← Book details Marainiya Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 34

Sashe 25

Marainiya Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_maaruf yaje yasamu abbanshi yagayamai yaji dadi da danshi yasamo mashi suruka yace in Allah yayarda zaije gobe susamu mai martaba yanda maaruf yamashi bayani ummy batama sanshiba dadi duk yabi yamamayeshi ummy kuwa takare kukanta tafara karatu maaruf dai baikara kirantaba yanaso yaji daga bakin abbanshi tukuna bayan kwana biyu alhaji adam saleh yaje yasamu mai martaba harda maaruf din akaje mai martaba yaji dadi amma kaaan zuciyarshi yana tuna danshi saidai ba yanda zaiyI dole ya amince musu dan idan yarshice bazai zubamata ido hakaba dolene yabata farinciki tunda dai itabatayi maganaba yagaya masu duk yanda abin yake adam sale yajinjina kai yana tausayawa mai martaba da kuma danshi dam ganin yake koda yaushe yarima zai iya dawowa saidao bayanda zaiyi tunda yaga danshi baidamuba mai martaba yanisa yace saidai wani hanzari ba guduba zaaji tabakin yarin inta amince to shikenam mum yakira awaya yace tazo itada ummy suna zuwa tana ganin maaruf saida gabanta yafadi tace nashiga uku yazubarmin da mutunci shiko kashe mata ido yayi tayi saurin kauda kanta mai martaba yamasu bayanin abinda yakawosu nan ummy tayi hamdala daya nuna batasanshiba amma kuma ai bazaitaba yuwuwaba kuka tafashe dashi na tsaka mai wuya kaba zaki baya damisa yazanyi dakaina ni MARAINIYA CE meyasa wannan abubuwan suke faruwa dani ya Allah kasa naci wannan jarabawar taka_

_kuka tajeyi sosai duk tabasu tausayi shikanshi mai martaba daurewa kawai yajeyi wannan alamarin Allah yanunamana karshenshi ummy tashi tayi dagudu rayi cikin gida maaruf kamar tayi ihu rashinyin maganarta zaiji dashi ko kukanta sarki yadubi abokinshi yace kuyi hakuri dolene zatayi kuka amma zan shawo kanta kuma dolene taji kunyar fadar wani abu ina tausayin yarinyar hakane inji baban maaruf dolene tayi kuka abata lokaci tayi nazarinkuma dan Allah kada atilastamata hakadai sukaita shawara yanda zasu bullowa alamarin bayan suntafi mum ta iskota har daki tana lallabata itama hawayen takeyi ummy ki yarda da kaddara haka Allah yatsara maki kinga is for ur onw gud kiyi aure dan bazaki tabbata hakaba kiyu kokari kesake wata rayuwa kozakiji dadin rauyawarki waninkukan ummy tafashe dashi tace mum bazan tabayin aureba zanjirashi koda kuwa shekara nawane wani tausayinta taji tana cewa dolene muzabamaki rayuwa mai kyau bazaki tabbata hakaba haka mum kefada acikin ranta afili kuma kallon ummy kawai takeyi tana hawaye gwanin tausayi_
[2/13, 2:23 AM] ‪+234 703 962 5239‬: 💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐🎀 *MARAINIYA CE* 🎀💐💐

💐🎀💐
*_NA MAMAN AHMAD_*
*_(MARDIYA KAOJE)_*

🎀
💐 *67* 💐
🎀

_bayan mum ta tabbatar ummy tabar kuka taje tasamu mai martava tace yarinyar nam tana cikin matsala kodon tasamu farinciki dole mu aurarda ita koda kuwa rammu bayaso dan natabbatar maaruf zairiketa da amana yaron yanada hankali sosai gaskiya kika fada nafisa ki tika kwantar mata da hankali kinunamata gaskiya yarinyar inasonta kamar yanda nakeson yayana nasota da yarima amma Allah bai nufaba ya Allah duk inda yaronnam yake Allah kasa yanacikin koshin lafiya yadawo dashi gida idan kuwa mutuwa yayi Allah yagafarta masa ameen mum tace tana share hawaye mai martabama haka yakasa daurewa shidai kullum adduarshi Allah yabaiyana masa danshi duk inda yake haka suka aje shawarar zasu bita ahankali agurin maaruf kuma massage yayima ummy nadan Allah tadaina yimashi asarar hawayenta da kalamai masu dadi dukda akan kada tasa damuwa aranta idanshibe mijinta bayanda zatayi tarika addua kawai zabin Allah shine agaba takuwaji dadin massage din dan yarage mata radadinda takeji addua shine makamin mumini_

_bayan kwana biyu ummy takoma makaranta haka tagayawa dija duk abinda yake faruwa dijama abin yabata tausayi wannan shiake kira da tsaka mai wuya amma tabata shawara tacire duk wata kunya tunda su mum su sukaga yadace tayi hakan tunda bahaka zata tabbataba kumashi yarima baasan inda yakeba ko yana raye ko yamutu oho ummy dai tashiga tsaka mai wuya bataji zataiya wannan abinba kamar amafarki maaruf kuwa baya gaji kullum cikin yin massage yakeyi yanamai nuna irin sonda yake mata kuma yana kwantarmata da hankali yana nunamata duk abinda tagani yafaru to daga Allahne kuma yakamce mata danta hafiz yana gaisheta takanyi murmyshi tace maaruf kana wahalda kankane abinda bazai yuwuba kwanaki sunshede yau kusan wata biyu da wannan maganar kullun cikin bata baki mum takeyi tana nusarda ita gaskiya ummy takance abata lokaci maaruf kuma baI fasa turamata massages ba amma bata taba reply ba kamar zaiyi hauka haka yakeji saidai yayi tawakkaki ga Allah yasan komai daga gareshine yau kam mum tace tanason tagayamata magana daya zatayi ko bazatayiba kuma tasani duk abinda yabiyo baya najiran dazatawa yarima ita tajawakanta mum tayi hakane donta nunamata yin auren shine mafita itama batadon tasoba ummy tace mum kiyi hakuri amma abani wata shidda inyarima baidawoba duk abinda kuka yanke na yarda dashi mum taji dadin wannan hukuncinda ummy tayanke_

_mum tana adduar Allah yabaiyana yarima kafib lokacin mum tanisa tace kina ganin haka yayi baiyi nisaba aa mum koshifa dannaga kundamune kumafa da sharadi mum tace to fadi muji ummy ta nisa tace koda kuwa minti daya yarage adauramin aure yarima yadawo dolene afasa daurin auren wanI mugun dadi mum taji amma bata nunaba tace to ummy duk zaa fada masu haka suka aje magana tagayawa sarki yakira abban maaruf yace yazo su tattauna bayan yazo harda matarshi maman maaruf yagayamasu duk yanda sukayi da ummy da sharadinta suka jinjina kai nan takira maaruf ayawa tagayamashi komai baiji ko darba saima wani dadi dayaji hajiya saratu tace amatsayina na alkali zanyi adalci duk sanda yarima yadawo indai baa daura aureba to lallai zaabashi matarsa haka sukare firarsu aka kira ummy suka ganta hjy saratu tace masha Allah shiyasa dai danta yalike ashe baiyi zaben tumun dareba bataga laifinshiba amma tana tausayamashi duk ranarda yarima yafawo dan tafahinci yanason ummy sosai baitaba cewa yanason wataba tunda matarshi tarasu sai akan ummy Allah yasa rabonshice haka suka tafi bakin maaruf kamar gonar auduga nan yakira ummy har yagaji bata daukaba yamata massage yna nunajin dadinshi da alkwarin bazata taba danasanin kasancewa dashiba itadai tabe vaki kawai tayi tace kai kasani_

*68*

_*washington dc*_
_yarima yananam sai abinda yayi gaba bayako tunanin nigeria balle wayanda kecikinta yama manta yataba aure jin leenah yakeyi kamar ranaa dan akwaita da iya karuwanxi kudi kuma cinsu takeyi ba kakkautawa kawarta kuma tananam sai abibda sukaga dama sukeyi fairooz yayi kudi sosai Allah yabudamashi har gidan kanshi yasiya batu haihuwa kuma leenah batamasa ranaba shikuma baidamuba dan dama basanta yakeyiba kawai yadai rasa yanda zaiyine danma taiya karuwancine har yakejin dadin zamada ita kuma yake mata duk abinda takeso yana daya daga cikin best drs daakeji dasu a asibitin rayuwarsu sukeyi ta turawa saidai wani lokaci yakayi mafarkin wata yarinya tanata binsa shikuma yana gudu saboda wata damisa da take tsakiyarsu tana huci yakancema yarinyar tazo sugudu tare amma ina yarasa wacece wannan yarinyar dabaya sati baiyi mafarkintaba har yasamata sunada my dream girl yanason haduwa da yarinyar amma baisan inda zai gantaba yanajin wani abu gameda ita kuma koma wacece tana cikin wani hali yanaji ajikinsa takayi ta tunaninta wani lokacin har bacci yakesonyi dan yaganta wata rana kuma yakanga damisar tana bacci amma a lokacin baya ganin yarinyar sai yahangotacan ciki wata korama tana sallah yayita jira bata zuwa haka zai koma baisamu ganintaba mafarkayya dai kala kala_

*bayan wata biyar*
_kandece zaune hakince sai lissafin kudi larai nazaune kusada ita tace umma wallahi jinake kamar wani abu zaifaru inna auti saleem anya kuwa nidai akoma dan chairman ne ahadani dashi amma wannan kowa yaji zaice asiri muka masa vuge bakinta kande tayi tace shegoya sakarai mai kashin tsiya yau saura kwana uku biki kike cewa afasa gashi ambiyamana makka dagani har babanki ga kudi paca paca kada inkaraji wallahi ranki zai baci tana wannan magarne taji anbankado kofa anshigo uwar saleem ce his excellency hajiya hajara da saleem ko sallama basuyiba kande tasaki baki suda sai yanda tace masu humm hjya hajara da tashigo da yan sanda tace arest dis woman nanko sukazo dasauri suka kama hannun kande sukasamata ankwa larai saida tayi fitsari ciki wando saleem yace Allah yaisa wallahi nidama nasan ba cikin hayyacina najeba mezanda kazama irinki just look at ur self yatoshe hanci kande kam sakin baki tayi tace shikenam hjy hajara tace to anniyarki batayi tasiriba nasamoma dana magani ai hankalima bazai dauka tasamu kande tayi mata mari uku masu kyau saleem yakara mata biyu yadube kande saida yadunkule hannu yamata wani wawan nushi_

_kande tarike baki najini yace saina daki kudina da kukaci yan iska matsiyatan banza makwabta sunji sai kuka aketayi yan gulma sukafara zuwa suna kallon wasu na daman munsani asirine haba aiko makaho yaga wannan yasan ba banzaba nan saleem yasamu larai yaita kidinta saida tabar motsi kande kuja take kamar ta mutu baki na jini malam ne yashigo yaji duk abinda yafaru yaceshi baruwanshi duk inda zaa kaisu barywanshi yayi Allah waddai da hali irinna kande haka aka kadasu mota aka tafi dasu mutane sai cewa suke Allah yakara nan malam yafara tunanin toko tanada hannun cikin batan yarima zato dai zunubine amma akwai wabi abu su kande baa diresu koinaba sai police satation aka kullesu cikin sell sai kuka sukeyi amma kande vana nadama takeyi dan kudirinta datafita saitayi abinda yafi wannan larai kam duk jikinta ciwo yakeyi baba kuwa baiga zaijeba insun iya su mutu acam kuma bawanda zaigayawa ko ummy bata saniba tsakanin ummy da maaruf kuwa yanzu tadan saki jiki daaji dan yanada addini yana mata waazi sosai tafara sakin jiki dasji dan yaiya soyayya hartana tunanin ashe akwai sauran farincikinta arayuwa a yanzu takanji zata iya aurensa basaida shawaraba shiko ahankali yaje binta yana bata uzuri baya fushi da duk abinda zata mashi zuwa yanzu kuwa harsa hafiz suna gaisawa dashi a waya mummy ma yake kiranta tanajin yaron kamar ita tahaifeshi yarima kuwa tanamai addua kuma har yau babu wani labari har sun sadakat sun rasashi......_
[2/13, 2:24 AM] ‪+234 703 962 5239‬: 💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐
💐💐🎀 *MARAINIYA CE* 🎀💐💐

💐🎀💐
*_NA MAMAN AHMAD_*
*_(MARDIYA KAOJE)_*

🎀
💐 *69* 💐
🎀
Chapter 25 · 0% Book details