← Book details Marainiya Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 34

Sashe 5

Marainiya Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bikin su Atika ne ya taso Nenne ta matsa dole Mariya taxo bikin ' yan uwanta Hurera, da atika.
Saida mami tayi da gaske Mariya ta yarda xataje a hakan tare da Hafsa domin duk a tsorace take.

Sadiq yasa ta a gaba da tsokana, ni dai Mariya kada ki manta da maganar mu idan Baba ya tambayeki kice kina da wadda kike so, ehe Na gaya miki Kenan.....yana mgn yana dariyan tsokana.
Bakinka ya sari danyen kashi , tace tana harararsa.
Mariya kyaleshi ke sai kinyi karatu yadda kike so zakiyi aure. Yawwa mami Na Allah ya bar minke.
Sun gama shiri yau dai sageer ne zai kaisu Dan ya jima baije ba karatu yakeyi yanxu kuma ya samu hutun makaranta.
Dai dai xasu shiga mota sadiq yace" matas karfa ki kula kowa kuma ana tambayanki ki fadi sunana"
Murguda mai baki tayi . ya sa hannu xai murda bakin tayi saurin kaucewa, cafko hannunta yayi tana kokarin kwacewa .
Sai jin muryarshi sukayi yace " Sadiq respect urself and maintain ur personality"
Saurin sakinta yai yana Sosa kai " sorry bros" yace.
Yana tunani a ranshi ko me yasa ya Salim ya sa mishi ido akan Mariya.

Shi kanshi Salim yana mmkin yadda ya tsani ya ga ko mgn mariya nayi da wani.
Wata xuciyar tace masa to kodai sonta kake. No..wannan karamar yarinyar nida nake da fadila.
Fadila 'yar kawar mami ce. Tana yawan xuwa gidansu anan taga Salim tunda ta dora ido akanshi taji ya kwanta mata, daga nan ta dinga shisshige mishi tun yana sharewa har suka daidaita Kansu suka kama soyayya.
Fadila yarince kyakkyawa, fara ce mai mulmulallen jiki da ka ganta kaga yar Hutu.ta gama secondary sch.
Yàñxu ta yi applying tana Neman admission sai dai fatan Allah ya bada sa a.
Fadila tana tsananin son Salim saboda ya mata ko ta ina .

Salim baki ne saidai ba wul ba yana da Dan Haske, kyakyawane , mai sanyin Hali Dan bai cika hayaniya ba .

Yana yawan sa manyan kaya . yana sakananama amma ba sosai ba.
Yanxu haka yana 27 yrs yan aiki ministry of finance.
Fadila Sam basa shiri da Mariya Dan acewarta tacika yawar mgn ko mai ta gani sai tayi mgn.
Tun wata rana da taxo suna Palo dukkansu Salim ya dawo daga aiki ta tashi xata je wajensa,
Mariya ta ce mata anty fadila Dan Allah in tambayeki. Tace ina jinki , ke bakya jin kunya kixo wajen saurayi .
Tace wa ya gaya miki wajensa nake xuwa tun kan kixo gidannan ina xuwa.
A a ba gidannan nake nufi ba yanxu da kika kama hanya xa kije wajansa me xaki ce masa ai abin da kunya a kya ji kunyar idanunmu ma balle Na mami.
In nice ke wlh idan mun hadu a gidansu daga gaisuwa baxan nuna alamar akwai wani abu tsakaninmu bama.
Kai wlh wasu mata ma basu da kunya , Allah yasa Ku gane , wai Ku nan a dole wayewa ko.
Ta fada tana wani tabe Baku.

Kunya, haushi, takaici, su suka lullube fadila, ji tayi kamar ta shako Mariya ta wawwanka mata mari , ji yadda yarinya karama ta kunyatata a idon mutane.
Dàga ranar ta rage zuwa gidan Dan haushin Mariya takeji koganinta bata son yi.

Luv u all

In dedication to Halima Auwal.

FASAHA WRITERS🖊🖊
👛👒MARIYA👒👛

41-45

By Anty Rukie ( Mmn Abduljll)

Sun isa da kwana biyu aka fara biki ba zama sai xirga xirgan biki suna cikin kawayen amarya atika da yake itace karama itace kusan sa'ar su.

Sun fita daban acikin 'yan matan , abokan ango da sauran samari sai kokari shigar da Kansu sukeyi su kuma duk a tsorace suke kasancewar basu saba tsayawa da samari ba. Bama kamar ita Mariya da take gudun kada babanta yaji labari yace xai aurar da ita tunda ya aurar da ' yan uwanta.

Ranar da xa'a kai amarene suka ce xa su leka Nenne kafin axo tafiya da amare xasu fita kenan suka ga wasu yara biyu suna fada ga yara an xagayesu ana kallo. Cikin sauri ta isa wajen tana kokarin raba su . sai ta samu sun rabu tana juyawa sai su ci gaba .
Bulalanta ta samu lafiyayye ta fara tsarga musu ihunsu ne ya jawo hankalin matan dake ta harkokinsu wasu hiran duniya sukeyi wasu girki wasu wanke kwanuka kowa dai da abinda yakeyi,.
Wasu daga cikinsu ne suka xo jin me yake faruwa daidai lokacin da Mariya ta dakawa yaran da suke wajen tsawa , kai duk Ku watse anan tunda Baku iya rabon fada ba saidai ku tsaya kuna kallo.. Sum sum yaran suka watse , watace daga cikin matan tace . ikon Allah lallai Mariya kin canza har kina wa yara fada basu raba fada . ta fada tana dariya tunowa da halin mariya. Watace acikinsu tace wlh kam mariyan da idan ana fada ita ke zigawa tana wakar Ku doku ba mai rabaku.ko ta mikawa masu fada kasa tana ga Na fada ga Na wasa , Wanda ya fasa yaji tsoro. Haka dai suke ta fadin abinda Mariya takeyi da ana ta dariya.
Kamo hannun Hafsa tayi, zo mu tafi ke kuma kin tsaya kin hangame baki da hanci kina kallonsu. A a Mariya barni naji ba labari akeyi ba .
Toh yi taji nikam nayi nan ta tafi tana mita kaji min mata kamar an tambayesu.
Hafsa dai biyo ta tayi tana dariya , Ai na tsaya nayi recording ma ya Sadiq ne bari mu koma zai sha labari.
Sai kuma kiyi Mariya tace mata.

Sati daya sukayi suka koma , suna isa gida suka fito da gudu suna oyoyo mami , jin muryoyinsu mami ma ta fito tana Oyoyo yaran mami suna rigerigen isa ga mami sai ganin sadiq sukayi ya nufo su guje yana dariya duk yadda Mariya taso kauce mishi saida ya sha gabanta yana oyoyo sisters.
Kauce wa tayi da sauri tana wa xai maka oyoyon kafin ta isa Hafsa ta rigata . kankame mami tayi , mami munyi missing dinki . mu fa ?
Kai ya sadiq ka damen, to banyiba asali ma mantawa nayi dakai , karya kike wlh. To shikenan gwara ma fa'iza nayi missing dinta kadan👌, amma kaida ya sageer kam lala lala ta fada tana tabe baki.
Toh ya Salim fa, cewar fa'iza . shikam sosae nayi missing dinshi banda su o' o ta fada tana wa Sadiq gwalo.
Xan kama kine yarinya, amma dai naga ya Salim ya hana .......bata gama fada ba sukayi 4 eyes da Salim din daya kafeta da idanu tayi tsit kamar ba ita ke surutu yanxunnan ba.
Karasa mana me ya hana , kaga Sadiq kyale min ' ya ta huta daga isowarta ka tsareta da surutu ko gaisawa bamuyi ba. Ta jata sukayi dakinsu jekiyi wanka kuci abinci Ku huta mariyata. Toh mamita.

Ya Sadiq ina xuwa haka? Wani abunne? Ya tambaya.
Eh naga kamar fita xakayi , eh kina bukatar wani abune? A hakan xaka fita, dubi shigarka fa. Me shigar tayi ,
Tab amma kana da matsala 3quarter da vest kasa ka fita kamar ba musulmi ba.
Matsalata dake kenan kauyanci kayan shan iskanne zaki wani ce kamar ba musulmi ba? Wa xai ganni yace ni ba musulmi ba , xa' a fada da wannan suma da katara, kumatu kamar Na inyamurai.
Ba wani nan kedai kishi kike kada wata ta kwace miki ni kada ki damu mariyata Sadiq nakine ba me kwace miki.
Mtseew kanka akeji. Kema xa'a ji naki idan na fada ma Abba ya daura mana aure kinga sai kiji dadin hanani sa kayan da bakiso nasaka.
Mtseew wlh kiran mami xanyi taga da kayan da xaka fita.
Saurin ficewa yayi yasan yanxu mami tazo sai tace magnar Mariya gaskiyace.

In dedication to Halima Auwal.

FASAHA WRITERS.🖊🖊
.
👛👒MARIYA👒👛

46-50

By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)

Bayan kwana biyu Mami ta ce Mariya ta kaiwa Salim abinci a dakinsa yayi bako. Hafsa xo mu kaiwa ya Salim abinci , Hafsa da take sallah maza kai musu kafin su fito masallaci.

Tana isa kofar dakin tayi sallama kasa kasa Dan batayi tsammanin da mutum acikiba tasa kai ta shiga.
Chapter 5 · 0% Book details