan nan dukta takure tana wasa da hannunta bini bini tana kallon Amal dakecin kwai abinta da hannu kusada shi yasa yadanji wani iri, he always hate yan aiki to be honest yaune rana ma na farko daya taba kallo fuskan yarinyar nan dake musu aiki agida kuma this is almost 1yr take gidan nan, ba yabo ba fallasa yace “jeki kwanta kiyi bacci” kanta akasa cikeda respect tace “saita gama cin abinci na wanke mata hannu na gyara wajen nasata bacci tukunna zan iya bacci” dan jinjina kai yayi saikuma yayi shiru bai kara cewa komiba, yakai hannunshi yataba wuyan Amal din jikinta yadan rage zafi maybe sabida ruwan daya watsa mata neyamaida idanunshi kan TV, tass Amal tacinye kwan ta cillar da plate kasa tace “akoshi” dasauri Ummi ta taho ta duka tadauki plate din da cokalin adan kunyace dan she’s not comfortable yanda Baban ke wajen tamika mata hannu tace “zo aje a wanke hannu” makemata kafada Amal tayi zata kama Babanta da hannun kwai dasauri ya matsa yace “je princess awanke miki hannu” turo baki tayi takalli Ummi dake kallonta, cikeda dabara da iya wasa da yara tace “zomuje muyi wasa da pampoo akitchen” wani kalan dirkowa Amal tayi abin harsaida yabama Baban mamaki tazo gaban Ummi da dugudu tace “ruwaaa, pampoo” da sauri Ummi taduka ta dauketa tana murmushi tace “yauwa Amalulu na muje, idan Aman yatashi gobe shima mu soyamai Omu Omu ko”? Gyadamata kai Amal tayi sukatafi kitchen, dan ijiyan zuciya yasauke to some extend kam she’s good with kids kawaidai shi bayason yan aiki ne and he don’t trust hygiene dinsu, dan ijiyan zuciya kuma yasauke idan ba yan aikin ba yasan Hadiza ba aikin nan zatayi ba ko sama da kasa zata hade.
Tass ta wanke mata hannu ta share mata baki tare suka wanke plate da spoon din tace “yanzu sai bacci ko, nagoyaki”? Gyadamata kai Amal tayi Ummi ta duka tace “yauwa babuuu Amalily” da gudu tahau bayanta tana murna dariya tayi bataso tasake fitowa daga kitchen din hakan yasa sai kawai tacire dankwalin kanta ta warware ta goyata dashi, wasu manya manyan kitson hannu ne akanta shiku ya tsufa sosai amman tanada bakin gashi mai kyau da santsi, zagaye kitchen din tashigayi da ita tana jijjigata tana mata waka ahankali. “Amal Amal yar gayu, Amal yar kyakkyawa, Amal yar fara saidai tana fitsari agado” dan ihu kadan Amal tayi tana hamma Ummi tai dariya tace “to nadaina Amal bata fitsari agado, Amal jaruma ce gimbiya mai kafafun zinare yi bacci to” haka tadinga jijjigata tana zagaye katon kitchen din nan da ita dantai bacci. Gajiya yayi da zama afalo dan dama jira yake agama wanke mata hannu yadauketa suje sama gashi kusan 30min shiru basu fito daga kitchen ba, baki yabude zai kwalama Yarinyar kira yakasa, shi wlh ya manta sunanta kuma is somehow yakirata yar aiki, dan tsaki yayi yamike tareda kashe tv yatafi wajen kitchen din, kofan abude hangota yayi tana tafiya a kitchen din tana jijjiga Amal data fara bacci abayanta suna zagaye, ko kadan bata luradashi ba dan bekai gaban kitchen dinba, yanda yaga take zagaye take jijjiga Amal abayanta gently tapping her bombom ta saman zanin goyo tana mata wake haka sai kawai hakanan yaji yaji wani iri aranshi, he can’t even understand idan guilt yakeji ko anger, wannan wani kalan rayuwane ace mahaifiyar Yarinyar na bacci anbar yar aiki da yarinya bata runtsaba tsakar dare, tun 9 yanzu kusan 3 idanunta biyu, is she not human being ita? Ko machine ce? Kowa fa deserves this sleep, dare mahutan bawa, koda aikinta ne there’s nothing bad idan Maman yarinyar natare dasu to help her out, abin is really really somehow azuciyanshi, jiyayi ranshi yamai badadi dauke kai yayi tareda dan gyaran murya batare daya karasa kitchen dinba, dasauri Ummi tajuyo jin gyaran murya, batare daya kalli kitchen dinba yace “kawota taje ta kwanta” dasauri Ummi tace “to” goyon tashiga kwancewa kafin ta sauketa tafara jan dan kwalinta ta jefa akanta sannan ta dauketa a hannu tariga tai bacci ta taho ahankali har zuwa gabanshi tamikamai ita tace “gata Alaji” dan juyowa yayi yakalleta ahankali yasa hannunshi ya karbeta yace “sannu da kokari, jeki huta kema” “to” ta amsa tana tsaye awajen, wucewa yayi itama tawuce falo takashe wuta sannan takoma dakinta ko 1min bata karaba sai bacci.
**

Wuraren 5 yabude ido sabida zafin jikin Amal data kwana dakinshi, tashi yayi zaune yakai hannunshi yatabata yarinyar nan needs hospital wucewa yayi yashiga bayi ya watsa ruwa yafito daure da alwala yawuce yasauka kasa motsi dayaji a kitchen yasa yawuce kitchen yar aikin yagani tana sharara da goge goge jin knocking kofa yasa ta dago kanta dasauri ganinshi yasa ta duka tace “ina kwana Alhaji” juyawa yayi yace “lpy lau kibar aikin nan kije ki shirya Amal ina dawowa daga masallaci zamu kaita asibiti” bai tsaya jiran amsanta ba yawuce, wanke hannunta tayi ta tafi sama azuciyanta tace Allah sarki Amal dina, dakinta taje ganin bata ciki yasa ta tafi dakin Aman yana baccin shi shikadai batanan to ko dakin Maman take bude dakin tayi da sallama bata wajen hakan yasa tai tunanin dakin Baban, idan da sabo tasaba shiga dan ita ke gyara dakin ta wanke bayi, bude kofa dakin tayi tadauki Amal dake bacci tawuce dakinta wanka tamata ta shiryata tsaf itama tai salla nan da nan tai parking jaka taje kitchen agurguje tamata air frying chips da sausage tasa mata a cute flask nata da ruwa tahada komi da yaro ke bukata, itama taje ta chanza kaya zuwa wani dan dogon Riga baki ba laifi yanada kyau but irin outdated one din nanne shima Anty tabata ta yana gyalen akai tazauna a falo rikeda Amal da yanzu bamata da karfi, shigowa yayi gidan ganinta zaune akasa afalo rikeda Amal data shiryata tsaf in this short time yasa yace “let’s go” dan kallonshi tayi saikuma ta tashi da sauri, harya zauna agaban mota yaga tafito ta kinkimo Amal da katon jakan a hannu tana tafiya da kyar kaman zata fadi yasa kawai yafito yataho da sauri, tsayawa Ummi tayi gabanta nafaduwa ganin yanda ya dumfarota, hannunshi yamika mata yace “bani jakan” bashi tayi yajuya itama tabishi bude bayan motan yayi ya ijiye jakan ya tsaya yana jiranta tana tahowa tashiga baya rikeda Amal saida tai settling down yamaida kofan yarufe yakoma gaba yashiga yatada motan yaja duk wani motsi da Amal zatayi saita tambayeta menene, ciwo, zafi, me kikeso, zakisha ruwa sannu ko Amal dina abinda baitaba ganin Mamanta tayiba.
Chapter 3 · 0% Book details