← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 24

Sashe 18

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babban wajene mai kunshe da sashi sashi daban daban wanda ya danganci mata kama da wajan gyaran jiki shagon ɗinki daya tara manyan teloli da sukasan ɗinki yasansu, kayan costumeties, komai da mace ke bukata zaka same sa awajan gefe kuma ga babba wajan cin abinci da babban event, wajan na mami ne bata jima da buɗesa ba nike kula da ɓangaran gyaran jiki na mata wanda aka zuba ma'aikata sosai waɗanda sukasan aikinsu, sosai wajan ya karɓu a wajan mata musamman na yankin mu dama kewaye, sauri nake zan koma gida saboda yamma tayi lokacin tashina yayi, banzo da mota ta ba driver ne yakawoni dan haka na futo bakin titi ina jeran nape, wata mota harta giftani tayo baya ahankali glass ɗin motar yake sauka mamallakin motar ya leko kansa yana murmush ya ce

"Hajiya Su'ad yammata kwana dayawa ko nemana bakya yi"

Ni dariyama yabani ko akanme zan nemesa daga gani É—aya danai masa to in nemesa ince masa me, buÉ—emin kofa yayi yana faÉ—in

"Zomu tafi gidan dama na nufa Ma'ma ta aikeni wajan Maminki" haka kawai naji bazan iya yimasa musu ba na shuga, tare muka shuga gida da Nurein hakan na lura ba karamin daÉ—i yayiwa Mami ba, wasa wasa saiga shakuwa ta shuga tsakanina da Nurein harya fara bayyana min asirin zuciyarsa tun ina sharesa amma yawan nacinsa yasa na amshi soyayyar sa, kamar da wasa muka fara soyayay mai zafi harta kai ga muna batun aure.

__________Ashirye ya futo cikin da kakkiyar shaddarsa ruwan zuma kallo É—aya zakayiwa shaddar kasan bata kananun kuÉ—i bace wani kyalli take da walkiyya mai É—aukar idanu hannunsa É—aure yakeda agogo na zallar fata baki, yakafa hular tangaran ta zauna das akan nasa kafafunsa na saye cikin tsadaddan takalmi Haf shoe baki mai matukar kyau, tunda yafuto Jakadiya take binsa tana masa kirari dariya ta bashi sosai yanda take zuzuta sa saida yadara wanda hakan yasa Umma dake zaune a falon ta ce

"Lah yau wacce rana Turaki yana dariya gaskiyya jakadiya nabaki dubu hamsin" guÉ—a jakadiya tayi wacce tasa Turaki ya toshe kunnansa yana murmushi ya kalli Juhaina dake zaune gefan Umma tayi tagumi tareda zubawa Turakin idanu ba karamin kyau yayi mata ba yau nan take wani abu ya tokare kirjinta, Turaki zama yayi a kusa da'ita ganin yanda ta kafesa da idanu ya ce

"Autar Umma lafiya kike kuwa irin wannan kallon kamar baki sanni ba" taɓe baki tayi tareda mikewa ta shuge ɗakinta faɗawa saman gado tayi ta fashe da kuka, tarasa yaya zatayi da soyayyar Fu'ad ta kasa son ko wanne namiji shi kaɗai takewa wani irin so, wayarta ta ɗauka ta kira lambar Khady tana kuka take cewa

"Deeja na kasa jurewa soyayyar Yah Yarima zata kashe ni yaya zanyi ina zansa kaina naji daÉ—i, inata kokarin ganin na manta da soyayyarsa amma yau ganinsa ya tada min tsohon mikin son sa daya jima yana addabar zuciyata, nayita nuna masa ta hanyoyi daban daban acan baya amma yakasa ganewa"

"Juhaina ya kikeso ki maida mana hannun agogo baya, ya zakiyi da Abdallah kuma wanda kika amshi soyayyarsa dan Allah ki manta da wani Ameen sauran wata" Khady ta faɗa ranta ɓace

bayanta Turaki yabi ya tsaya bakin kofa yana jiyo maganganunta da khady shuga yayi ciki ya zauna gefan gado saida ya zauna É—in sannan ta gansa da sauri ta kashe wayan tana maida kanta saman fulo

"Tashi ki gayamin da gaske sona kike mai yasa kike sona?"

Sake ɓoye fuskarta tayi cikin fulo, ganin baza tayi magana ba yasa yamike tareda faɗin

"Shi kenan ni zanje kano na dawo anjima zanzo saiki faÉ—amin da gaske kike sona zaki aure ni?"

Fucewa yayi daga gidan har zuwa inda tawagar fadawa suke waÉ—anda zasuyi masa rakiya zuwa kano, zai biya ta masarauta yakai sakon mai martaba.

Sai bayan sallar La'asar Turaki ya shuga gidanmu dake tarauni mai gadi bai tsaya tambaya ba yabuÉ—e masu get tawagar motocin guda biyar suka shuga ciki, Turaki ya shuga main falo da sallama, gidan shuru kamar ba kowa saida yasake sallama sannan hanne mai aiki ta futo, murmushi tayi dan ta ganesa saidai jikinta yai sanyi sosai dan ganinsa saiya tuna mata da Uncle Fahad mutumin kirki,gaishesa tayi sannan ta wuce ciki ta sanar da su Ummi zuwansa tare suka futo da Mami ya zube kasan carfet yana gaidasu, tuni hawaye yafara wanke fuskar Mami Ummi dake ciccin magani ta ce

"Fu'ad sai yau Allah yakawo ka kai mana gaisuwar Fahad samada shekaru uku da rasuwarsa"

Arazane yaÉ—ago yana kallon Ummi muryarsa tana rawa ya ce "Ummi ban gane ba mai kike faÉ—a haka ina Fahad"

Mami da har tafara kuka ta ce "Fahad Allah yai masa rasuwa wata biyar da bikinsa yan fashi suka shugar masa gida suka kashe sa"

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, la'ilaha illallah muhammadan rasulilla"abinda Turaki yake iya faÉ—a kenan kafin yafashe da matsanancin kuka..

07039793439

[6/10, 7:37 AM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹

Story and writtin by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️

Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

25&26

Kuka yake sosai yajima yana kukan wanda kukan nasa ya kuma karyarwa da Mami zuciya ta wuce É—akinta itama tana kuka,ya jima yana kuka har sanda Yaya Jabeer yadawo yai masa rakiya makabartar da'aka binne Ankul, sosai yai masa addu'a kafin zuciyarsa ta karye yashuga basa hakuri kan rashin zuwansa, kamar wani mahaukaci haka yake zaro zance naban hakuri kamar wanda yake magana da yarayyan mutum, har saida Yaya Jabeer ya rukosa suka futo zuwa wajan mota har sannan kuka yake, bayan sun dawo gida Abinci Ummi ta kawowa Fu'ad ba yanda zaiyi haka yafara tsakurar abincin dan yafaÉ—awa Ummi shifa a koshe yake amma ta kafe saiya ci, zuba idanu yake yaga gilmawar Su'ad amma shuru ba alamarta, kunya tasa yakasa tambayar ina take, gabansa yabuga da karfi har saida yasa hannu ya dafe kirjinsa ya lumshe idanu yana addu'ar Allah yasa ba wani auran tayi ba, tabbas idan akace Su'ad ta auri wani bayan Uncle to kuwa ya cika mara sa'a a rayuwa, lumshe ido yayi tareda kwantar da kansa saman seater yanajin zuciyarsa naci gaba da bugawa kamar zata fasa kirjinsa ta fito saboda fargaba.

Tun daga bakin gate na gidanmu nasan yau munada babban bako ganin manya manya motoci acikin gidan, can gefe na faka motata Ameera ta kalleni da alamar tambaya ta ce

"Anty yau wa muka samu a gidan nan yacika da fadawa haka?"

Ban bata amsa ba sakamakon gabana da yai wata irin faɗuwa, na futo daga motar na ruko laidar hannuna dana siyo mana yoghurt Ameera tuni ta shuge ciki ni kuma saida na tsaya na kulle motar sannan na shuga zuwa ciki, lumshe idanuna nayi saboda wani daddaɗan kamshin turare dana shaka tabbas nasan kamshi nan amma na rasa a inda nasansa, cigaba nayi da tafiya har zuwa falo na uku inda komai nawa ya tsaya cak na wucin gadi sakamakon idonsa daya shuga cikin nawa ledar hannuna na saki sannan na wuce ɗakina da gudu ina sakin wani marayan kuka😥ganinsa danayi yatuna min da masoyina Fahad, sosai nake kuka har zuwa sanda Ummi ta shugo ɗakina

"Wai wannan kukan na menene najin daÉ—in ganin Fu'ad ne kona me?"

"Ummi Uncle! dana gansa sai naga kamar zan gansa tareda Uncle É—ina,ban saba ganinsa shi kaÉ—ai ba ko yaushe zan gansa yana tare da Uncle É—ina, Ummi da gaske Uncle yatafi kenan bazai kuma dawowa ba?"bazai sake rayuwa tare damu ba?"shi kenan mun rabu, bazan sake ganin saba bare naji ko muryarsa!"

"Su'ad zaki fara ko, to kije sitting room Fu'ad É—in yana can zai maki gaisuwa"

"Gaisuwa kuma Ummi shekara nawa da mutuwar Uncle maiya hana sa zuwa sai yau yaga damar zuwa"

"Idan kikaje sai kiji dalilinsa na kin zuwan" tana gama faÉ—ar haka ta fuce daga cikin É—akin, ban futa ba har saida Amira tazo tace "Ummi tace lalle ki futo wajan Uncle Fu'ad karta shugo ta sameki"

Da sauri na É—ago na kalli Ameera sai kuma na duro daga gadon na yafa mayafina na fuce daga É—akin.

Zaune na same sa ya saka kansa cikin kafafuwansa sallamar danai tasa ya É—ago yana kallona da jajayan idanunsa dasuka sha kuka, kujeran dake kallon wacce yake kai na zauna batare da na gaidashi ba dan Allah yagani batun yau ba nakejin haushin Fu'ad saboda nasan yanda suke da Fahad bai kamata ace har zuwa shekarun nan baizo gaisuwa ba.

"Ashe Fahad mutuwa yayi?"mai yasa ba'a gayamin ba?"ina can ina rayuwa ashe nayi rashin aboki amini É—an uwa"

"Ashe dama ka damu dashi ainazaci daka damu dashi daka nemesa a tsawon wannan lokacin"

"Bana kasar nan Princess ina london shekaru uku kenan, yanzu hakama saboda shi nabaro tarin ayyukan dake gabana nazo kawai danna gansa saboda ina kiran lambobinsa basa shugowa, gaya min ina yan fashin da suka kashemin aboki an yanke masu hukunci"

"E! an yanke masu, amma Zainaba har yanzu tana raye a gidan yari"

"Maiya kawo Zainaba cikin wannan zancan" komai daya faru na kwashe na gaya masa, idanunsa yai ja sosai alamar ɓacin rai ya ce "Matsalar kasan nan kenan shi kenan ita baza'a kasheta ba yanzu ba time damunje gidan yarin amma zan dawo nan da friday yazama dole akashe ta kamar yanda takashe min aboki" mikewa yayi yana kallona ya ce

"Zan koma sai...shuru yayi bai karasa ba sakamakon shugowar Ameera ta miko min wayata tace "Anty gashi Yaya Nurein ke kiranki" amsar wayar nayi ita kuma ta futa, kara wayan nayi a kunnena ina murmushi

"Ina kika shuga kika bar wayarki inata kira?"

"Nayi bako ne ina sitting room nabar wayan a É—akina"

"Bako Su'ad maiyazo yi wajanki" murmushi nayi ina kallon Fu'ad ta gefan ido ganin yanda ya kafeni da idanunsa yana aunamin wani kallo dana kasa gane na mene, hakan yasa na kara narkar da murya cikeda shakawaɓa na ce

"Kai Hubby maine na damuwa abokin Uncle ne fa yazomin gaisuwa kaima kasan babu wani a zuciyata inba kai...ban karasa ba naga Fu'ad a kaina yana huci ya fisge wayar yasa ta a aljihunsa yafuce daga É—akin a fusace, murmushi nayi inabin bayansa
Chapter 18 · 0% Book details