← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 24

Sashe 11

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ankul kai tsaye gidan Baban su Zainaba ya wuce, har É—akin baban yashuga yazauna yana gaida Baban dake masa wani kallo kamar zai kai masa duka.

Yace "Yanzu gobene ɗaurin auranka amma ka kasa zuwa ka gayamin sai yayarka ce take gayamin saboda bakuda zumunchi kun rainani ko saboda ni banida kuɗi, to bazan wakilceka ba kaje ka nemi wani bani ba" taɓe baki Fahad yayi tareda mikewa ya ajje masa ledar ɗinkin da Mami tace yakawowa Baban sannan yace

"Badamuwa Baba inma bakaje ba bazan rasa wanda zai wakilceni ba barema da kaina zan iya karɓarwa kaina aure" yana gama faɗar haka yafuce daga ɗakin, dai dai sannan Zainaba tashugo ɗakin a ruɗe ita bata taɓa jin zancan auran ba sai yanzu innarta ke sanar mata, zubewa tayi gaban baban tana rusar kuka

"Wallahi baba ka cuceni kaine kayi silar rabani da Fahad gashi yanzu inaji ina gani zaiyi wani auran ka kasa taɓuka komai😰kilama tazo ta haifi namiji shi kenan dukiyar da muka sakawa rai tabar tamu"

Dariya Baba yayi kamar wani sabon kamu ya zira hannunsa a aljihu yafuto da wani kullin magani yana nuna mata yace

"Kalli wanan É—azu na samosa a wajan wani malami badai gobene É—aurin auran ba to yanda aka kaimasa amarya haka za'a É—akkota kedai ki zubamin idanu kawai inada abinda nake kullawa"

Sosai Zainaba take murna dajin maganar da Baban yafaÉ—a hakan yasa ta koma É—akinta zuciyarta fes da farin ciki.

*RANA BATA KARYA*

Tun sassafe samarin gidanmu suketa shirin tafiya karaye dan shaida É—aurin auran Aminatu da Fahad, sosai Fahad yake cikin farin ciki marar musaltuwa kallo É—aya zakayi masa ka gano farin cikin dayake ciki, yana sanye cikin Fara kal É—in shadda yasha malum malum shugarsa shida Jabeer iri É—aya ce, ko'ina ka hangosa baki buÉ—e sai zuba murmushi yake duk sun shirya Fu'ad kawai suke jira yagama shiryawa su wuce, Tsab yagama shirinsa yafuto yana gyara zaman rawaninsa suka jero shida Fahad zuwa wajan da motocin dazasu shuga suke.

Ina tsaye baki window ina leka compound burina kawai na saka sa a idona nai masa kallo na karshe, irin kallon danasan har abada bazan sake masa irin kallon ba.

Da sarsarfa yake tahowa kasancewar su Fahad sunyi masa nisa dan harsun shuga mota shi ya tsaya amsa waya, binsa nake da kallo yanda yayi kyau cikin bakar shadda ya ɗora malum malum ta farar shadda wacce akayiwa aiki a gaban rigar da bakin zare, rawaninsa da takalminsa harma da agogon fatar dake hannunsa duk bakake ne, kamar wanda akace ya juyo muka haɗa ido cak ya tsaya yanamin murmishi tareda ɗagomin hannu yaci gaba da tafiya, murmushin da nakejin har abada bazan taɓa mantawa dashi ba kasancewarsa na karshe da yayimin ina kallo ya shuga motarsa wani yaja wanda nake zaton tare sukazo saboda kayan gidan sarauta dana hango a jikinsa da'alama dogari ne,komawa nayi na zauna gefan gado tareda jan tagumi, ina nan zaune har barci ya ɗaukeni ban sani ba saidai farkawa nayi naji gidan yakaraɗe da hayaniya na buɗa ido da sauri na sakko daga gado dai dai da shugowar Fadila tana murna da faɗin yarinya bani tukwaici nagaya maki wata magana...✍️

07039793439
[6/4, 7:48 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹

Story and writtin by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️

Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

*Na gaisheku Æ´an group É—in KUKAN ZUCIYA comment É—inku na sani nishaÉ—i wannan page É—in gaba É—aya nakune kuji daÉ—inku*

"Wanne abu zaki gaya min da har saina baki tukwici nasan dai cewa zaki an É—aura min aure da Fahad koba haka zaki faÉ—a ba" ban jira Fadila ta ce komai ba na faÉ—a bathroom na kunna famfo ruwa na zuba na fashe da matsanancin kuka "Shikenan shikenan yanzu na zama mallakin Uncle haba kaddara mai yasa zaki mana haka maiyasa zaki rabani da farin cikina wayyo Allah wayyo zuciyata wayyo Ameen" ta karasa faÉ—a da karfi tareda nemar waje na zauna na fashe da matsanancin kukan takaicin rashin Prince Ameen,
Mami gaba ɗaya hankalinta na gida hakan yasa ana gama ɗaurin aure itada Momy matar wan Ummi suka juyo gida, Ba wani shagalin biki akai ba sabida yanda bikin yazo ba shiri ga kuma rasuwar Daddy dako wata biyu bai yi ba, da mangariba Mami da sauran tsirarun ƴan uwa suka mika ni gidan Fahad, gidan da nasa a raina zan tabbata ina Kukan Zuciya a cikinsa, basu wani jima ba aka tafi aka barni daga ni sai halina tunda muka shiga gidan nake kuka ta cikin mayafin daya lulluɓe min duka jikina basu jima da tafiya ba uncle ya shigo, sallamar dayai tayi dai dai da bugawar zuciyata wanda yai sanadin dana kuma fashewa da kuka ya zauna kusa dani ya buɗe mayafin daya lulluɓe ni yana murmushi saidai annurin fuskarsa lokaci ɗaya ya kau, ya saki mayafin jiki sanyaye, bai cemin uffan ba haka nima bance masa, nadai lura jikin Uncle yai matukat sanyi ganin ya fita yasa na kwanta kan gadon ina kuka sosai, Fahad mai saukin hali kullum kalaman lallashi yake bina dashi musamman ganin naki sakin jiki da shi, kyautatawar Uncle a gareni yasa nabar kukan fili na rashin masoyi na koma kukan zuciya, Uncle na matukar kokari sosai ganin ya kwantar min da hankali komai na gida shi yake yi tun bana sakin jiki da shi harna ware na saki jiki muka koma kamar da sanda muna gida, har sannan mikin son Ameen Fu'ad na nan ɓoye cikin zuciyata nakan tina dashi a kullum nakan kuma so nasan a wanne hali yake yanzu ina yawan ɗaukar wayar Uncle a ɓoye nayita kallon hoton Fu'ad ina kukan zuciya wani bin sai nayi kamar zan kira lambar sa sai kuma na tina haramcin hakan na ajje wayar na ɓuya a ɗaki nai kuka sosai tareda addu'a Allah ya cire min sonsa a zuciyata, sanda hutun da aka bawa Uncle a wajan aiki ya kare ya koma aiki randa yatafi sai naji gidan shuru kewar gida ta kamani gashi muna hutun school,

Zaune suke gaban malam na gangare wanda yasha uban rawani da malum malum kamar malamin gaske, Zainaba tana kuka take cewa "Dan Allah malam ka taimakamin inason mijina, gashi ya sakeni har saki uku, ya auri wata, sonake yasaketa yazo yamaidani acusa masa tsanarta sosai yaji nan duniya ba warda ya tsana sama da ita ya korata gidansu da takardar saki uku" malam ya zana wata kasa dake gabansa ya girgiza kai ya ce

"Auran nan babu rabuwa aciki duk wanda yace zaija to komai zai iya faruwa dashi sannan kema babu sauran zama ke dashi sai dai kizaɓi abinda kike so bayan wannan"

"Malam ka taimakeni!"

Ungo wannan yamika mata wani kullin magani yace "Ki zuba sa a inda kika tabbatar zai taka koya tsallaka, inhar kikayi haka to ba abunda zai iya yiwa matar tasa zai zama fanko awajanta ita kuma zata kasa jurewa harta kai ga ta nemi saki, bayan yasaketan kizo ki gayamin zansan yanda za'ayi sai'a maida auran naku" cikeda murna tabasa kuÉ—in daya butaka ita kuma ta dawo gida ta tisa baba agaba akan ya kira Fahad yace yana son ganinsa yanzu, lokacin Uncle na shirin barin office dan haka ya shaida ma Baba da gashi nan zuwa yanzu insha Allah, Da gudu Zainaba tashugo cikin gidan tun É—azu tana tsaye kofar gida tana jiran zuwan Fahad tun daga nesa data hango motarsa ta dawo gidan ta kunce kullin maganin daga gefan zaninta ta zuba sa a kofar É—akin Baba, mahaifiyarta data futo daga É—akinta tabita da kallon tuhuma "Zainaba mai kikeyi haka a kofar É—aki ba sallamar Fahad nakeji ba, waima maine wannan a hannunku" Baba daya leko daga É—akinsa yace.

"Kefa mairo kin fiya saka ido ina ruwanki da maine a hannunta ke Zainabu cewa Fahad yashugo ina ciki"

Fahad yashugo da sallama yana gaida Innah mairo fuskarta cikeda fara'a take amsa masa gaisuwar, yana shuga É—akin Baba Zainaba tayi wani tsalle tana murna harda taka rawa, a kasa ya zauna yana gaida Baba, ta inda yake shuga bata nan yake futa ba faÉ—a yake sosai

"Yanzu saboda rashin zumunchi irin naku ace kayan abinci ma bazaku iya saimin ba saina roka kuna kallon halin danake ciki aikima ya gagareni amma bazaku rinka tausayamin ba wannan ba halin ubanku bane, ubanku mutumin kirki amma kaida yar uwarka mahaifiyarku tashuga tsakani na da ku"

Fahad dariya ma abin yabasa daya tuna ko karshan wata saida Mami tagaya masa ta turawa Baba kayan abinci, shine yanzu zai zo yana masa mita "Ayi hakuri baba ban zaci wanda Mami takawo harya kare ba yanzu bari naje zan aiko maka dasu"

"Basai ka aiko ba kabani kuÉ—in kawai nasiya da kaina" mikewa Fahad yayi yana murmushi yafuta, mota yaje ya É—ebo kuÉ—i ya kawo wa Baban sannan yafuta, har sannan Zainaba tana zaune kofar É—akin daÉ—i ya kume ta ganin har sau biyu yana taka maganin.

Yau sosai nakejin nishaɗi hakan yasa da wuri na kammala abinda zanyi nai wanka ina zaune gaban madubi na gama tsantsara kwanliya wacce najima banyi irinta ba tun kafin rasuwar Daddyn mu, doguwar rigar material nasa wacce takama jikina tamin kyau sosai na feshe jikina da turere mai kamshi, na gyara gashina dayasha kalolin mayuka sai kamshi yake da kyalli, ban ɗaura ɗan kwalinba na ajjesa saman kujera ina kallon agogo karfe huɗu saura kwata, mamaki nake maiya hana Ankul dawowa bayan yacemin karfe biyu zai dawo zama nayi na ɗakko wayata na kunna data nahau online hira muke da Yaya Fatima kiran Fahad yashugo wayan nawa da sauri na ɗaga cikeda shagwaɓa

Nace "Shine kayi zamanka har yanzu baka dawo ba bayan kace karfe biyu zaka dawo" ina jiyo sanda yai murmushi mai sauti

"Kina son nadawo ne, inna dawo maizan samu mai kika tanadarmin?"

"Na tanadar maka da komai,kuma ni tsoro nakeji nafison innayi motsi na ganka kusa dani hakan yana faranta min rai"

"Da gaske to gani nan a hanya" kashe wayan yayi saida yayi sallar La'asar a masallaci dake É—an nesa da gidansa kaÉ—an sanna ya karasa gida.
Chapter 11 · 0% Book details