← Book details Marainiya Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 34

Sashe 6

Marainiya Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turus tayi ta tsaya tana kallonshi baki bude, ajiye mana Salim din yana masallaci.
Ajiye abincin tayi sannan ta dago tana kallonshi wayanshi yake dannawa hankalinshi kwance kamar bai San da mutum a dakin ba.
Har ta juya ta fara tafiya sai kuma ta dakata ta juyo kai kuma to xaman me kakeyi?
Kamar ya ? Ya tambaya.
Gani nayi ana maxa sun tafi masallaci sallah kai kuma kana xaune lafiyanka qlau, da hankalinka a jikinka kai kuma ba mace ba balle kace kana da lalura.
Dago kai yayi ya kalleta,
" so, what concerns u."?
Ya tambaya. Kallonshi tayi da kyau sannan tace
" sorry wlh Na dauka kai musulmine"
To da wa yace miki ni ba musulmi ba ya fada yana binta da mugun kallo.
Yi tayi kamar bata ga kallon da yake mata ba.
To nidai a matsayina Na musulma ' yar uwarka nake baka shawaran kaji tsoron Allah Kuma ka rike ibada. Allah da kansa yace ban hallice kuba sai Dan Ku bauta mini.
A yadda kake yanxunnan Baka bauta wa Allah ba sai yaushe xaka bauta mishi.
Shidai kallonta yake da mmkin irin karfin halinta.
Toh naji Malama jeki.
Zakayi sallan? Ta tambayeshi, ikon Allah wai me ya damekine.
Xama tayi a kujeran da ke kusa da bakin kofa,
Mlm ina guje maka mutuwar baxata, mutuwa bata sallama ba kuma sanarwa lokacinka nayi xata daukeka ko ka shirya ko Baka shirya ba, ina maka tsoron axabar qabari ina maka tsoron wutan jahannama gamuwanka da ubangiji da ya halicceka ya raya ka, ya axurtaka da ni,imominsa ya Baka lfy ya maka dukkan gata amma ka butulce masa ka gagara bauta masa.
Mu dauki misali da d'an da ka Haifa a cikinka kayi masa dukkan gata ya girma karshe ya za ya kasance marar biyayya marar jin maganan ka fi sabilillahi ya xa kaji.
Zata ci gaba da magana..yayi saurin katseta... Naji kuma Na gode insha Allah xan gyara kanwata.
Yawwa yayana Allah ya sa,nima Na gode ta tashi xata fita.
Ya sunan malamar? Ya tambaya , Mariya tace. To Na gode Mariya.

Tana fitowa sukayi kicibis da ya salim , a take ta tuno abinda yace mata rannan, Na shiga uku tace a xuciyarta amma a xahiri sai tace sannu ya Salim, baice komaiba sai kallonta da yakeyi, ganin haka sai kuma ta tsargu.
" ya Salim ko banyi dadai ba nidai gsky Na fada masa ko" ta karashe mgnn da fiskan tausayi. Gyada mata kai kawai yayi yana kuma tunanin wato ita Mariya wannan Hali AJININTA YAKE. Dan tun dazu ya dawo ya ke jin duk abinda take gayawa abokinsa.

Ko da ya shiga bai nunawa mansur yaji abinda sukayi da Mariya ba. Sai cewa yayi "mansee yane "? Ajiyar xuciya mansur ya ya sauke duk ta gama kashe masa jiki abin kunya yarinya karama take tunatar dashi ibada, kai, dole ma ya gyara.

Mansur abokin Salim ne tun suna secondary sch. Har tertiary institution, haka halinsa yake be damu da sallah ba sai idan ya ga dama yakeyi, ga shegen Neman mata, akwai banbancin Hali sosai tsakanin sa da Salim.
A ranar dai haka ya koma gida jiki a sanyaye sai jin muryanta yake kamar yanxu take masa mgn kuma ya qudura a ranshi xai gyara halayenshi.
Saidai me, kwana biyu ya rasa sukuninsa kamannin yarinya yake mishi gixo ido a bude ko a rufe, ga muryarta mai zaki da ya gagara barin dodon kunnenshi.
Shiryawa yayi cikin shiga mai kyau ya tafi gidansu yana parking a kofar gida su kuma sun fito xasu je islamiyya , ganin xasu wuce yasashi saurin fitowa , sallama ya musu suka amsa,
Zasu wuce Dan ita Mariya tama mantashi.
" kanwata ba gaisuwa?
Mariya ko baki ganeni bane.
Sai a sannan ta ganeshi "ina yini " tace kanta asunkuye " lfy "
Ya amsa da murmushi a fiskarsa, su fa' ixa ma suka gaisheshi ya amsa tukun suka wuce.

Wayarsa ya fitar daga aljihunsa ya dannawa Salim kira. Hello mutumina gani a kofar gidanku kana cikine?
No, bana nan but yanxu xan dawo kadan jira ni.
No...no problem xan wuce kawai , after all ma Na riga Na ga abinda naxo gani,
Wani irin harbawa xuciyar Salim yayi.ya daure yace me kazo ganine mutumina?
Don't worry dolema xan dawo and I will tell u.
OK sai mun hadu bye,
Toh fa , Salim dai ya shiga damuwa Allah dai yasa ba abinda yake tunani bane.

In dedication to Halima Auwal.

08161594233 for cmmt.

Luv u all.
👛👒MARIYA👒👛

51-55

By Anty Rukie(Mmn Abduljalal.)

Washegari ma haka mansur ya sake xuwa daidai zasu tafi karatu kamar dai jiya suka gaisa kuma suka ce mai ya Salim be dawoba, yace ba damuwa gobe ma xai dawo.

Ko da Salim ya dawo Hafsa taje ta sanar dashi abokinsa yaxo bai sameshi ba, yace mata ta kira mishi Mariya.

Tambayarta yayi wa yaxo daxu, ta ce mishi abokinsa Na rannan ne jiya ma yazo bai sameshi ba.
Me sunanshi? Ya tambayeta.
Nima dai bansan sunanshi ba.
Ok , kina nufin be fada miki sunansa ba.
A ah bai fada ba.
To me yace miki da yaxo?
Ni ba abinda yace min .
Tsakaninki da Allah, yace mata.
Wlh ni ya salim ni be ce min komai ba .
A ina to kuka hadu yau din? A kofar gida zamu je islamiyya. Jiya fa? Jiya ma haka. Kun gaisa ne?
Eh mun gaisa. Kiranki yayi kuka gaisa ko kuwa ?
Ya tambaya tare da tsare ta da idanu. A a nikam bai kiraniba.
OK tashi kije.
Tashi tayi tana maida numfashi wadannan tambayoyi Ai ko a kotu iyakaci , ko ina ruwana da wani abokinka .
Ke, me kikace? A a ba da kai nake ba cewa nayi yunwa nakeji xanje inci abinci.

Yau kam yayi niyyan sai ya jira xuwan mansur yaji me yake kawo shi tunda yasan baya xuwa wajenshi akai akai sai sa'i da lokaci.
Kamar jiya suka hadu bayan sun gaisa suka ce mishi ya Salim yana ciki.

Suna wucewa ya shiga ciki ya samu Salim a daki.
Bayan sun gaisa sun taba hira Salim ya tambayi mansur kwana biyu kana xuwa Baka samu Na me ya faru ne aboki?

Ba abinda ya faru sai alheri xuwa kuma yanxu nasa kafa Dan inada ajiya a gidannan.
Wani dummmm Salim yaji sai ya kanne yace, ajiya wani iri aboki?
Murmushi mansur yayi yana shafa kai . Ajiya mutum kuma mace mai muhimmanci a rayuwata.
Kafeshi Salim yai da ido , wa kenan ya tambaya.
Black beautyn gidannan.
Daure fiska Salim yayi , amma dai mansee kasan ba type dinka a yaran gidannan beside dukkansu kanana ne .
Yes Na sani she is young but believe me RENONTA
ZANYI.
Mansur ya Kira shi in a serious tone, ka sanni Na sanka kasan kuma nasan kai waye, ba xan tan tabayin SAKACIN da xai lalata rayuwar kannenaba so pls kabar mgnar nan kawai.

Saukowa yayi daga kan kujera, Salim pls joke apart, I really love ur sister believe me.
No mansur, I can't .
Salim ya xanyi ka yarda dani, me xan ce maka ka yarda dani, I am now a changed person, yarinyar nan ta canxa min tunani ta canxa min rayuwa , wlh xan Iya komai domin ta.
I can do anything to make happy, I mean it friend, ya karashe maganar kamar xaiyi kuka, shi kanshi Salim ya tausaya mishi bai taba ganin shi a irin wannan yanayi ba kuma ga dukkan alamu maganar da yake yi Iya gaskiyarshi yake fada, amma kuma wani irin hashin mansur yakeji a kasan xuciyarsa,
Kai baxai yiwu ba ,
Mansur ne ya katse mishi tunani da cewa pls frnd help me, wlh bani da wata mummunan manufa akan sister, aurenta nake sonyi pls ya karashe da fiskan tausayi.
No it can't be, let her be Mr man. Yarinyarnan is very young kuma karatu takeyi kada ka gurbata mata tunani ba xai yiyu Na barta ta hada karatu da soyayya ba.

OK Na fahimceka, but at least let me introduce myself to her, ina tsoron kar wani ya min shigan sauri,
Kaga mansur yarinyar nan ba haka take ba baxa ta saurareka bama,
Toh ka taimaka ka Sanar da ita.
Ni kuma Salim ya fada yana nuna kanshi, wannan ma ai nemawa kai rainine , to ma ince mata me?

Oh my God , Salim u don't know what am going through, u could have allow to atleast talk to her even once.

Na gaya maka baxata saurareka ba , haka dai mansur yayi pleading but all to no avail, atlast suka rabu cikin bacin rai, don mansur ya Nina zai yi duk yadda xaiyi Mariya ta so shi har ya cimma burinshi Na aurenta.
Wannan magana ta konawa Salim rai Dan ya San abokinshi kuma yasan what he is capable of doing.
Lallai dole ya dauki ya dauki mataki tun abu be yi nisa ba.

In dedication to Halima Auwal

FASAHA WRITERS🖊🖊
👛👒MARIYA👒👛

55-60

By Anty Ruky( Mmn Abduljalal)

A haka suka isa makarantar jiki duk a sanyaye, Salim, Sadiq da kuma sageer su suka yi rakiyar Dan an hana fa'iza xuwa.

Bayan an gama duk a binda ya dace an basu class ss1b. Sannan a hostel kuma blue house , komai nasu daya Dan principal da malaman Duk sun dauka tagwayene saboda Kansu daya kuma suna kama saidai Hafsa ta danfi Mariya haske.

Ana gama kwashe kaya Mariya ta juya ta kama tafiya tabar Hafsa tsaye a gunsu tana matsar kwalla.
Salim ne ya kirata ta tsaya amma bata juyo ba .Takowa yayi ya iso inda take, Mariya kuka kike, shiru ba amsa, mariya , talk to me pls.
Sai a lokacin ta samu ta fashe da kukan da take dannewa, kamo hannunta yayi har gurin motar su ya bude ya turata ciki sannan ya xagayo ya shiga shima.
Duk Sadiq Na lura dasu shima yaso binta ya mata mgn ganin Salim ya riga shi ya ci gaba da rarrashin Hafsa da ta kankameshi ta ke kuka me ban tausayi.
Chapter 6 · 0% Book details