← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 24

Sashe 9

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su'ad idar da sallarta kenan tana zaune saman dadduma tana azkhar Ummi tashugo ɗakin ta zauna gefan gadon su'ad ɗin ahankali tafara magana da sigar lallashi "Su'ad kiyi hakuri ki ɗauki kaddara kisa aranki auranki da Fahad babu fashi naga wannan dogon yazo mana gida, bansan dame yazo ba amma inaji ajikina kamar da abinda kuke kullawa, yanzu dan Allah bakiji kunyar Mami ba agabanta kike nunawa ɗan uwanta baki sonsa ke bakisan kara ba, tunda aka haifeki take ɗawainiya dake koni dana haifeki bansan wahalarki ba, ita komai tasamu ke dukkan takardun kadarorinta sunanki ne komai ta samu Su'ad burinta akoda yaushe tasaki farinciki ashe kodan wannan bazaki so ɗan uwanta ba, inda watace bazata taɓa goya maki bayaba amma dayake kaunar datake maki daga zuciyarta ne haka ta zaɓi farin cikinki akan na ɗan uwanta, koma ba wannan ba ashe bazaki iya cikawa Daddynki wasiyarsa ba daya bari, dan Allah amatsayina na wacce na haifeki na rokeki daki hakura da Fu'ad ki rungumi kaddararki Fahad insha Allah bazakiyi nadamar auransa ba zakiyi farin ciki" tunda Ummi tafara magana Su'ad ke kuka gaba ɗaya Ummi tagama kashe mata jiki amma yaya zatayi da zuciyarta kan abinda takeso, ita bata taɓa son Ankul ba batajin kuma zata so shi, bare takaisu ga aure, to inta auri Fahad maita aura, kanin Mami zuciyarta tabata amsa tayaya zata iya zaman aure da wanda takewa kallon kanin mahaifiyarta, koda ta auri Fahad batajin zata iya basa kulawar da mace take bawa namiji ina zatakai kunyarsa, batasanma Ummi ta futa a ɗakinba sai data ɗago kanta da niyyar tayi magana kana taga ɗakin ba kowa sai ita, Fu'ad massages yayi mata ya koma asibiti wajan sarkin mota za'ayi masa karin jini.

Washe gari Ankul sassafe yaɗauki hanyar karaye karfe goma acan tayi masa bai wani jima ba ya juyo kai tsaye asibitinsu ya wuce bai biyo gida ba, tinda yazauna a office ɗinsa yakasa aikata komai ko feshan ɗinsa Dr hafis yaturawa su, Dr hafis daya tashi ya shuga office ɗin Fahad harya zauna fahad baisan yashugo ba saida yasa hannu yataɓa sa kana ya kallesa da sauri yana ajjiyar zuciya kamar wanda yai kuka.

"Amma bakada lafiya kwana biyun nan naganka sai'a slow" Fahad ya É—ora kansa jikin kujera ahankili kujeran ke juyawa dashi yace "Lafiya kalau nake kawai inada damuwa ne akan Su'ad" Dr Hafis dariya yayi "Su'ad Su'ad ko yaushe dai maganarka akanta nagaya maka kafaÉ—a mata awuce wajan katsaya kana kallon ruwa sai kwaÉ—o yayi maka kafa tukunna" sauke numfashi Fahad yayi tareda futar da iska mai zafi daga bakinsa

Yace "Na nawa kuma asheni ina zaune yaron nan Fu'ad yagama siye zuciyarta" nan dai Fahad yasanarwa da Dr Hafis komai "Kabar damuwa kayi addu'ar neman zaɓin Allah hakan zaifi wannan damuwar da kake ciki wacce zata iya haifar maka da ciwo" godiya yayiwa Dr sannan suka mike suka futa tare dan tuni lokacin tashinsu yayi.

Fahad koda ya koma gida wayar Fu'ad yakira yajima bai É—aga kiranba sannan ya É—aga.

"Aboki kana inane ko ka koma"

"A'a ina kano asibiti jiya wajan tahowarmu motarmu ta faɗi sarkin mota yabugu aka kaganshi a kwance tun jiya ba cigaba ɗazu naiwa mai martaba magana yasoma shirya masa tafiya cairo anjima jirginsu zai tashi" Fahad wanka kawai yayi ko abinci bai ciba ya wuce wajan Fu'ad wanda tun a wayar dayaji muryarsa yasan yana tare da damuwa, sanda yaje kallo ɗaya yamasa yaga yayi wani zuru zuru shidaman haka yake yanzu ne damuwa zata saka sa rama kilama nan gaba kaɗan saiya kwanta zazzaɓi bayan sun kai sarkin mota airport suka juyo Fahad dake tuki ya kalli Fu'ad daya ja uban tagumi kansa kurum ya girgiza yana faɗin

"Duk kabi kasa damuwa aranka kalli yanda kayi wani ziru zuru kamar wanda yatashi daga jinya" murmishi Fu'ad yayi yana kallon Fahad dayaci gaba da faÉ—in "Ni naruga nabar maka Su'ad harma naje karaye munyi magana da Baban karaye kasan girman ka awajena ya wuce na auri abinda kake so tabbas dan son Su'ad ina sonta tun randa tazo duniya naji banida wata mata inba itaba!" Fu'ad yaÉ—ago kansa yana kallon Fahad kana yace

"Bazan iya auran abinda kakeso ba aboki kai kafi cancanta daka aureta saboda kafini sonta, kai karayu da kaunarta ni kuma yan watanni nayi a soyayyarta dan haka bazan iya auranta ba ni na bar maka bazan aureta! ajje ni gidan Anty Hadiyya" mirmushi Fahad yayi yanabin Fu'ad da kallon tausayi

Yace "Bazan ajjeka ba da gidanta kake sauka naga inkazo kano ko kwana nawa zakai muna tare sai wannan karon ashe daman har mace takai girman da zata raba amintarmu" lumshe ido Fu'ad yayi yana murmushi

Yace "Su'ad tayi kaÉ—an ta rabamu muje ni daman banson naje gidanne ta ganni ta shuga damuwa banson damuwarta ko kaÉ—an" Fahad baice komaiba yaci gaba da tukinsa "Inason nasai kayan sawa banzo da shirin kwanan garin nan ba sai gashi ina shirin yin na biyu"

"Wanne kaya kuma zaka siya, ga nawa nan nasan zasuyi maka saidai tsayinko" kallon juna sukai sai kuma suka fashe da dariya atare suka furta "Maika tuna" nan ma dariyar sukayi kamar basune a damuwa ba Fahad yace "Natuna rayuwarmu ta scaundry inban wanke Uniform É—ina ba na saka naka su Moha suyita tsokanata saboda yanda rigan ke sakkomin har kusan kasa oh rayuwa kaga yanda muke da Moha kamar baza'a rabuba amma tunda muka kammala school bamu kara ganin juna ba ko yana raye" har sannan murmushi bayyane kan fuskar Fu'ad yace "Allah nima nakasa mantawa da Moha koya zama sojan ko yaya oho Allah dai yasake haÉ—amu wata rana" har suka karasa cikin gida suna hira, gidan shuru kamar babu kowa da'ace da ne da tuni koba yaran gidan zaka samu Mami da Ummi a falo suna hira amma damuwa yanzu tasa kowa zaman tunani a É—aki shiyasa ba wanda yasan da zuwan Fu'ad gidan.

Karfe huÉ—u baban karaye yaiwa gidan tsinke tunda ya zauna yakewa Mami faÉ—a wai ta zuga É—an uwanta yaje ya gaya masa ya fasa auran Aminatu "To kisani wallahi koda zan É—aura aure gobe da safe Fahad yasakomin ita da dare to saina É—aura aidai na cika wasiyyar É—an uwana kuma ku sani na maida É—aurin auran nan da kwana shida ranar asabar mai zuwa aure babu fashi!" yagama faÉ—ansa ya tafi ko gaisawa basuyi ba, Ummi daÉ—i taji sosai nan take tasoma kiran waya tana sanar da bikin Su'ad asabar, Fahad jiki a sanyaye yamike daga wajan yakoma É—akinsa anan yasami Fu'ad kwance kan gado yana kuka kamar wani mace dan gaba É—aya yana jiyo faÉ—an baban karaye daga inda yake saboda yanda yake maganar cikin faÉ—a da fusata

"Fahad maiyasa banda sa'a a soyayya kowacce mace naso bana samu abaya naso Suwaiba kamar hauka amma ta yaudareni yanzu naso Su'ad wacce itama ke sona kamar ranta amma kaddara ta rabamu Fahad mai nayiwa soyayya take azabtar dani haka nagama soyayya bazan karaba!" mikewa yayi yana yiwa Fahad sallama ba yanda Fahad bai lallashi Fu'ad ba kan yazauna zuwa safiya sai yabi jirgi ya koma amma yakafe har yakai kofar futa daga falon farko na gidan yaja ya tsaya jin Su'ad na kiran sunansa kallo É—aya yayiwa fuskarta bai sake kallonta ba saboda yanda zuciyarsa ta tsinke

"Daman kana gidan nan ban sani ba yaushe kazo"
"Ɗazu muka shugo da Fahad yanzunma tafiya zanyi" yafaɗi haka yana cigaba da tafiya da ɗan gudu take binsa saida yafuta compound sannan ya tsaya "Zantafi Su'ad kiyi biyayya ga iyayanki duk ɗa nagari yana son ganin farin cikin iyayansa kisa aranki daman can Allah bai kaddara zamuyi aure ba! iyakarmu soyayya kimanta dani ki rungumi mijinki Fahad zakiji daɗin zama dashi fiye dani insha Allah zan dawo ran asabar wajan ɗaurin auranku" kam ta kame waje ɗaya jin maganganun Fu'ad bata ankare ba taga Fu'ad yana shirin fita daga gidan wani ihu ta saki tareda faɗin Fu'ad Come back please!!! ta zabura zatabi bayansa taji an riketa duk da idanunta a rufe suke da ɓacin rai tasan wane saboda jin kamshin sa datayi "Kasakeni Ankul kasakeni nabisa kana kallo farin cikina zai tafi" gaba ɗaya Fahad jiyake kamar yayi kuka ganin yanda jikin Su'ad ke ɓari kamar mai shirin tada aljanu🤭"Saketa Fahad" Ummi dake kallonsu tun ɗazu ta faɗi shiko sake kankameta yayi danshi yafara tunanin ba lafiyarta kalau ba "Kasake ta nace! tabisa suje can ta nemi wasu iyayen su ɗaura mata aure da shi saboda ke bakisan tawalkali ba, shi yana namiji ya iya tafiya yabarki ya gaya maki gaskiyya amma kin kasa ɗauka saboda idaninki sun rufe da makauniyar soyayyarsa" Fahad baiyi aune ba sai kawai gani yayi Su'ad ta sulale ta faɗi kasa tana wani irin numfashi daba shi ba hatta Ummi dake faɗa saida hankalinta yatashi, Mami da sauri tayi kan Su'ad tana faɗin

"Shikenan kun kashe min ita ku bakuda asara ni kuka cuta Su'ad dan Allah kitashi ke kaɗai nakeda ita ke nake kalla ako da yaushe naji sanyi a raina ke kika maye min gurbin da a kullum ke damuna a zuci Aminah...😥
[6/4, 7:48 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹

Story and weitting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️

Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
S ANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

12&14

Fahad ya kinkimi Su'ad yasata a mota gaba ɗaya hankalinsa yatashi asibitinsu ya wuce da'ita Dr Hafis ya karɓeta ruwa ya jona mata tareda mata alkurai harya samu tadawo normal tai barci, Hafis yadafa kafaɗar Fahad yace "Agaskiyya kubi yarinyar nan a yanda takeso abokina nasan duk akan maganan nan ce dan Allah abarta kasan yanda jininta yai mugun hawa kuwa, wallahi kuka cigaba da kuntata mata zaku iya rasata gaba ɗaya"
Chapter 9 · 0% Book details