Sashe 58
Mazan Ko Matan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Cikin 20min Nura yashigo gidan adan tsorace dan yadauka ciwon Hajiya ne yatashi yana shigowa falon suka hada ido wani kallo data mai saida gabanshi yafadi wlh dasauri Nura yazo wajenta yaduka yana kallonta yace “Hajiya menene? Wani abu yafaru ne? Jikinki ne? Mama meya sami Hajiya”? Yayi maganan cikeda so dakuma kulawa ga Mamanshi nuna kanta Hajiya tayi tace “Nura tunda kai aure yau shekara goma zuwa gomasha kenan nataba saka a hanya mara kyau?” Dasauri ya girgiza kai yace “a’a” tace “nataba cemaka ka bakanta ma Hadiza koka kuntata mata, kai nama taba gayamaka ga yanda zaka tafiyar da gidanka?” Dasauri yace “a’a Hajiya, Hajiya meya faru waya bata miki rai haka eh Mamana”? Bubbuga kirjinta Hajiya tayi tace “Nura ni uwa ce, na haifi mace na haifi namiji, nasan darajan yara, banda haka d’a nakowa ne, abinda bazanso ama nawa ba wlh bazan taba bari ama nawani ba” Mama tace “kwarai!” Hajiya tace “Nura Ummi ta daukeni matsayin uwar da batada shi, bamata min kallon maman mijinta sai mahaifiyarta, bata kyashi tashiga kitchen tadafamin abincin dazanci takuma dafa na gida, wlh wlh abinda Ummi kemini ko Meena diyar dana haifa da cikina batamin, tabani abinci, ta kwashe kayana takai washing machine ta wanke tazo ta goge, ta gyaramin wajen kwana ta kunna turare, idanba na kora Ummi ba ko nace tabarwa Meena wannan tayiba yarinyar nan ita kemin komi da murmushi kan fuskanta Nura yau karasa wanda zaka wulakanta sai Ummi?” Cikeda mamaki yake kallon Hajiya danshi ya manta yama Ummi wani abu dasauri yace “Hajiya mena mata kuma? Takikkirani tun shekaran jiya ban samu nakirata back ba ban mata reply message ba shinefa kuma ai ban natsu bane” sosai Hajiya ke kallon Nura jin yau kwana uku rabon dayamayi magana da yarinyar tanason tai magana Mama tace “Nura bakai magana da Matarka ba yau kwana uku tana matarka koma menene ai ka kirata kaji ta tashi lafiya tunda hakki ce agareka gaskiy……….” Hannu Hajiya tadagama Mama azuciye hakan yasa Mama tai shiru ganin yauwa ran Hajiya alalace yake, Hajiya na kallon Nura dake gabanta aduke tamike tace “Nura auren huce takaici ko auren sha’awa fadamin wanne kayi da Ummi?” Nura na kallon Hajiya yama kasa magana saikuma yace “kaman ya Hajiya”? Cikin fushi Hajiya tace “how dare you Nura baka kira yarinyar nan for 3days kaji yatake ba you think is okay, dazu Meena takawota asibiti da sunana kamata koran kare!” Mikewa tsaye dasauri Nura yayi yashafa kanshi zuwa fuska yakalli Hajiya yace “Hajiya wani irin koran kare? Cewa Meena nayi tawuce takomar da ita gida is not good Hadiza dake that condition taganta” cikin fushi Hajiya itama tace “wat do you mean by that Nura are you trying to say Ummi tasa Hadiza in that situation”? Cikida gajiya da maganan yace “Hajiya no bahaka nake nufiba amman dai ai aurenta danayi yasa Hadiza ke neman rasa ranta so I have to keep her away from Hadiza kada tazo takara samin heart attack, am just protecting Hadiza Hajiya” Sosai Hajiya kewani kalan kallon Nura the way he said everything da zuciya daya kai tsaye is as if Nura baida single feeling for Ummi aranshi all abinda ke ranshi ke kuma damunshi ayanzu is just Hadiza he sees nothing wrong a abinda yayi, jinjina kai Hajiya tayi irin na manya cikin wata kalan murya tace “ai shikenan Nura tunda aurenta shine dalilin dayasa Hadiza ke neman rasa ranta saisa ka wulakantata baka daukan wayanta, tazo asibiti kuma kamata kiran wulakanci dacin mutunci Ummi ta tafi garinsu! Tabarmaka gidanka!” Dawani kalan sauri yakalli Hajiya sake jinjina matakai Hajiya tayi yanzu damuka dawo mun nemata sama da kasa bata, Meena ta duba bolt taga ta chanza location ta tafi jabi takira mai bolt wai yakaita Adamawa line” kusan shiru falon yayi na kusan minti biyu duka abinda yafaru dazu a asibiti na dawowa Nura jiyayi ranshi yabacı matuka, cikeda bacin rai yace “yanzu sabida dan maganan danayi wanda da Meena ma nayi magana bada itaba shine ita mai zuciya tawuce ta tafi garinsu”? Sosai Hajiya ke kallonshi cikin tsantsan bacin rai yace “ai shikenan Allah kiyaye, nina tafi asibiti” yajuya fuuu zai fita haryakai kofa Hajiya takirashi tace “Nura!” Juyowa yayi idanunshi sunyi jazur yakalli Hajiya tace “Nura kasani abin nan dakayi nikamawa” cikin fushi sosai Nura yace “Hajiya wai mekike cewa haka? Idanma ita nama fadan menene ba matata bace? Bazan iya ma matata fada ba? Niba mijinta bane? Itane sarkin zuciya takama ta tafi bazata iya fahimtan wat am trying to do ba, inbar Hadiza tamutu sabida Ummi? Inbar Ummi tashiga dakin sabida banso nabata mata rai eh? Things are not done like that Hajiya? Taje bazan kirata ba bazan bitaba idan tagaji da zama tasan hanya tadawo Abuja inba hakaba tayi zamant……” Tass! Hajiya ta daura mai mari abinda bata tabayiba, yadafe kubcinshi yana kallon Hajiya, dakuwa Hajiya tamai tace “kaci mai garinku Nura kaji u are very stupid, how dare you call yarinyar dake kula da mamanka all this sort of names Nura kasan bakason yarinyar nan why did you marry her? Ubanme yakaika ka aureta eh? Naga ba ita tace tana sonka ba, kotace lallai saika aureta kaika nemeta, kaiharka isa kayi magana haka akan Ummi data taimakeka da gidanka da yaranka dani uwarka, kazaci zaman ka nake agidan nan shashasha dakai zaman Ummi nake wlh agidan ma right from day one danazo itane komiba, yarinyar dake kula maka da gida da yara, tarbiyan su waye ajikin Aman da Amal Ummi, how dare u say such things about my precious daughter ina tarbiya ka da hankalin yaje eh, Nima da izinin Allah gobe zan barmaka gidan kome kaga dama kayi kuma kasani ba Ummi ka wulakanta ba ni mahaifiyar ka ka wulakanta dan yarinyar nan tadaukeni amatsayin mahaifiya, the poor thing tariga taga baka sonta baka bukatanta gwara ta koma garinsu kafin kamata kora da hali, kaji kunya Nura girmanka bai amfaneka da komiba indai wannan ne kalan rayuwan daka daukama kanka mayaudari kawai, innocent yarinya marainiyan Allah kawulakanta haka sabida burinka yacika yanzu shikenan kaje kada ka nemeta bazance kayi ba Ummi ko’ina kike Allah tsare ai Meena nada number kakarta zan kira naji kaje kayı duk abinda kakeso just know this wlh gobe zan bar gidanka kaji na rantse maka” tajuya fuuuu zata wuce dasauri Nura yataho gabanta yasha yayi kneeling tareda rike kafanta yace “Hajiya dan Allah ki yakuri baki fahimceni bane, dan Allah kada kiyi fushi dani Hajiya dan Allah dan Allah Hajiya kiyakuri” hankade kafanshi Hajiya tayi tawuce dakinta tarufe kofa tana kallon Meena dake kuka.
Ahankali Mama tace “Nura baka kyautaba a gaskiya bahaka ake zama da mata biyu ba, nasan Hadiza batada lafiya kuma i get you are doing everything possible kaga tasami lafiya kar hakan yasa ka tauye hakkın Ummi wacce itama matace agareka, hakkine akanka kaje ka ga lafiyanta akullum ranan duniya which bakayiba, ita dutse ce kwana uku bata daura ka a idoba, batai magana dakaiba tazo asibiti ai ka kaita gefe kamata magana mai dadi ba kamata koran wulakanci ba kodako da Meena kake magana ai agabanta ne, kazaci bazataji ba dadi bace mahaifiyar ka na maka fada kuma kana kiranta sarkin zuciya, Allah kiyaye, tagaji da zama zata dawo, haba Nura fisabillahi fa? Haka ake magana? Kanada kanni kuma Kanada diya mace kaima Nura haba” shafa kanshi yayi yayi huci mezafi yace “Mama gida nawa akeso naraba kaina tsakani ga Allah eh? Ga Hadiza ga Ummi yanzu kuma Hajiya eh Mama”? Cikeda tausayi tace “yanzu tunda Jamila na wajen Hadiza, jekabi sahun Ummi kaga, ka kuma gwara kiranta awaya ko Allah zaisa kasameta ni zanji da mahaifiyar ka”.
Ahankali Mama tace “Nura baka kyautaba a gaskiya bahaka ake zama da mata biyu ba, nasan Hadiza batada lafiya kuma i get you are doing everything possible kaga tasami lafiya kar hakan yasa ka tauye hakkın Ummi wacce itama matace agareka, hakkine akanka kaje ka ga lafiyanta akullum ranan duniya which bakayiba, ita dutse ce kwana uku bata daura ka a idoba, batai magana dakaiba tazo asibiti ai ka kaita gefe kamata magana mai dadi ba kamata koran wulakanci ba kodako da Meena kake magana ai agabanta ne, kazaci bazataji ba dadi bace mahaifiyar ka na maka fada kuma kana kiranta sarkin zuciya, Allah kiyaye, tagaji da zama zata dawo, haba Nura fisabillahi fa? Haka ake magana? Kanada kanni kuma Kanada diya mace kaima Nura haba” shafa kanshi yayi yayi huci mezafi yace “Mama gida nawa akeso naraba kaina tsakani ga Allah eh? Ga Hadiza ga Ummi yanzu kuma Hajiya eh Mama”? Cikeda tausayi tace “yanzu tunda Jamila na wajen Hadiza, jekabi sahun Ummi kaga, ka kuma gwara kiranta awaya ko Allah zaisa kasameta ni zanji da mahaifiyar ka”.