← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 24

Sashe 15

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuru tayi tareda tagumi tana kallona tama kasa cewa komai, jikinta yayi sanyi har mukazo tafiya sanda Ankul yazo bayan sallar mangariba, batayi masa zancanba muka koma gida.

Ranar monday Ameera tafara zuwa school tun bakwai da rabi Ankul yake kaita bata dawowa sai shida na yamma nake zuwa É—akkota, gefe nima naci gaba da karatuna.

Mami bayan tafiyarsu Su'ad ganyan magarya tasamu guda bakwai ta dakasa ta zuba a ruwa ta karanta suratul bakara daga aya ta farko zuwa ta biyar, sai ayatul kursiyyu da wattaba'u da amanar rasulu da kuliya aiyuhalkafirun kulhuwallahu falaki da nasi...ayoyi da dama tayi amfani dasu ta tofa, ta ajje ruwan washe gari da dare da kanta taje har gida ta kaiwa Su'ad tace ta tabbatar Uncle yayi wanka dashi a tsabtataccan waje lokacin Uncle yana nan kallonsu kawai yake baice komaiba, sai bayan tafiyar Mami

Yace "Waton duk rokonki danai karki faÉ—awa kowa lalurata saida kika faÉ—awa maminki ko?"yayi kyau nasan zaman da zanyi dake" Uncle yafaÉ—i haka cikin fushi

Dariyama yaban hakan yasa nayi dariya kafin nace "Ba dole na faÉ—a mata ba kafara batun rabuwa yaya kake so nayi da rayuwata in bana tare dakai koba haka bama Meera tana bukatar kani kaga dole mu nemi mafita"

Rike baki Uncle yayi cikeda mamakin maganarta yace "A'a kidaice Antyn Meera tana bukatar mijinta, mai wannan yake nufi" yafaɗi haka yana buɗe jarkar da Mami ta kawo ruwan, taɓe baki yayi kana

"Ya ce yanzufa sai tace sammu akaimin shine taje ta haÉ—o wannan" dariya nayi tareda É—aukar jarkar nace

"Nidai taho nayi maka wankan nan a alamu muka gani wanda ya tabbatar mana da zarginmu" baice komai ba yabiyoni ɗin, cikin ikon Allah kwana uku yana wanka yadawo normal ranar yini yayi yana murna sai faman kirana yake daga office naga shirya shi wallahi yau ya warke dayasan hakane aida tuni yagayawa mami da kansa amma kyautata dabance bari yadawo, bai shugo gida ba sai Takwas na dare yasame mu zaune a falo Meera tana kwance kaina sai faman juyi take tunda ta dawo daga school takemin korafin cikinta yana ciwo faɗa nai mata akan rashin cin abinci nabata abincin taci danna zaci yunwa takeji amma maimakon ciwon yayi baya saima gaba yake, ko zama baiyi ba ya koma ya haɗo mata magani harda allura yai mata muna nan zaune a falo har ɗayan dare tana fama, sai wajan biyu saura tacemin yadaina zataje ta kwanta, wayata na bata na kaita ɗakina nace ta kwanta intaji ciwon takira lambar Ankul sai nazo, na wuce ɗakin nasa harya kashe light ya kwanta na kwanta kusa dashi yajani jikinsa yana faɗin zoki kwanta sarkin tsoro ba abinda zan maki nima na gaji yarki ta rusa mana wannan daran namu, har barci yafara fuzgata naji karar faɗuwar abu a falo hakan yasa muka mike tare nida Uncle da sauri nai hanyar futa falon Uncle yaruko hannuna yanamin wani kallo wanda bantaɓa ganin irinsa daga garesa ba, ya mike ya haɗani daa jikinsa yana sauke numfashi "Ina sonki Besty" yafaɗa da murya a shaƙe, karajin motsi danai yasa na fusge hannuna tareda faɗin

"Uncle sakeni kilafa Meera ce jikin ya motsa ta futo kar zafin ciwo yasa ta futa waje a daran nan" sake haÉ—ani yayi da jikinsa yana sakin ajjiyar zuciya kallon idanunsa nayi yanda suka canza launi yasa nai murmushi

Na ce "To tawo muje mu dubata saimu dawo tare" tare muka futa dai dai an kunna hasken falon abinda na gani yasani kwala ihu haÉ—eda salati na kankame Uncle jikina yana rawa manyan kartini majiya karfi kallo É—aya zakayi masu ka gane su waye, Uncle sakina yayi yana tunkararsu bako alamar tsoro a garesa

"Lafiya zaku shugo mana gida da daran nan" wata dariya wani acikinsu ya bushe da'ita yana girgiza yabawa Uncle amsa da

"Wajanka aka turomu mu É—auki ranka"

Murmushi mai ciwo Uncle yayi ya ce "Raina kuma kamar kaine mala'ikan mutuwa" da sauri na kankame Uncle ina kuka nake faÉ—in

"Dan Allah karku kashe sa zamu baku duk abinda kuke bukata amma karku taɓamin mijina" zama wanda na lura shine ogan nasu yayi kan kujera yana kureni da kallo yace

"Gaki kuwa kyakkyawa zaki iya fansar mijinki da wannan kyan naki ki bani minti goma kacal mu shuga daga cikin na kawar da kishina shi kenan na barki da mijinki" Uncle wani irin ihu yayi tareda kallon wanda yai maganar ya janyeni daga jikinsa ya doshi wanda ke maganar yana tattare hannun jallabiyar dake jikinsa a yafara kokarin kai masa naushi, É—aya daga cikinsu ganin ya doshi ogonsu yasa ya shammacesa ta gefansa ya caka masa wuka a gefan cikinsa

"Ya Allah" Uncle yafaɗa tareda dafe wajan daya yankesa da gudu nai kan Ankul ina kwala masa kira ganin yanda jini yafara zuba, kafin nakai ga Ankul ya zube a kasa saboda jinin dake zuba daga jikinsa, ɗora kaina nayi saman cikin Uncle nasoma kuka yanda yake futarda numfashi yasa nakai hannuna zan cire masa wukar da har sannan take jikinsa aka banko kofar shugowa ana faɗin karki taɓa Su'ad da sauri na ɗago ina kallon mai magana...✍️

07039793439

[6/8, 11:44 AM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹

Story and writtin by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️

Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

21&22

Da sauri na ɗago kaina na kalli wanda yashugo Cp Mukhtar ne bayansa ummi da mami ne sai Yaya Jabeer da tawagar yan sanda kamar masu shirin yaki, da sauri Jabeer ya'isa inda Uncle ke kwance ya tallafo kansa, Cp ya saka wani kyalle ya zare wukar jikin Uncle sannan C P yabada umarnin a tafi dashi asibiti bisa jagorancin yaransa, ina kallo su Yaya Jabeer suka tafida Uncle hospital Mami kuwa ta zauna dafa'an tana kuka ganin halin da ɗan uwanta ke ciki da wuyama ya tashi😰 Kwamishina ya tusa keyar yan fashin dasuka shugo mana gida, amaimakon nagansu su biyar kamar yanda suka shugo saina lura babu ogansu wanda yazauna kan kujera, C p yace mu rofe gidan su ajjemu a asibiti sai sannan nayi magana

Nace "Yaya Mukhtar akwai fa sauran ɗaya su biyar suka shugo,nan da nan yabaza yaransa suka cigaba da bincike gidan sai sannan na tuna da Ameera na shuga ɗakinta amma naga wayam bako alamarta hannu na ɗora aka🙆‍♀️ na fashe da kuka ina faɗin "Wayyo Allah na shiga uku banga Ameera ba," nafaɗa ina rushewa da matsanancin kuka, duk yanda aka bincika gidan ba Ameera ba ogan yan fashin, C p yabar sauran yaransa suna tsoron gidan yayinda mu kuma muka wuce Hospital inda aka kai Uncle muna shuga dai dai an futo dashi daga ɗakin tiyata dan yankan yataɓa masa hanjinsa, bin gadon da'aka turoshi nayi da kallo ganin yanda fuskarshi tai haske yasa na fashe da kuka tareda rungume Mami, Ummi tace

"Ba kuka zakuyi ba mugodewa Allah dayasa aka kawosa asibiti da wuri da tuni mun rasashi amma yanzu da izinin ubangiji zai tashi nan da yan awanni" shuɗewar awanni Uncle bai farkaba nayi kuka na harna gaji Mami ta koma gidanmu, gefe guda kuma yan sanda na gudanar da bincike kan wanda yaturosu da kuma ɓacewar Ameera.

Wajan sha biyun ranar juma'a Uncle ya farka yana wata irin karkarwa da sauri na futa na kira Ummi kasancewar asibitun datake aiki ne,tare suka shugo da wani likitan, Uncle ya ruko hannuna cikin ciwo yake faÉ—in

"Su'ad kiyafemin mutuwa zanyi ina Ameera ina Mami, Ummi ga amanar Ameera nan na damka a hannunku kuriketa kar'a bawa dangin mamanta nabar maku ita duniya da lahira,Su'ad kiyi hakuri yau mutuwa zata rabamu fatana ko bayan raina karki manta dani kirinkami addu'a,Allah yabaki wani mijin wanda zai soki fiyeda son danake maki,naso ace nayi tsawon rai ta yanda zankula dake nabaki farin cikin rayuwa amma mutuwa zata rabamu kigayawa Mami tayi hakuri daman mu kaɗai muka rage yau gani nima zan tafi na barta😰"

Wata shakuwa da yayi can kuma sai aman jini, gaba ɗaya likitocin sukai kansa kowa da abinda yake masa har sannan hannunsa yana cikin nawa ni kuma na kifa kaina kan gadon dayake kai inata kuka duk da maganganunsa basuyi tasiri a zuciyata ba danni gani nake kawai zafin ciwo yasa yake waɗan nan surutun, salatin dayayi haɗe da kalmar shahada yasa na ɗago ina kallonsa idanunsa na kallon sama naji hannunsa dake cikin nawa yasaki, Ummi naga taja baya tana salati ɗayan likitan yaja farin kyallan dake lulluɓe jikin Uncle ya rufe masa fuska, ban fuskanci mai suke nufi ba saida naji ɗayan likitan ya kalli Ummi

Yace "Sai hakuri Dr kullu nafsin za'ikatul mot"

Ai bansan sanda na mike ba na rungumo Ankul da karfi nace "No!!! wallahi karyane! nace karyane ba Ankul ɗina bane yamutu kaine dai bakasan aikinka ba, na buɗe Ankul ina kallon fuskarsa "Kanaji ana maka sharrin ka rasu Fahad katashi ka shaida masu baka mutuba katashi nace Uncle Dan Allah besty ka tashi ka gaya masu kana raye" rukoni da'akayi yasa najuya ina kallon wanda ya rikeni Yaya Jabeer ne idanunsa sun kaɗa sunyi jawur ba kuka yake ba amma tabbas halin dayake ciki kwara ace kukan yake zuciyarsa zatafi samun sauki😰rungumesa nayi tareda fashewa da kuka

Nace "Dagaske wai da gaskene Uncle É—ina ya rasu, Yaya Jabeer ka karyata dan Allah ka karyata min Innalillahi wa'inna ilaiheer raji'un" Ummi ta ruko hannuna muka futa zuwa gida, su Yaya Jabeer suka tsaya zasu tawo da gawar Ankul.

Har muka shuga mota ina kallon É—akinda gawar Uncle ke kwance inajin wani irin kewarsa datake shugata, shikenan kuma na rabu da Uncle bazan sake ganinsa ba? na rasa Ankul kamar yanda na rasa Daddy na gaba É—ayama kukan yaÉ—auke na koma kamar wata mutum mutumi har sanda aka gama haÉ—a gawar Uncle aka kirani wai muyi sallama sosai nasawa zuciyata juriya nai masa addu'a da fatan Allah yasa aljannace makomarsa.
Chapter 15 · 0% Book details