← Book details Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 96

Sashe 72

Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

What are the perks na auren educated independent woman??🤗
And what are the perks na auren uneducated uncivilized lady???🤗

Don’t forget ku shigo class dina na matan Aure with just 2k chat me up today wa.me/+2347012181461
💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣9️⃣

https://chat.whatsapp.com/JgukZW7wzUHL8lbg9IraqN

INDAI KAYAN SAWAN YARANE TO GA KANKAT NAKAWO MUKU❤️
Do you want your kids to look like those yan gayu kids you admire on instagram? Definitely yes, Eshamin kiddies got you covered. mun shiga mun fita mun tattaro the best for your kids, with chikini money zamu fito muku da yaran ku tass. We make beautiful dresses (rtw and bespoke) headbands and turbans. When it comes to kids fashion you know I no get no 2

You can also check us on IG
https://instagram.com/eshamin_kiddies?igshid=OGQ5ZDc2ODk2ZA==

29
Mota suka shiga instead instead sutafi gidan Hajiya direct super market yasa driver yafara kaishi, tsaraba ya kwasa dayawa yakai wajen kayan zaki tsayawa yayi yana kallon roban mentos cingum Ummi ne tafado ranshi sanin tanaci, ahankali yasa hannunshi yadauki roba daya yasa a cart su Aman ma suka kwashi abubuwan dasukeso dukansu yaran were so happy sukaje suka biya direba ya deba yasa a boot suka wuce gidan Hajiya.

Yaran sunsan gidan Hajiya sosai ko sunzo salla anan suke zama sai idan Mommy su tazo takan dauke su suje gidan su adawo dasu wajen Hajiya da yamma.
Suna shiga gidan Hajiya da gudu suka sauko daga mota sukai ciki, matan dake taya Hajiya aikatu na kayan abinci sai sannu da zuwa sukema Nura dayayi kyau gaidasu yayi cikeda girmamawa ya ciro ragowan cash na aljihunshi yamikama babban ciki su raba sai godiya suke yawuce ciki daidai bakin kofa yaga Hajiya tabude mai hannu rungumeta yayi warmly yace “Hajiyaaaaa” “barka da zuwa Nura, sannu sannu, maraba lale” sakinshi tayi sabida Aman da Amali dasukace “Grandma where’s Aunt”? Gwaggo na murmushi tace “sunje school amman sun kusan dawowa” shiga falon sukayi Nura yasami waje ya zauna yana kallon yanda Aman da Amal ke guje guje suna fadawa kan lumtsa lumtsan kujerun Hajiya falon a gyare sai kamshin turaren wuta yake, sosai Hajiya ke kallonshi yadan rame yafada, yama danyi duhu kadan, kusadashi ta zauna tareda shafa kanshi cikeda so tace “ya kake”? Murmushi yamata yace “I’m fine Hajiya kada ki ramu I’ve moved on” sosai Hajiya ke kallonshi feeling at ease da yanda yayi maganan kanshi ta shafa tace “Madallah, to jeka wanke hannu kazo kaci abinci da kaina namaka girki yau” cikeda kulawa yace “Hajiya bana hanaki aiki ba, me Meena keyi da Um…….” Saiyay dan shiru kafin dasauri yace “all this matan dake tare da ke ai zaki iya sasu koda ace Meena na school” murmushi tamai tace “I cooked for my son, Oya tashi ka wanko hannu kazo, na gyara maka side dinka, idan kuma gidanka zaka sai shima nasa aje a gyara” yatsine fuska yayi yace “banson naje gidan nan Hajiya ina nan, maybe dai naje Adamawa” Hajiya na kallonshi cikeda gamsuwa tace “yakamata kaje kaga Gwaggon Ummi kam” Gyadamata kai yayi kaman ya tambaya ina Ummi yadai shiru yatashi hannu yaje ya wanke duk Hajiya na lurada shi yanda yake kalle kalle he’s just dying to see her, yadawo sosai dagashi har yaranshi sukaci abincin Hajiya kaman wayanda suka fito daga yunwa tass yagama ya mike yace “bari naje na watsa ruwa a side dina” Hajiya dake bawa su Aman abinci abaki da hannunta tace “toh” wucewa yayi yafita yataka zuwa wani side dake dan nesa dana Hajiya babba ne flat din, bude kofa yayi yashiga an gyara falon dayaji komi sai kamshi yake yawuce bedroom ga akwatinshi har ankai ciki, ruwa ya watsa yafito ya tsaya ta window yana goge jikinshi daidai nan yaji yaranshi na ihu ihunsu yacika gidan. “Anty Ummiiiiiii” dasauri yasa hannunshi yadan dage labulen ya leka, Ummi yagani sanye da dogon rigan abaya black mai shegen kyau ta yane gyalen akai dayadan zamiye baya ana ganin kitson datayi ma shuku yan kanana masu kyau hannunta dayasha jan lalle rikeda jaka haka dayaga books aciki tawani daga Amal da bala’in mamaki takasa yarda yaran ne kaman Hajiya bata sanarda ita zuwansu ba.

Tsayawa Nura yayi chak yana kallonta she look peng, way prettier than before, black skin nata nawani kalan sheki though idanunta sun fada ciki but she looks thicker than yanda ya santa, dan lumshe idanu yayi yana kallonta yanda harta daura Amal abayanta ta rungume Aman ta gaba suna juwa juwa matan gidan na musu dariya, jiyayi zuciyanshi ya buga! Kasa daina kallonta yayi she looks sooo happy da ganin yaran suma yaran haka, saida yaga da ita da su sun wuce dakin Hajiya sannan yasaki labulen window idanunshi kaman zasubi Ummi falon.
Chapter 72 · 0% Book details