← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 24

Sashe 24

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Mirmushi yayi tareda danna wayarsa ya karata da kun nan sa yayi sallama bayan sun gaisa da mahaifin nasa yake tambayarsa "Abie har yanzu baka zoba gashi gobe É—aurin aure fa"

Abie na dariya ya ce "Dole sai nazo nayi zaton tunda ga maimartaba ni basai nazo ba tunda ko nazo É—an gayya nima zanzama"

"Abba kazo, aurena fa yanzu saika ki zuwa bikina?"

"Ameen baka da kunya ni kake gayawa bikinka" Fu'ad yana dariya ya ce

"Abba kaifa abokina ne da mai Martaba ne shine bazan iya faÉ—a masa haka ba"

"Shikenan zanzo goben mu haÉ—u a kano can naga za'a É—aura auran nima zaman nan ya isheni ga tarin ayyuka ga Jameela taki zaman Abuja narasa zaman me take anan?"

Fu'ad a ransa yace zaman samin ido mana amma a fili saiya waske da cewa "Abie aure kawai zaka kara anan kai zamanka da amaryarka anan ita kuma taci gaba da zaman nan É—in"

"Ba ruwana idan taji wannan maganar taka zaku kwashi yan kallo" Abie ya katse wayar yana dariya.

BARAKA

Duk yanda takeso ta jure takasa yau tunda gari ya waye takejin xuciyarta ba daÉ—i daurewa kawai take ganin gidan nata yasoma tara baki, zuciyarta ce ta wani irin bugawa ganin fitowar Fu'ad cikin shiga ta alfarma, yana sanye cikin dakakkiyar shadda mai sheki da walwali kallo É—aya zakayiwa shaddar kasan bata kananun kudi bace saboda yanda take maiko da É—aukar idanu ga wani kamshi datake fiddawa na musamman, hula takalmi agogo duk kansu jajaye ne, bakaramin kyau yayi ba kai bazaka ce yanada aure ba har yana da y'a, yanda yake washe hakora yana dariya shi kaÉ—ai ma ya isa ya bayyanar maka da tsantsar farin cikin dayake ciki, gaisawa yake da yan uwan Baraka harya karasa bedroom É—inta inda take zaune ta zabga uban tagumi saida ya zauna kusa da ita yana mirmishi ya ce

"Yadai wife naganki wani iri?" bakaramin jarumta tayi ba waja maida hawayan dake kokari xubo mata tace

"Banjin daÉ—i kaina na ciwo kaÉ—an kaÉ—an"

"Oh sorry wife kisha magani ki kwanta ki huta and karki sawa kanki damuwa please" batare daya sake duban inda take ba yamike ya fice daga room ɗin,yana fita ta kife a kan gadon ta fashe da kuka mai tsima zuciya...✍🏻
Chapter 24 · 0% Book details