← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 24

Sashe 12

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Horn É—in motarsa dana jiyo yasa na futa da sauri na buÉ—e masa get,yashugo da motar na maida gate É—in na rufe na karaso wajan motar na buÉ—e masa murfin motar, yafuto yana dariya tareda sakani cikin jikinsa ya sumbatar bakina yace

"Kinyi kyau sosai besty bakiga yanda doguwan rigan nan tai maki kyau ba" sosai naji daÉ—in yabon da yai min hakan yasa na kuma shugewa jikinsa ahaka muka jera zuwa ciki, saida nakaisa har É—akinsa na haÉ—a masa ruwan wanka ya shuga yana tsokanata inzo na tayasa wanka, na futo daga É—akin da gudu ina dariya, Allah yasani kunyarsa nakeji banajin akwai wata rana da zatazo wacce zan iya tayasa wanka, ina nan falo zaune ya futa sanye da wando 3 kwata da farar t shart mara nauyi, kusa dani ya zauna ya jawoni jikinsa yana shafa gashin kaina

"Waini yaushe za'a daina jin kunyata saboda Allah ace wankama har yanzu da kaina nake baza'arinka yimin ba" rufe idona nayi alamar jin kunya ina dariya kasa kasa nace

"Nifa bazan iya ganinka ba kaya ba ajikinka ai kunya zanji" dafe baki yayi yana dariya kasa kasa

"Ok yanzu nagane laifin nawa ne, aiko yazama wajibi yau saina cire wannan kunyar dake tsakaninmu Allah yakaimu dare" murmushi kurum nayi tareda mikewa na kawo masa abinci na ajje bisa carfet dan nasan Ankul tun tuni bai fiyason cin abinci a dannig ba, sosai yaci abincin yana tsokanata inata dariya muna nan zaune muna hira har aka kira mangariba yafuta masallaci ni kuma na wuce É—akina nai alwala.

Ankul bai shugo gidan sai wajan karfe takwas da rabi lokacin har nayi shirin kwanciya bayan nayi wanka na saka night wear na zuba humra sai tashin kamshi nake banji shugowar sa ba kasancewar harna fara barci sai mutum naji cikin bargo ya haÉ—e jikina da nasa, na buÉ—e baki ina shirin yin ihu ya saurin haÉ—e bakina da nasa, yanda yake kissing É—ina yasa jikina yaÉ—auki rawa Sosai yake min wasu kalar abubuwa wanda sam bansan dasu ba, gaba É—aya yafuta hayyacinsa niko har sannan jikina rawa yake musamma sanda naji yana kokarin shuga jikina sosai nake kuka da rokonsa amma baimasan inayi ba saidai cak ya tsaya yana maida numfashi lokacin dayai kokarin shuga jikina J É—insa yaga tai wani irin kankancewa da sauri ya janye jikinsa daga jikina ya kwanta gefena yana maida numfashi, ban fuskanci komai saima zato danai ko rokonsa danake ne yasa ya tausayamin yafasa abinda yai niyya amma yanda naga yana numfashi yasa na kunna light da sauri tausayinsa ya kamani ganin yanda ya haÉ—a gumi aruÉ—e nace

"Ankul lafiya maiya sameka" janyoni yayi jikinsa tsawon lokaci yana cikin wani yanayi yanda idanunsa sukayi ja yasa na ruÉ—e na soma kuka,

"Ankul na amince gani kayi abinda kai niyya dani inda zaka dawo dai dai amma ni tsoro...hannunsa yasa saman laɓɓana alamar nayi shuru, hawaye naga sun zuba daga idanunsa yace

"Bazan iya maki komai ba Su'ad bansan iya tsawon lokacin dana É—aukaba batare dana gano cewar bani da cikakkiyar lafiya ba nidai nasan har sanda muka rabu da Zainaba lafiya ta kalau" sam ban gane inda zancan nasa ya dosa ba hakan yasa gaba É—aya hankalina ya kuma tashi aruÉ—e nace

"Bakada lafiya Ankul tashi to muje hospital kona kira Dr Hafis yazo ya duba ka"

"Ba rashin lafiyar jiki nake nufi ba kalli nan" yafaÉ—i haka yana nunamin J É—insa, kallon inda ya nunamin É—in nayi da sauri na runtse idona saboda gamon danayi, Fahad yana murmushi yace

"BuÉ—e idonki ki kalleni ki gane rashin lafiyar danake nufi ya zamuyi" yanzu kam nagano abinda yake nufi

"mu gayawa Mami nasan zata samo maka magani"
"A'a karmu gayawa kowa mubar wannan sirrinmu ne, zan nemi magani bansan da matsalar bama da tuni nasamo magani, wannan yazama sirri nidake karki gayawa kowa dan Allah"

"Haba Ankul tayaya zan iya gayawa wani wannan matsalar ai tamuce dagani sai kai" rungumoni yayi jikinsa har barci ya É—aukeni baiyi barci.

Fahad dayaga Su'ad tayi barci tashi yayi yai wanka ya gyara jikinsa ya É—akko system É—insa ya soma binciken magani daya dace ya sha.

Tun sanyin safiyar lahdi yaketa shirya kayansa cikin trabiling bag fuskarshi fal da damuwa ga kansa dake masifar sara masa saboda damuwa idanunsa sunyi jawur sosai kamar wanda yai kuka,kofa yabi da kallo ganin tayi motsi cak ya tsaya yana bin Khadija data shigo ta zaune kan sofa ta fashe da kuka "Yaya Prince yanzuma tafiya zaka kuma yi ka barni ni ɗaya?" Khady ta faɗa cikin kuka sosai, rigar hannunsa ya jefa saman bed da sauri ya tsugunna gaban Khady yasaka hannunsa cikin nata yanaji inama shine yake wannan kukan inama shima zai iya kukan nan ko zuciyarsa zata masa daɗi "Khady yi shuru dan Allah ba laifina bane laifin Abie ne na gaya masa bana son tafiyar nan amma ya kafe dole wai saina fara aiki a asibitin legus nima zanso ace an barni nan na rinka ganinki ko yaushe amma insha Allah na maki alkawari zan rinka zuwa duk karshan mako please Khady ki daina kukan nan" cikin kuka Khady ta gyaɗa kanta tana bin ɗan uwan nata da kallon tausayin rasa masoyiya da yai, Khady da Juhaina daketa rawar kai tare suka raka Prince har filin jirgin sama saida yatafi sannnan suka dawo gida, a legos gida da motar hawa asibitin dazai fara aiki dasu suka basa kai tsaye yafara aikinsa ba ruwansa da sabgar kowa indai ba hospital zai je ba to bazaka taɓa ganinsa a waje ba kullum yana gida kamar mace,

Sauri sauri yake shirin futa bayason makara saboda karfe tara yanada feshen É—in dazaiwa c s, takwas saura ya shuga hospital É—in tun daga resepsion yake amsa gaisuwar ma'aikata yanda suke basa girma kai kace shine mai asibitin a mutumche yake amsa gaisuwar saidai fuskar nan tasa tamke ba ko É—igon fara'a haka yake haka suka saba ganinnsa shiyasa basu wani damu ba.
Bai tsaya a ko'ina ba sai kofar katon office É—insa tamkar falon wani gidan saida ya zauna saman kujera ya sauke ajjiyar zuciya tareda cusa hannuwansa duka biyun cikin gashin kansa yana fuzzar da iska mai zafi daga bakinsa, shirye shiryan shuga tiyata yafara yi ta hanyar canza kayan jikinsa ya shuga É—akin tiyatan.

Anty Jameela na murmushi ta damkawa Suwaiba rafas ɗi nyan dubu dubu guda uku "Ga somin taɓin kuɗin aikinki nan bazan baki sauran ba sai aiki ya kammala"

Murmushi Suwaiba tayi daÉ—i takeji sosai a ranta da ganin wannan uban kuÉ—in wai duk nata ne hakan yasa tace "Bakida damuwa Hajiya aiki kamar angama sane gobe insha Allah tun safe zanwa garin legas tsinke na ruga naga inda yake da gidan dayake zaune abu É—aya zaki bani makullin gidan"

"Au kinga na manta wallahi gashi" tamika mata makullin bayan ta ɗakkosa daga jakarta, mikewa Suwaiba tayi tana wani juyi kamar tana gaban mijinta🤭dariya Anty Jameela tayi bayan taga futar Suwaiba daga ɗakin, harda tsallanta na murna gobe iwar haka burinta ya cika an ɓatawa Fu'ad suna shida sarautar saidai yagani anayi💃

Fu'ad tunda yashuga asibiti bai futo ba sai tara na dare gaba É—aya agajiye yake jin kansa, ta restaurent ya biya yayi take away sannan ya wuce gida wanka yafara yi saboda gajiyar daya kwaso, jiyake inama yanada mata tabbas yau da saidai su raba gajiyar nan, abincin yaci yaÉ—an hau online bai jima ba yafara jin barci haka yasa ya kashe datan ya wuce bedroom.

Dare yayi sosai ahankali take juya kanta cikin barci kafin ta farka a firgice tana salati, salatin datayi shiya tashi mai martaba dake kusa da'ita yana barci, a kiÉ—ime ya farka yana tambayar "Asiya lafiya naganki haka maiya sameki wani abune ya faru?"

"Lafiya kalau ranka ya daÉ—e amma wani mafarki nayi, hankalina yatashi anya ko One boy yana lafiya" Mai martaba maida kansa yayi ya kwanta tareda lumshe ido kana yabuÉ—esu akan matar tasa "Lafiya kalau É—anki yake É—azuma saida mukayi waya dashi lokacin yana hospital yace bai koma gida ba" Umma sakkowa tayi daga kan gadon ta shuge toleit mai martaba yabita da kallo yana sakejin son matar tasa uwar gidansa yana sake shuga ransa musamman ganin yanda ta damu da lamarin Fu'ad ko yaushe batada magana saita Ameen yayi kaza ko yaranta data haifa bayajin tana yiwa so kamar yanda takewa Fu'ad, da Khadija duk da sauran matansa suna zargin son datakewa Fu'ad badan Allah bane dan tana ganin nan gaba shine sarki shiyasa take sonsa, shidai yasani ba haka bane son datakewa Fu'ad tun yana yarone sau tari Ummu kafin ta rasu tasha bata Fu'ad ya jima awajanta shiyasa suka shaku sosai, Umma tafuto ta shimfiÉ—a dadduma ta tayar da sallah tana rokon Allah yakare mata É—anta ya nesantashi daga abinda tayi mafarkin yasamesa yanzu, sanda ta gama addu'o'inta ta shafa ta koma ta kwanta sannan ta lalubi wayarta taga karfe 03:44 am lambar Fu'ad ta buga tajima tana ring sannan yaÉ—aga aÉ—an tsorace yake tambayar Umman lafiya

"Lafiya kalau One boy kawai cewa nayi bari na tashi É—ana ya ribaci daren nan da koda raka'a biyu ce ta nafila" dirowa yayi daga kan gadon yana murmushi yace

"Na gode Ummana na mike kuwa alwala ma zanyi nayita sallah daga nan har safiya ina rokon Allah yakarawa Ummana lafiya da nisan kwana tayita bani kulawa har zuwa taga jikokina" dariya Umma tayi ta kashe wayar ta shige jikin mijinta tana murmushi, Fu'ad bai koma barci ba sai bayan sallar asuba daya dawo daga masallaci ya koma barci bayan yayi karatun kur'ani izifi uku yai azkhar sannan yakoma ya kwanta,dan yau bazai shuga hospital ba sai huÉ—u na yamma.
Chapter 12 · 0% Book details