Sashe 17
Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mami kuka take sosai jikinta sai karkarwa yake yaya Jabeer ya riketa zuwa motarsa muka shuga zuwa gida, sosai masoyana suke ta zuwa tayani murna,wasa_wasa saiga Mami ta kwanta ciwo kamar bazata tashi ba kwananta biyar a asibiti sannan taji sauki aka sallamota.
Rayuwa nake wata irin rayuwa mara jin daɗi kullum cikin kuka muke nida Ameera musamman in mukaga hoton Ankul dole tasa Mami ta ɗeɓe duk hotunansa dake cikin gidan, karatuna naci gaba namaida hankali sosai wajan zuwa makaranta cikin shekaru biyu na kammala natafi low school.
__________Ahankali yafuto daga cikin tsadaddiyar motarsa fuskarsa ba ɗigo annuri, yajima tsaye nan jikin motar yana kallon cikin gidansa, kafin ya saka hannu yaɗau jakar Laptop ɗinsa ya saɓa a kafaɗarsa yafara takawa a cikin compound ɗin, har zuwa tsakiyar falo, da gudu wata kyakkyawar yarinya da bazata wuce shekaru biyu ba ta futo daga ɗaki ta ɗanesa cikin muryarsu irinta yara tace "Papi welcome back" lumshe idanu yayi tareda sumbatar kumatun yarinyar
Yace "My Princess yaya gida" futowa tayi daga ɗakinta tayi kwalliya sosai cikin kananun kaya riga da wando wanda suka matukar amsar jikinta, kokarin shugewa jikinsa take yaɗaga mata hannu, ya ɗauki yarsa suka wuce ɗakinsa, dage kai Baraka tayi tanabin mijin nata da kallo tarasa gane kan wannan bahagon mijin nata shekaru uku kenan da auransu amma babu wata shakuwa a tsakaninsu bata taɓa ganin dariyarsa ba sai ranar data haifa masa Baby taga yana murmushi sanda yagaya mata yasawa yarinyar Aminatu Su'ad kowa da Su'ad yake kiran yarinyar amma shi yabi ya kakaba mata Princess tarasa wanne irin so Fu'ad yakewa Princess indai yana gida to yana tare da'ita harta kwana tare suke da'ita ko ita sai yayi sati bai haɗa makwanci da'ita ba indai ba bukatarsa ce takawosa ba,
Wanka yayi yafuto yana goge ruwan jikinsa da karamin tuwel Princess ya kalla wacce ke zaune saman gado tana game a wayarsa murmushi yayi yanajin kaunar yarinyar tana kara shugarsa, lumshe idanu yayi yana tuna farkon haÉ—uwarsa da Su'ad irin soyayyar dasukayi har zuwa kallon karshe dayayi mata ranar É—aurin auranta da Fahad, da sauri ya zauna gefan gado yadafe kansa yana sake tuna rayuwarsa tunta yarinta shida Fahad yatuna yau shekaru uku kenan ba wanda ya nemi a wani acikinsu, da sauri ya É—akko tsohon sim É—insa na nageria ya saka cikin wayansa yai copy É—in lambar best freind kamar yanda yai save É—in numbar, yakira yafi sau goma amma maganar É—ayace lambar bama ta aiki, sake dafa kansa yayi ya kira Abokinsa Usman bayan sun gaisa yace
"Usee asamarmin jirgi inda dama zuwa gobe nakeson sauka a nageria"
Dariya Usee yayi yace "Turaki ikon Allah yau kuma nageria tai kira kenan kaida madam ko kai É—aya?"
"Nida Princess banda Mamanta"
"Angama mai girma turaki"
Ko Baraka bai gayawa tafiyar ba sai sanda zasu tafi airport yace "Zamu tafi gida da Princess ba daÉ—ewa zamuyi ba bana tunanin zamu wuce one week"
Rau rau tayi da idanu kamar zatayi kuka tace "Ni wanne laifi nayi dabaza'a tafi dani ba, shekara uku fa rabonda naga mamata"
Batare daya kalleta ba yace "Ni tawa mamarma mutuwa tayi samada shekaru rabona da'ita yaya nayi saike da kullum sai kinji muryanta kuna vidio call kina ganinta"
Tana kallo jirginsu yatashi tana hawaye ta tare texzii tahau zuwa gida zuciyarta kamar zata fashe saboda bakin cikin Fu'ad ita kam sam bazata taɓa ɗorar da farin cikin aure ba babu wata soyayya a rayuwar auran nasu share hawayanta tayi tana faɗin "Anty Jamila duk ke kika jamin dan haka nima bazan taɓa baki haɗin kai wajan cikar burinki"
__________Jin ana kwankwaso kofa yasa na mike da sauri na buÉ—e dan daman zaman jiransa nake, tsayawa yayi a bakin kofar ya harÉ—e hannuwansa a kirji ganin an buÉ—e kofar yasa ya shugo da sallama saida ya zauna na kawo masa lemu da ruwa, bai sha ba saima wani kallo dana lura yana bina dashi, ganin na kamasa yana kallona yasa ya É—auki wayarsa ya waske yana dannawa.
Binsa nayi da kallo dan ganinsa saiya tunamin da Ankul É—ina ba kaÉ—an ba suke yanayi da Uncle É—in dande wannan yafi Uncle tsayi, sanye yake cikin kananun kaya blue jeans da black shart katse shurun namu nayi ta hanyar faÉ—in "Nura ko"
Kallona yayi yana wani taɓe baki kana yace "No Am Nurein"
"Ok Mamin bata nan taje nan zoo road amma ina zaton tana hanya ni sakon data bani tace nura zan bawa kai kuma kace Nurein so inaga ba naka bane"
É—agowa yayi yana kallona karaf idanunmu suka sarke cikin na juna kallon ido da ido mukai wanda hakan ya haifar min da wani bakon yanayi
Kyauda idanuna nayi daga cikin nasa ina danna wayata Mami nakira na shaida mata tayi bako
"Su'ad bako kuma ba Nura bane"
"E Mami wannan ya ce sunansa Nurein dariya Mami tayi kana ta ce yajirani gani nan a hanya"
Ajje wayata nayi saman kujera na kunna Aljazira ina kallon labarai, shuru nayi ina kallon labaran
Kallona yake yana É—an murmushi ganin yanda nabada hankalina kacokan wajan kallon "Malama kinzo kin kunnawa mutane kallon saiki fassaramin abinda suke cewa danni dai ba fahimta nake ba"
Taɓe baki nayi ina cigaba da kallona bance komaiba
"Toki canza mana tasha inbazaki fassaramin ba"
Dafe kaina nayi nace "Nifa na gaya maka ban san mai suke cewa ba"
"Ai yanda kika zurawa tibi kyakyawar fuskar nan taki kawai yatabbatar min da kinsan mai suke faÉ—a" bai jira cewata ba ya É—auki remote ya canza tasha, zanyi magana kenan Mami da Ameera suka shugo da É—an tsallanta Ameera ta karaso wajena ta mikomin ice cream
tace "Anty na ga tsaraba na maki"
"Kai nakuwa gode my Deauther kamar kinsan anjima nakeson zuwa havila nasha ice cream"
Idanun Nurein akaina yake gaida Mami cikin girmamawa yace "Ma'ma tace nazo na karɓar mata sako wajanki"
"E munyi waya da'ita tace zakazo shiyasa da zan futa nabawa Su'ad ta ajjiye maka" ina kallon ya lumshe idanunsa yabuÉ—e su akaina, Mami tabasa sakonsa tai hanyar shuga É—akinta
"Mami wannan Nuran fa bai sha ko ruwa ba balle lemun dana ajje masa"
Juyowa tayi tana kallonsa "Nura nanfa gida ne amma ko ruwa baka sha ba" shafa kansa yayi yana murmushi ya ce
"Mami nagode na koshi ne banjima da shan ruwa ba a mota na"
"Ummm to inma dai ta fulani kayi kai ka juyo" murmushi yayi yamike ya É—auki ledan kayan da Mami tabasa ya tako zuwa kujerar danake kai yasa hannu ya É—auki wayata yajima yana dannawa kana ya ce
"Maine pin É—in faÉ—amin" yafaÉ—a da murya kasa kasa
"Nima ban sani ba" nafaÉ—a ina maida hankalina kan kallon danake, Amira yakira da hannusa suka futa tare da wayata a hannunsa, jimawa kaÉ—an Ameeran ta kawomin wayata tana dariya "Anty waifa tambayata yayi kinada saurayi,ni kuwa nace masa mijinki ya rasu" ta karasa faÉ—a jikinta a sanyaye
"Sai yace maki mai kuma" dariya yayi wai damancan da shi kika dace nama basa number É—inki" wayana kawai na É—auka na shuge É—akina.
__________Hannu yabawa Chiroma suka cabke tareda rungume juna, Chiroma ya É—auki Amina yana shafa kanta ya ce "Baby Su'ad ce yau a kasarmu kinzo kiga takwararki" harara Fu'ad ya zabgawa Chiroma tareda yin gaba ya shuge É—aya daga cikin tawagar motocin da Mai martaba ya turo su É—auki Fu'ad É—in, ko cikin mota hira suke sosai shida Chiroma har suka karasa gida, a compound yasami Umma cike take da É—okin ganin One boy É—inta musamman daya sanar mata tare yake da Baby Su'ad, rungumesa tayi tana dariya ta shafa kansa tareda jan kumatunsa kamar wani karamin yaro ta ce
"Ah lalle nayi farin ciki da ganinka gaduk kanin alamu maman baby tana kulawa dakai sosai irin wannan kumatu haka" dariya yayi tareda bin bayanta zuwa ciki tana É—auke da Baby Su'ad, kai tsaye sashinsa ya wuce yai wanka yaÉ—an huta har zuwa dare sanda Umma takirasa yazo suci abinci da mai martaba.
"Masha Allah my Son ka girma amma wannan baturiyar tazo kenan bazata koma ba" mai martaba yafaÉ—i haka yana nuna Baby Su'ad dake kwance saman cinyarsa tana wasa da rawaninsa
Fu'ad zama yayi kasan carfet yana murmushi yake gaida mai martaba dake amsawa fuskarsa sake, tare suka ci abincin suka gama sannan suka gangara hira anan Mai martaba ke cewa Fu'ad
"Al'ameen banason zamanka acan wata kasa nafison zamanka nan kusa dani kullum shekaruna daÉ—a ja suke girma yana daÉ—a kamani, ko yaushe mutuwa zata iya É—aukata in baka kusa akwai matsala, kasani akwai masu harin kujerar nan ni kuma nafi aminta dakai, shiyasa nayi magana da Ummanka akwai babban fili dana sai maka tun kwanaki kadawo ka gina asibiti ka zauna kusa dani hankalina zaifi kwanciya"
Fu'ad shafa sumar kansa yayi wacce ke kwance luf tasha gyara ya ce "Allah yaja da ranka ina godiya amma ni nafison zaman wata kasa can hankalina yafi kwanciya idan ina nan yakan tunamin da abubuwa da yawa waÉ—anda sun kasa goguwa a zuciyata" yafaÉ—i haka da raunanniyar murya.
Umma murmushi tayi cikeda tausayi dan tun sanda taji sunan yarinyar Ameen ta tabbatar da har sannan da sauran soyayyar Su'ad a zuciyar Fu'ad "AMEEN Kayi hakuri kamanta komai kadawo kasarka da zama hakan zaifi maka"
"Insha Allah zan dawo Umma" yafaÉ—i haka yana mikewa dan zuwa cikin gida yagaida sauran matan mai martaba.
Girgiza kai Umma tayi tareda faÉ—in "Narasa wanne irin so Ameen kewa yarinyar nan ba yakasa mantawa da ita kullum addu'a nake masa amma kamar tiri kalli yanda ya koma da Fu'ad mutum ne mai faran faran ko yaushe fuska a sake amma ni rabon danaga dariyarsa harna manta"
Murmushi kawai Mai martaba yayi ya mike zuwa sashinsa, duk yanda Fu'ad yaso ya zo kano wajan Fahad abin ya gagara ko yaushe suna tare da mai martaba in anka gayyaci mai martaba zuwa wani taro saiya turasa shida Chiroma gaba É—aya ya gaji shifa saboda haka bayason zaman bare yafi kaunarsa zaman nesa fiyeda gida.