← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 24

Sashe 21

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"One Boy yaya jikin, sai kuma ga Sweet heart tazo cuta ta warke"

Murmushi kurum yayi sai sannan Umma taga Baraka dake zaune can gaban gadon kan kujera,

"Ran uwargida ya daɗe yaushe kika zo, na baroki a gida kin rigani zuwa,kodan na tsaya duba marassa lafiya a genarel hospital" Baraka murmushi kurum tayi taci gaba da danna wayarta, Umma katuwar dadduma ta shimfiɗa ta zauna nima ta umarceni dana zauna ta zubomin abinci, kasa cin abincin nayi sai danna wayata da nake, shugowar Dr yasa na mike zan futa, dan tun ɗazu nake zuba idanu naga ta inda Yaya Shareef zai ɓullo amma shuru gashi har anfara kiran sallar la'asar, futa nayi ina lalubansa amma babu shi babu alamunsa ko matarsa ma bata inda ya ajjeta, cikeda damuwa nake danna lambarsa harta shuga bugun farko yaɗaga yanamin dariya.

"Yah Shareef ina kaje ne?naga baka compound na hospital É—in"

"Waini kike tambayya toni kin ganni nan a abuja nafi minti talatin ma da sauka"

Shar shar idanuna suka zubo da kwalla "Yaya zakamin haka ka barni a garin mutane katafi ka barni yanzu yaya zanyi na koma gida?"

"Kinga kwantar da hankalinki motata ma tana nan garin jirgi nabi saboda kiran gaggawa na samu daga office, Umman mai martaba ita tace na barki gobe su Mami zasuzo duba Fu'ad saiku wuce tare"

"Kwana kuma yaya anan garin kai haba bazan iya ba"

"Bazaki iya kwanan gidan surukai ba" naji an faÉ—a daga bayana katse wayar nayi na juyo ina kallon Umma dake magana "Kiyi hakuri ni nayiwa Maminki waya ta turo mana ke Fu'ad yana cikin kunci da damuwa kamar yanda abokinsa Uthman yagayan kece damuwar Fu'ad, kiyi hakuri inma wani laifi yayi maki ku sasanta, yana sonki sosai Su'ad inya rasaki a wannan karon bazai iya jurewa ba, zuciyarsa tayi rauni sosai a kaunarki ki tausaya masa"

Sunne kaina nayi kasa ina wasada zoben hannuna ganin bance komai ba yasa taja hannuna muka koma É—akin, bakin mata da miji muka tarar jin danai Umma ta ce

"Lale da Abiee munyi fushi sai yau kazo duba one boy É—in nawa" hakan data faÉ—a yasa na gane mahaifin Fu'ad ne wannan

"Ayi hakuri abubuwane sukayi yawa musamman wannan guguwar zaɓan data tunkaro mu bamuda lokacin kanmu kullum muna yawon kamfen, kuma nasan zuwan nawa ma baida amfani tunda gaku keda mai martaba,sannan ga Antynsa itama tana kusa tunda taki zaman abuja"

Dariya Umma tayi batace komai ba, kallo É—aya Anty Jameela tamin ta É—auke kanta taci gaba da danna wayarta, nima shareta nayi nagaida Abiee kawai wanda ya amsa fuska sake yana tambayar Umma

"Asiyya ina kika samu ya"

"Au ashefa baka santa ba ita ta zaunar da Fu'ad anan" Umma tana faɗar haka yadafe baki🤭cikeda mamaki ya ce "Au anyi abun kunya nakasa gane Su'ad ɗin Fu'ad, haba shiyasa naga bakin ɗan naki yaki rufuwa" wani kallo da Anty Jameela tayi masa yasa yai shuru badan yagama magana ba, ɗakin yai shuru har sukai shirin tafiya, Baraka tabi bayan su tanawa Anty Jameela magana

"Anty wai wannan yarinyar wacece É—in su Abban Su'ad naga sai wani shisshige mata yake gani a waje amma bazai ce inmasa wani abu ba saidai ita"

Anty Jameela saida tayi dariya kana tace "Hmmm wannan itace Su'ad budurwar Fu'ad wacce yaiwa mahaukacin so mijinta ya rasu shine yanzu yake so ta auresa, sorrynki yarinya idan har kikayi saken da wannan yarinyar ta shugo maki gida, kiga abata nan ma daya haifi ya sunanta yasa saboda ya raina maki hankali, lokaci yayi da zakizo mu haÉ—e kai muyaki yarinyar nan dan inkika sake ta shugo kin kaÉ—e ke matar shige (Anty mai zafafa) ita kuma matar so kinga babu haÉ—i, dole kiyita ganin takaici"

Hannu Baraka ta ɗora aka🙆‍♀️"Wayyo na shuga uku daman Su'ad sunan budurwarsa yasa nifa na zaci na mahaifiyar sa ne, wayyo Allah na Fu'ad yakashe ni"😰gaba Anty Jameela tayi tabar Baraka anan tsaye tana goge hawaye.

Nifa duk zaman garin ya'ishe ni, musamman yanda Fu'ad yake wani kallona duk na kasa sakewa hakan da Umma ta lura yasa gabda mangariba tace natashi mutafi gida, Fu'ad ya marairaice fuska

"Umma tun yanzu zaku tafi yau bazaki bari ayi sallar insha ba"

"E tafiya zanyi bakaga bakuwa ba, gida zamuje tai wanka ta kwanta ta huta gajiyar hanya" bayan Umma nabi data futa naji ya ce

"Su'ad jimana" najiyo na kallesa "Wayan waye a hannunki"

"Ta Mami ce" nabasa amsa ina kokarin futa,baicemin komai ba harna fuce, a wani babban super market muka tsaya Umma ta zaɓamin dogayan riguna masu kyau nayi amfani dasu tunda banzo da shirin kwana ba sai kayan ciki data sakani na zaɓi size ɗina, koda mukaje gida ɗakinta ta kaini ta haɗamin ruwan wanka nayi na shirya cikin daya daga cikin rigunan data saimin, nai sallar mangariba ina nan zaune ina cin abinci, aka shugo da sallama.

É—ago kaina nai na kalli wacce tai sallamar itama kallona tayi ta É—auke kai batare da tacemin komai ba, Umma ce ta shugo hannunta rikeda plate da aka shakosa da kayan fruit ta ajje agabana tana kallon yarinyar dake zaune gefan gado,

"Juhaina bakiga bakuwa ba?Su'ad ce fa budurwa Turaki"

Dan taɓe baki tayi tana kauda kai gefe ta ce "Naganta sannu fa" tana gama faɗar haka tai fucewarta daga ɗakin, murmushi Umma tayi tana rakata da kallo harta fuce.

Sosai Umma take bani kulawa kamar yarta haka ta maidani, yanda kowa yasanni agidan abin har mamaki yake bani, kwana na biyu a garin aka sallami Turaki daga asibiti saboda yaji sauki sosai, wata irin kula yake bani duk da ni zaman gidan dik ya isheni hakan yasa na kira Mami ina mata korafi

"Nifa Mami wallahi tahowa zanyi gida, kawai daga zuwana sun wani rikeni ba dangin iya bana baba inata zama masu a gida"

"A'a karki taho ki bari jibi zanzo duba Fu'ad É—in saimu taho tare" nidai badan son raina nake zaman gidan nan ba wallahi.

Da yamma ina zaune nayi wanka nasha kwalliya cikin doguwar rigar Atamfa Umma ta bani washe garin randa naje kusan kala shida da'alama bayarwa tayi aka É—inkomin su, wayar Mami ce a hannuna ina chat, kiran Nurein daya shugo yasani kwantawa saman doguwar kujera tareda kara wayar a kunnena, ko sallamar danayi bai amsaba ya ce

"Wai zaman me kike a garin mutane yau kusan kwananki huÉ—u kullum nazo bakya nan an shaida min kina bare, garinsu Fu'ad ne fa mai kikeyi?"

"Nima zaman yana damuna Hubby nafison nadawo gida amma sunki bani dama jinake kamar na gudu"

"Kinga karki rainamin hankali nafasan maike tsakaninki da gayan nan inma ba iskanci ba maiya kaiki zama a garinsu"

"Nurein mai kake nufi?"

"Kinga dan Allah kitaimakeni ki dawo nifa tsoron gayan nan nake karya kwacemin ke, Su'ad ina matuwar sonki banson abinda zai rabani dake, kinga Abbana harya fara maganar turowa gidanku wata yar matsala aka samu da tuni sunzo ma please dan Allah kidawo"

Ajjiyar zuciya nasauke kana nace "Ok naji Hubby zan dawo jibi"

Wayar naji an zare daga kunnena a tsorace na mike dan nidai nasan ni kaɗaice a falon, Fu'ad na gani tsaye akaina yana kallona yana juya wayar a hannunsa, kallo ɗaya nayi masa na kauda kaina daga kallon nasa saboda masifar dana hango cikin kwayar idanunsa, cije leɓe yayi ya zauna kan kuja ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana girgiza kafar saman, na lura yana son yin magana amma tsabar fushi yasa yakasa cewa komai, nima zama nayi a kujerar dana tashi kaina a kasa ina jiran inji abinda zaice, karar wayar tasa na ɗago ina kallonsa, yanda yake huci yaso tsorata ni kallona yayi ido cikin ido.

"Narasa maine maki kika daina sona Princess,na lura so kike ki kasheni da raina, kinsan irin son danake maki kuwa? Kinsan tsawon shekarun nan dai dai da dakika ɗaya sonki bai taɓa raguwa a zuciyata ba, kinssan mainene so kuwa Su'ad kinaso ki kaina lahira kwana na bai kare ba? sa'arki ɗaya wayar nan vataki bace wallahi da yau saina kwankwatsata naga ta inda wannan mayan zai sake kiranki, akaro na biyu karki yadda ayi na uku dan wallahi rai zaiyi matukar ɓaci, akanki zan iya yin komai, wallahi kinji na rantse idan na kara jin kina wayada gayan nan ko kika sake tsautsayi yasa na ganshi to wallahi saina ɗaure sa ko ɗan gidan waye a kasar nan saidai nima a ɗaurenin" yana gama faɗar haka yasa wayar a aljihu yasoma tafiya.

"Kabani wayata to, waccan ma ka kwacemin wannan ai ta Mami ce kuma ni gidanmu zan tafi" ganin bai kulani yasa na mike nabi bayansa.

"Nifa kabani wayata haka kurum zaka rabani da shi naga tare ka ganmu ko aurata kayi dazaka rinka kafamin sharuÉ—a" afusace ya juyo kamar zai dake ni yake faÉ—in

"Haka kikace ko? wayar yamiko saida yabuɗe kofa zai futa ya juyo yanamin wani kallo dana kasa fassara sa ya ce "Ki shirya zansa a maidaki gida, kuci gaba da soyayya da Nurein Allah yabarku tare...✍🏻

07039793439

🌹 *KUKAN ZUCIYA* 🌹

Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️

Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

29&30

Gaba É—aya kuma sai jikina yayi sanyi na koma na zauna, ashe Umma tana kallonmu ta saman mai martaba.

"Kibi Turaki a hankali kwanan nan nakasa gane kansa gaba É—aya ya canza nema yake ya birkice mana, ki shirya nasan yanzu zakiga ya turo ki futo amma banso tafiyarki yau ba, ba komai ai kin kusa zama tamu gaba É—aya"
Chapter 21 · 0% Book details