← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 24

Sashe 2

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nidai sakin baki nayi ina kallonsa yanda naji yayi hausa raÉ—au,kin shuga motar nayi har sanda nafara jiyo jiniyar motar yan sanda motace Hilox baka cikeda yan sanda da bindigogi sai wata farar mota a tsakiya sannan wata Hilux É—in shake da yan sanda har sun gifta mu naga sunyo baya sun tsaya dai dai inda nake da sauri É—aya daga cikin yan sandan yadiro daga saman mota yabuÉ—e murfin karamar motar da suka sako a tsakiya,Yah Mukhutar ya fito daga motar yafara takowa inda nake tsaye, kamewa nayi ina binsa da kallo harya karaso inda nake na sara masa tareda faÉ—in
"Ouwr wellcome sir"
"Wellcome Su'ad mai kike tsaye anan wajan"
Uncle FAHAD ne ya ce nazo na tafi da bakonsa gida" hannu yaya Mukhtar yabawa bakon balaraben suka gaisa kana ya umarce sa daya shuga motarsa, ni kuma ya tusa keyata zuwa tasa motar inda na tarar da babbar yayarmu Fateema zaune aciki, itama tambayata tayi mai nake tsaye a bakin titi, nabata amsa kamar yanda na bawa mijinta, ba jimawa muka koma gida na shuga ciki hannuna É—auke da Sajad É—an Anty Fatima, "Ke kuma ina kika samo wannan yaron" Mami ta tambayeni tana amsar Sajad dake hannuna, kafin nabata masa Daddy ya shugo wani tsalle nayi na É—ane Daddy ina masa sannu da zuwa tareda tambayar sa yaya jikinsa.

Ummie dake biyeda bayan Daddy ta daka min tsawa tana faɗin na sakesa banga bashida lafiya ba, niko ko sauraron ta banyi ba naci gaba da makalkale Daddy na da shima yake murnar ganina yana faɗin "Auta me Mamie take baki ne naga kin yi kiba kamar ba keba" dariya nayi ina bin kofa da kallo ganin shugowar Uncle Fahad da bakon balaraben sa, da gani zakasan ba karamin farin ciki sukayi ba da ganin juna ba, nifa har ga Allah mamaki bakon nan ke bani yanda naji hausa raɗau a bakinsa kamar jakin kano😂 yana gaida su Daddy yanda suke amsawa cikin sakin fuska ya tabbatar minda sun san sa, bayan sun gama gaisawa kai tsaye Uncle Fahad yaja hannun balaraben bakon sa suka wuce sashin samarin gidan mu.

Mami ce ta umarceni dana kaiwa su Uncle Fahad abinci, nakuwa É—auka zuwa É—akin sa suna baje saman bed sai hira suke, nayi sallama na shuga ina ajje warmars É—in hannuna bakon balarabe ya kalleni kallon dana kasa fassara sa wanda ban cika ganin irinsa awajan kowa inba Uncle É—ina Fahad ba "Wai da gaske wannan Su'ad ce ta girma haka?" bakon ya tambayya yana kallon Uncle Fahad, zama nayi a kan kujera ina kallon Fahad dan naji amsar da zai basa ai kuwa naji yana faÉ—in

"Itace mana kaga tazama yammata ko?" ɓata rai nayi ina kallon Uncle Fahad batare da nace komai ba, nasaba sosai da Uncle Fahad kusan komai tare mukeyi dashi kama daga cin abinci buga kollon kafa ya kaini makaranta ya ɗakkoni, dan duk cikin samarin gudanmu banida Amini kamar Fahad, ganin zaman danai na jiran yazo muci abinci ne yasa yace "Yau inada bako bazanci abinci dake ba kije kuci tareda Daddy ko Ummi" na ɓata rai tareda mikewa ina faɗin "Ai dai bakon naka zai tafi! zaka dawo ka same ni, ni kuma a sannan zan canza Amini na komawa yaya Yazeed" ina gama faɗar haka na fuce a fusace ina bugo masu kofa, murmushi Fahad yayi yana bin Fu'ad da kallo ganin yanda yabi Su'ad da kallo harta futa bai kawo komai a ransa ba yace

"Kaganta nan yar rigimar gidan nan kenan haka take hukuma ce ita saida lallashi" murmushin gefan baki Fu'ad yayi batareda ya kalli inda Fahad yake ba yana sauke ɓoyayyar ajjiyar zuciya.

Kwanan Fu'ad biyu a gidanmu bana shuga sabgar sa haka shima bai shuga tawa, ko gaisuwa bata taɓa haɗamu ba, haka kurum dai inason ganin sa shiyasa sau tari nake zuwa wajan Uncle Fahad innasan suna tare, wasa wasa nafara gane son bako ya shuga zuciyata.

Mami tana zaune a bedroom É—inta na shuga da sallama zama nayi kusada ita ina wasada zoben hannuna da Uncle Fahad ya kawo min kwanakin baya dayaje Saudiyya umara

"Mami wannan bakon balaraben wai a ina Uncle ya samo sa yazo ya zaunawa mutane a gida duk ya hanamu sakewa nida Uncle ɗina" mami kallona tayi tana murmushi "Abokin Fahad ne tun zamanin scoundry harma da jami'a, shekarunsa goma kenan yana CANADA acan yake aiki tun bayan kammala karatun su na jami'a Ƙanin mahaifinsa yasamar masa aiki a can" mikewa nayi na koma ɗakina ina shirin tafiya makaranta yau lacture ɗin yamma nake da'ita, tsab nagama shirina cikin doguwar rigar Atamfa kamar yanda na saba nayi kusan rabin kayana duk dogayan riguna ne acewar Uncle Fahad wai doguwar riga tafimin kyau shiyasa in muka kai ɗinki kannace komai yagayawa telor ɗin amin doguwar riga, tun ina mita harna saba koni ɗaya nakai ɗinki ita ɗin nake cewa amin saboda ina son duk abinda Uncle ɗina keso, kamar yanda shima yake son abinda nakeso, rolling mayafi karami nayi na futo ina baza kamshi, Uncle na tarar a falo shida bakonsa wanda yakafe ni da lumsassun idanuwansa kamar na maijin barci, harna karaso na zauna hannun kujerar da Uncle ke zaune akai

"Kinyi kyau besty irin wannan tashin kamshi haka sai ina?" "Uncle inada lacture yau na shirya ka tashi ka kaini"

"Besty futa nakeson nayi a hospital inada feshan amma bari na ajje ki inyaso in kika tashi zansa Seteven ya É—akko ki" mikewa mukai atare muka jera zuwa wajan adana motoci na gidanmu.

Ahankali Uncle ke tukin motar kamar bayaso yanayi yana kallona wani bin yayi murmushi wani bin ya kashe min ido É—aya nidai bance masa komai ba harya ajjeni cikin school É—inmu yana É—agamin hannu har yabar harabar makarantar tamu, jinai an ruko hannuna na juya da sauri ina kallon kawata Ameera dake min dariya

Tace "Nakasa gane maku keda Uncle Fahad kamar wasu masoya ko yaushe kuna tare jibi yanda yake wani ɗaga maki hannu yana kashe maki idanu kamar yana gaban budurwar sa" dariya nayi tareda soma tafiya ina faɗin "Ina kikaga Amini ya koma masoyi akwai abota mai karfi a tsakaninmu shiyasa kowa yake mana kallon masoya amma ni sam bama haka da Uncle, ban taɓa masa kallon masoyi ba yanzun dai na faɗa soyayya wacce nake zaton zata wahalar dani danna ɗakko da zafi"

har muka gama lacture na futo zuciyata makale da tunanin bakon Uncle, zuciya da ruhi na É—okin komawa gida nayi tozali da kyakkyawar fuskarsa mai cikeda annurin dake sanyaya zuciyata, wajan dana hango motar gidanmu na dosa kofar baya naketa kokarin buÉ—ewa amma taki buÉ—uwa sai ta gaba dana ga anbuÉ—e min da sauri na shuga duk azatona Uncle ne saida na zauna ina buÉ—e jakata batare dana kalli wanda ke ciki ba nace "Uncle amma kayi saurin dawowa" jin baice min kala ba yasa na É—ago ina kallonsa, kallon kallo mukai ido cikin ido ni nafara É—auke idanuna daga cikin nasa tareda sauke ajjiyar zuciya take wata kasala ta rufeni, nai saurin É—ora kaina saman seat na motar na lumshe idanuna ina jin yasoma tafiya da motar munyi tafiya mai nisa naji yayi parking gefan titi sai sannan na buÉ—e idanuna ina kallon sa, hannunsa duka biyun yana saman stearin motar yayinda ya É—ora kansa saman sitiyarin yana kallona da lumsassun idanun sa masu samin kasala kamar bayaso yasoma magana da muryar sa mai matukar daÉ—in ji da sauraro kamar baya so

"Ke bakya yiwa mutane magana saidai kirinka azabtar da zuciyar mutum!" da sauri na ɗago na sake kallonsa kashe min ido ɗaya yayi tareda ɗage gira, da murmushin sa daya doki zuciyata, bance masa kala ba saima gyara zamana danai "Kinsan yanda nakejin zuciya ta kuwa?" zuciyata bugawa take ko wanne bugun numfashi yana bugawa da sonki da kaunarki!, Su'ad hakika zuciyata tayi sartse da kaunarki ina sonki! ina sonki Su'ad!!, da sauri na ɗago ina kallonsa dan tabbatar da gaske bakon Uncle ne ke gayamin yana sona....✍️

Free book ne idan kinbi link baiyi ba kimin magana kai tsaye ta wannan lambar 07039793439 ki save Number ta da Mamie Yusuf Daboo
[6/4, 7:46 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA* 🌹

Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️

Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

2-3
Kafin na gama tantance shin da gaske daga bakin Fu'ad maganar ke futowa na kuma tsinkayo miryar sa yana cewa "Ki tausayawa jaririyar zuciyata ki amshi soyayyarta na taɓa soyayya a can baya da wata wacce na mato a kanta kullum mafarkina da burina shine tazama matata ashe ita ba da gaske take sona ba yaudara ta take sai daga baya naji labarin auranta da wani bani ba! ni bana yaudara ba kuma nason a yaudare ni, mutum ne ni kaifi ɗaya idan nace E! to bazan taɓa canzawa ba nace a'a, Su'ad dan Allah karki yaudare ni in kinsan kinada wanda kikeso karki ɓoyemin zuciyata bata iya soyayya ba in inason abu haukan so nake masa So nake masa bana wasaba, kaunarki ta shugeni tun kallon farkon danai maki Su'ad"

Tsit nayi a zuciyata ina tunanin Shin wai wacce amsa zan bawa Uncle Fu'ad shin na amshi soyayyar sa kona ja aji, batare dana gama shawara da zuciyata ba najiyo ina magana "Ina sonka Uncle Fu'ad nima dan Allah karka yaudare ni ban taɓa soyayya ba banma taɓa yin saurayi ba ko yaushe idan wani yazo wajena Uncle baya bari ya kuma dawowa yace yafison nayi karatu mai zurfi kaima na roke ka muyi soyayyarmu cikin sirri karka bari ya sani!"

"Bakida matsala dani bazan taɓa bari Uncle ɗinki yasani ba nidai fatana ki soni sona gaskiyya! ina mai tabbatar maki auranki zanyi nan bada jimawa ba" sosai muke soyayya da Uncle Fu'ad munyi wata iriyar shakuwa musamman a waya mukan ɓata lokaci muna waya musamman cikin dare inda muke musayar kalaman soyayya, zuciya ta tuni ta narke a kaunar Fu'ad ta yanda nake jin inban aure shi ba bazan taɓa iya zaman aure da wani ba, gaba ɗaya na basa dukkan soyayya ta.
Chapter 2 · 0% Book details