← Book details Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 96

Sashe 85

Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Supermarket yakaisu yace “kuma Mommy ku shopping” yaran were so happy kowannen su ya debama Mummy abun da ransu keso, sukaje kanta yabiya kowanne ya karbi ledanshi na Amali yafi karfinta ya amsa yace “lazy Princesses” kaman zatai kuka tace “Dady I am stronger than owlett din pj mask fa ko Ya Aman”? Aman yace “yes Dady, nikuma I have lots of super power, Dady I can lift this car up” Dan zaro idanu Nura yayi yace “sannu special boy” Amali ta kwashe da dariya, Aman yace “Daddy kaga Amali ko Lazy princess kawai” wani tsalle Amali tayi zata fara halin dasauri Nura ya dauketa yace “yakuri Hajjaju, muje mu shiga mota” baya yabude ya ijiye Amali da kayansu shikuma su Aman first born adole babba ya shiga gaba yace “Dady I want to start driving nima” dasauri Nura yakalleshi duka duka fa Aman is just 4, kawai dai irin brilliant smart kiddo din nan ne sai kawai yayi dariya cikeda sonshi yace “okay Son zan koyama idan kakai 15yrs” tada motan yayi suka tafi sai hospital.

Kashe motan yayi yafito Aman yace “Dady this is a hospital is my Momy sick”? Gyadamusu kai yayi yace “but taji sauki, muna zuwa zamu tafi mu kaita gida ma” gyadamai kai yaran sukayi ya rufe motan holding shopping din Amali suka wuce ciki sai kallon yaran ake dan Amali and Aman are so cute wlh kaman yaran larabawa, ga Ummi tamusu gayu, Aman kuma harda saka sun shade black na Rayban da Dadyn shi yasiyamai shi adole babba, dan baiso ana referring nashi as yaro.
Ahankali Nura yayi knocking tareda bude kofan dakin, Hadiza na zaune kan gado Mama na hada mata shayi zata sha aka bude bude kofan kawai taga yaranta sunci gayu kaman ba su ba, looking finer and healthier than yanda ta barsu, dawani kalan gudu suka taho barinma Amali tace “Mommyyyyyyy” wani kalan tsalle Amali tayi Hadiza ta sauka daga gadon da sauri tadauketa sama Aman shima yazo yana cire glasses nashi, tsugunnawa Hadiza tayi tana kallonshi she can’t believe ita ta haifi this big handsome smart adorable boy, rungumeshi tayi sosai tana rike da Amal, kuka taji yazo mata but saita daure sabida su, bata taba tunanin Nura zai kawo mata su ba, she can’t even kwatanta excitement nata sai kawai tashiga mammanna musu kiss kaman zata hadiye su, Nura ya gaida Mama tabashi plastic chair ya zauna yana kallonsu kasa kasa.
Shafa fuskan Maman shi Aman yayi yana kallonta dan yaron akwai wayau he understand a lot of things batare da an fadamai ba yace “Mommy what’s wrong with you? You look so skinny and dark” dasauri Amali tace “yes Mommy, meke miki ciwo? Ya Aman mu mata addu’a kaman yanda Anty Ummi ke mana ko”? Dan murmushi kadan Hadiza tayi tace “Momy’s tummy hurts” kaman zasuyi kuka sukace “sorry Mommy” Amal ta shiga tofamata addu’a Mama tace “wannan tsohuwan yarinyar da wayau” dan murmushi kadan Nura yayi, saida tagama ma Mommy addu’a, Aman yabata ledan hannunshi yace “Mommy I got this for you get well soon” kallon Aman Hadiza tayi yanada wani kalan charismatic composure na Baban shi, she can’t believe yaronta ne Aman, Alhamdulillah! Hannu tasa ahankali ta amshi ledan zatai magana itama Amali ta sauka da gudu ta dauko nata ledan dake gaban Dady akasa ta dawo da gudu takawo mata tace “Mommy I got this for you, get well soooooon Mommyyyy naaaaa” Amali tai maganan like a little sweet girl, bude ledan Hadiza tayi trying so hard ta rike kukan datakeji, ledan Aman tafara budewa drinks ya kwaso mata cres, yasan Maman shi na yawanshan, da vita milk da cake loaf, da peanut da biscuits manya manya Oreos da chocolate cookies, tabude ledan Amali kuma su minti mai tsinke da cingum ne aledan dayawa exactly shopping din yara dai, sai kawai tafashe da kuka ta rungumesu Aman yace “stop crying Mom is the tummy still hurting Dady call Dr for Mom” girgiza musu kai tayi tace “am just so happy ne yarana sun kawomin tsaraba, yarana are all grown up kunyi kyau, and I miss u very well” Amali tace “Mommy give me one sweet” dariya Mama tayi Nura ma yayi murmushi kadan Mama tace “kin kawo tsaraba kuma kina roka, kanki kika sayomawa kenan su Amali manya” murmushi Hadiza tayi tadauki sweet tabata takalli Aman daketa kallonta shima yana lurada duk yanda Maman shi ta chanza kaman ba itaba tace “mekake so kai ma nabaka?” Ahankali yana kallonta da this affection na mother and son yace “chocolate Mommy” wani kalan son Aman Hadiza taji ya shiga ranta barinma dayace mommy, dauka Hadiza tayi tace “nabude maka?” Gyadamata kai yayi yana kallonta har lokacin, tabudemai ta bashi amsa yayi yace “thank you” vita milk daya kawo mata tadauka tabama Mama tace “Mama budemin nasha” dasauri Aman ya karba yace “Dady will open it, grandma batada hakori” yaje gaban Nura yabashi, ahankali Nura yasa hannu ya karba yakai bakinshi ya bude dan ba opener adakin yaba Aman, Hadiza ahankali tace “thank you Dadyn Aman” zama duk yaran sukai kan gado kusada ita Amali nashan sweet, Aman na cin chocholate, Hadiza na shan vita milk tana nan nan da yaran, ahankali Nura yamike yakalli Mama yace “bari naga Dr nazo” Mama tace “to” fita yayi yaci karo dasu Baba akofa suka gaisa nan da nan yayi clearing all the bill yakarbo magungunan da aka bata yabiya yayi signing discargw papers din yataho dakin yabama Mama magungunan ta yace “an sallamemu mutafi” Motan Nura Hadiza tashiga da yaran da suka zauna baya da ita sai surutu suke mata su Mama kuma suka shiga motan Baba, suka tafi gidansu Hadiza parking yayi duk aka shishiga gidan.

💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 3️⃣6️⃣

Huuuuhuuuuuu agyara hanya gafa MAMMI HAJIA tazo mana da kayan mata wey no be juju, ba jazz, ba abacadabara ko suddabaru aciki amma kuma aikinshi yafi yankan wuka, MAMMI HAJIA fa tariga tayi suna awannan harkan dan haka ku garzaya aguje kar ayi baku zaku iya shiga whatsapp group nata ta hanyar danna link din nan.

https://chat.whatsapp.com/L9xdTKd3MXZJRW8zkAMSqH

36
NOTE: akwai school of thought daban daban i read something daban daban kan idda. Ance bari terminate idda, at the same time some sunce sai cikin yazama mutum shine yake terminating idda Soo Allahu A’alam Allah masani, feel free to correct me or shed more light on the issue Allah ya ganarda mu gabaki daya Ameen.
Chapter 85 · 0% Book details