← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 24

Sashe 7

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jingine yake jikin bishiyar sab sab data kawata wajan iska na kaɗawa a hankali yajima a wajan ya kaɗaice kansa, gaba ɗaya bayason hayaniya ko kaɗan shiyasa yazame daga cikin sauran mutanan dasuka rage a gidan dan tuni wasu sun tafi tunda angama naɗin harma anyi walima, wayarta yaketa faman kira tana ring amma ba'a ɗagaba, tun daga nesa Juhaina take hango Fu'ad a nan rayuwarta ta duniya ba namijin datake so samada Yarima Fu'ad hankalinta duka yana kansa shiyasa ma takasa kula ko wanne saurayi amma shi ta lura sam hankalinsa baya kanta kwanakin nan takejin raɗe raɗin wai yana son wata yarinya a kano, ahankali ta karaso wajan tana murmushi bishiyar dake kallon wacce yake jiki taje ta tsaya tana faɗin "Yaya Turaki ashe kana nan anacan cikin gida ana nemanka, Umma tace nazo nan tasan bazaka wuce nan ɗin ba" batare daya daina danna wayar dayake dannawa ba yace "Kice gani nan zuwa" ɓata rai Juhaina tayi kana tace "tace kafata kafarka" fara tafiya yayi tabisa da sauri danya fita sauri kasancewarsa dogo shiyasa yakeda sauri, saida ko yarugata shuga sasin Umman, yasami Umma da Anty Jamila matar Abbi ɗinsu baiko kalli inda Antyn takeba ya zauna kusada Umma ya ɗora kansa saman kujera ya lumshe idanu ahankali yace "Umma duk bana cikin nutsuwata wani iri nake jina kamar wanda zan rasa wani abu arayuwata!" Umma ajjiyar zuciya tayi ahankali tana kallon Fu'ad tace "Al'ameen ba abinda zai sameka sai alheri wannan nauyin da'aka ɗaura maka ne yasa kakejin haka, kazama jarumi mana kaida ke shirin zama sabon sarki😹" murmushi yayi tareda mikewa ya wuce sashinsa dake cikeda abokansa ciki harda Fahad, Anty Jameela kwafa tayi tareda girgiza kai tana bin Fu'ad da kallo wanda yai burus kamar bai ganta ba, fuuu ta fuce daga falon ranta na suya da watsin da fu'ad yayi da ita, tabbas saita basa mamaki tayi alkawari saita lalata rayuwarsa saitayi silar da zai rasa duk wani farin cikinsa harma da sarautar da ake son naɗasa dan wannan turakin da aikai masa taga alamar sharar fage ne.

Fu'ad can bedroom ɗinsa yashuge yana sake kiran layin Su'ad haka kurum yakejinsa wani iri muryarta yakeso yaji kozai sami nutsuwa, wannan karon bugun farko ta ɗaga muryarta a sanyaye ta masa Allah yasa alkhairi da addu'ar Allah yataya ruko "Princess naji muryarki ba dai dai ba" kamar zatayi kuka take faɗin "Barci nayi na gaji shiyasa kaji muryata haka" sake gyara kwanciya yayi yana faɗin "Ban yarda ba indai kina cikin damuwa kema kinsan ina ganewa faɗamin kawai maike faruwa" fashewa tayi da kuka, gaba ɗaya ya ruɗe harda tashi zaune yadafe kai🤦‍♂️ "Oh Baby gayamin maike damunki inbaki gayamin ba billah yanzu zan kamo hanyar kano batare da kowa yasani ba" shagwaɓe murya tayi "Banida lafiya zazzaɓi nake tun safe Ummi taki kulani Mami kuma bata nan bare ta kaini hospital" komawa yayi ya sake kwanciya "Raguwa zazzaɓin kikewa kuka tonan da watannima haihuwa zaki, wacce tafi zazzaɓi wahala, kisha ko paracetamol ne anjima zan kiraki naji yaya kikeji" kai kurum ta girgiza masa saboda wani tausayinsa daya mamaye zuciyarta tayaya zata bari a rabatada Fu'ad wanda yai soyayya akaro na farko baiji daɗiba yanzuma ace bazai sameta ba, ai wallahi ko sama da kasa zata haɗe koda tsiya koda tsiya tsiya sai an aura mata Fu'ad idan suka ki kuwa wallahi guduwa zatayi tashuga duniya dadai ta auri Uncle wanda takewa kallon kanin uwa.

Fu'ad da Fahad da dare suka shirya cikin koriyar shadda wacce Fu'ad ya ɗinka masu, sosai sukai kyau komai nasu iri ɗaya suka saka sai suka futo kamar wasu twince inka gansu inba saninsu kayiba zakace uwa ɗayace ta haifesu saboda kamanni dasuke ɗanyi kaɗan saidai Fu'ad dayafi Fahad fari da tsayi, Fahad ba fari bane can shidai baza'akirasa da baki ba hakaza baza'ace masa fariba yanada tsayi kaɗan amma saboda yanada kiba saita shanye tsayin nasa, Suna hakimce a bayan mota yayinda Sarkin mota kejansu, har zuwa G R A gidansu Fu'ad yazo gaida mahaifinsa dayazo garin jiya da dare basu sami haɗuwa ba saboda hidama dasuke da mutane, Anty Jameela suka samu a falo taci uban kwalliya tana hakimce tanacin Apple, Fu'ad ko kallon inda take baiyi ba kai tsaye ya wuce sashin Abbi ɗinsa, ya mugun tsanar matar nan tunda take ƙazabtar masa da kanwarsa guda ɗaya tilo dayakejin duk duniya bayada sama da'ita yana matukar ji da Deejah akanta zai iya rabuwa da komai indai zatayi farin ciki, Fahad dakebin Fu'ad da kallon mamaki yace "Amma naga kamar Anty Jamila muka wuce a Falo ko bamu gaidata ba" taɓe baki Fu'ad yace "Saime to dan bamu gaidata ba haifarmu tayi!" karaf maganar a kunnan Antyn dake shirin shugowa sashin murmushi tayi tareda laɓewa har suka gama gaisawa da Abbi saida taji suna sallama kana tai saurin ɓuya a bayan labule saida suka futa ita kuma ta shuga, Washe gari sassafe Anty Jamila taiwa Abbi karyar zataje gidansu yajirata ta dawo bazata jimaba zata dawo saisu wuce Kaduna inda can Abbi ke aiki, bata doshi gidan nasu ba kai tsaye hanyar wani daji ta yanka a motarta tajima tana gudu a motar nan cikin jejin kana ta sauka a motar da jingina tareda rufe idanunta tasoma karanto wasu ɗalasimai kafin tarufe bakinta wata iriyar guguwa mai karfi tayi sama da ita🙆‍♀️🏃‍♀️🤭

Zainaba zaune gaban mahaifinta dake cin tuwo, saida tajira ya gama ci sannan tace "Baba waiya maganarmu ne ta Fahad wai haka zanyita zama nifa indai ba gidansa ba wallahi bazan sake aure ba, kuma zuwan danaima rannan na gano wata babbar masifa dake shirin faruwa damu domin na gano son Su'ad a cikin idanun Fahad" Baba ya bushe da dariya yana faɗin "Wannan shine kuskure na karshe da Fahad zaiyi idan har yasake ya sake aure Allah ne kaɗai zai fuddashi daga tarkona amma badai mutumba"😂dariya Zainaba tayi tana jinjinawa Baban nata ganin ashe shima har yanzu hankalinsa nakan Fahad ɗin "Ai baba basai kayi komaiba ni kaɗaima na ishi Fahad inada tarin abubuwan dana tanadar masa matukar yai kuskuran auran wata batare daya maidani ɗakina ba...✍️

Inkinsan kinason karantawa kuma zakina yin commeny to maza yi save ɗin wannan lambar 07039793439 da Mami Yusuf Daboo kimin magana zanyi adding naki a group ɗina🙏
[6/4, 7:46 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹

Story and weitting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️

Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

9&10

Fahad cikeda kewar Su'ad yashugo gida kwana biyun nan dayayi babu ita ba karamin ɗaga masa hankali yayi ba musamman jiya zuwa yau gaba ɗaya taki ɗaga kiransa a waya, kai tsaye ɗakin Mami ya shuga ganin ba kowa a falon sai hanne mai aiki, Su'ad na kwance kan gado ta lulluɓa da katon bargo jiya zuwa yau ita kaɗai tasan mai takeji a zuciyarta batajin zata iya hakura da soyayyar Fu'ad data gama mamaye mata dukkan zuciyarta, ɗakin shuru ba motsin komai saina zubar ruwa dayake jiyowa daga bathroom, harya juya zai futo azatonsa Su'ad ɗince ke wanka, jiyowa yayi jin saukar numfashin mutum a bargo janyo bargon yayi tareda saurin zama gefan gadon a ruɗe yake faɗin

"Besty bakida lafiya ne" taɓa jikinta yayi yaji zafi sosai dafe kansa yayi yace "Kinsan kina zazzaɓi kikazo kika lulluɓa da bargon nan kinaso kimin asara ko" kallon inda yake banba saima tsaki da naja tareda juya fuskarta na daina ganinsa, hawa yayi saman gadon sosai yana matsawa kusada niba hasale nace "Ka futar mana daga ɗaki Fahad banason ganinka banason sake ganin fuskarka" dafe kai yayi🤦‍♂️cikada damuwa ya sauka daga gadon yana kallon Su'ad da mamakin maganarta, futowar da Mami tayi daga bathroom yasa ya kalli Mamin yace "Mami maiya sami Besty naji tana magana kamar wacce aljanu suka taɓa"

Mami jingina tayi da kofar bathroom tana kallon Fahad da duk damuwa ta bayyana karara a fuskarsa tausayin ɗan uwanta yakamata tasani ba karamin so Fahad yakewa Su'ad ba saidai yayi sake yayi wasa da damarsa tuni wani yariga sa shuga zuciyar Su'ad "Fahad maiyasa zakamin haka? taya zaka sami Kanol ka gaya masa kanason Su'ad waya gaya maka haka ake soyayya ina mai umartar da lalle ka janye batun auran nan domin yata tanada wanda takeso har sunyi alkawarin aure" da sauri ya zauna gefan gado saboda jirin dayaji yana kokarin kayar dashi, "Mami tayaya zan hakura da soyayyar da zuciyata ta rayu da'ita samada shekara ashirin! inason Su'ad banajin akwai wani namiji a duniyar nan daya fini kaunarta, itace rayuwata zuciyata gaba ɗaya itace ni" yakarasa faɗa hawaye suna biyo kuncinsa "Fahada na rantse da Allah koda son Su'ad zaiyi ajalinka saika barta, inba haka ba babuni babu kai kaje kanemi wata yar uwar bani ba!" tana gama faɗar haka ta koma bathroom saboda wani kuka dake kokarin taso mata na tausayin ɗan uwan nata guda ɗaya jal daya ragemata anan duniya, Fahad kallon Su'ad yayi wacce ke kuka kamar ranta zai futa jin maganganun su Mami wai ita yaya zatayi da ranta shin Aminci zata zaɓa ko kauna, sosai kukanta ke taɓa zuciyar Fahad jiri na ɗibansa haka ya fuce daga ɗakin zuwa nasa ɗakin ko takalminsa bai cire ba ya kwanta saman gado tareda fashewa da kuka.

Yaya Jabeer wanda yafuto daga É—akin Ummi kasancewar tare suke da Fahad basusan da zuwan baban karaye ba sai yanzu daya dawo Ummi ta faÉ—a masa komai, turus yaja yatsaya sanda ya shuga É—akin Fahad ya gansa kwance yana rizgar kuka kanar wanda akace masa Mami ta rasu, gaba É—aya Jabeer ya kiÉ—ime É—ago Fahad É—in yayi yana faÉ—in "Uncle lafiya kake kuka haka?" ruke Jabeer yayi "Jabeer kataimakeni yaya zanyi da zuciyata Su'ad bata sona tace bazata aureni ba!" Jabir dafe kansa yayi shi dariyama Fahad É—in yaso basa hakan yasa yace "Shine zaka tsaya kana wannan kukan sai kace wanda akaiwa mutuwa wallahi kaji na rantse matukar ina raye Su'ad batada wani miji inba kai ba barima kagani"
Chapter 7 · 0% Book details