← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 24

Sashe 4

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "Naga abincinki baki ciba, Ummi tace yau gaba ɗaya bata ganki ba ina kikaje" turo baki gaba tayi dan in tana gaban Uncle ɗin nata gaba ɗaya narkewa take ta koma karamar yarinya, shi kuma yayita biye mata tana zuba masa shagwaɓa da shiririta "Nifa Uncle yau ba kalar abinda nakeso ba akayi, kuma ai Ummi tasan bansan kunun gyaɗa da doya shine tayi ni bazanci komaiba yau" tafaɗi haka tana gyara kwanciyarta, "Wacce irin maganace haka Besty amma dai kinsan banson ki zauna da yunwa ko yanzu fa har karfe biyu bakici komai ba, kinga tashi gayamin mai kike son ci saina saka a siyo maki" da sauri na mike na zauna saman gadon ina murmushi kafin nace "Nifa Uncle kawai ka kaini nayo take away chips nakeson ci da shawarma sai meat pie da Peach mai sanyi" dafe kansa yayi yana kallonta kafin yace "Oh Su'ad nagaji dayawa yau mutum biyu naiwa cs yanzu haka gudowa nayi nazo na huta kuma ki sani na sake futa, bari kawai nabawa Seteven yasiyo maki" komawa tayi ta kwanta tana ɓata rai ahankali take mita "Shikenan kaje ka kwanta ɗin aidaman nasan basona kuke ba yan gidan nan ace na wuni banci abinci ba amma ba wanda ya damu dani, dan anga Mami da Daddy basa nan ne aida ko shi nasan zai kaini naci abinda raina keso" Fahad zama yayi gefan gadon yana cewa "Kinga bafa wani abun damuwa bane wane yace maki bamu damu dake ba, yanzu dai bari naje nayi wanka nazo na kaiki kici abinda ranki keso, kema ai kinsan bama haka dake farin cikinki ai shine nawa koba hakaba yar Uncle" yafaɗi haka yana kashe mata ido ɗaya, gabanta ne yai wata irin faɗuwa saboda ganin kallon dayake mata wanda baida maraba da irin wanda Fu'ad ke mata ako da yaushe, Bayan yayi wanka yazo suka fita tare basu wani jimaba suka dawo gida

Su'ad tare suka shugo gida da Uncle Fahad, shike rike da ledojin da tayo siyayya, tsakiyar falon ta baje taci wancan taci Ummi da yaya shareef na kallonta ba wanda ya kulata harta gama ta wuce É—akinta.

AMEEN sosai yakejin daÉ—in zaman Kano tun washe garin randa yazo yacewa Yunus ya koma gida inzai komo zai biyo jirgi ko fita zaiyi shi kaÉ—ai ke fita a motar FAHAD sau biyu yana kaiwa HIDAYA ziyara suyi hira sosai yai wasa da yaranta sannan yadawo gidansu Fahad kusan baida matsala da kowa a zamansa na gidan, sosai Ameen keson rayuwa irin haka ta ba ruwan kowa da kowa ba kamar suba a masarauta ko ina zaka kana tareda rakiyar fadawa shi yasa ya kwashe sati biyu a garin kano kafin ya saka ranar tafiya,
karfe goma na safiyar Ranar Lahdi Fu'ad yagama shirinsa na komawa garinsu, har sannan baiga futowar Su'ad ba, har sun gama sallama da Ummi sun futa compound yanata waige waigen inda zaiga Su'ad ta fito harya shiga mota yahangi futowarta lokacin Fahad na kokarin tasar mota, da sarsarfa ta karaso wajan tareda buÉ—e back seat ta zauna, Fu'ad ya sauke wata nauyayyar ajjiyar zuciya wacce har Fahad ya kallesa batare dayace komai ba ya juya yana kallon Su'ad
"Daman kinada lacture amma baki shirya da wuri ba sai yanzu, bayan nagaya maki karfe goma zankai Fu'ad airport" cuno baki tayi gaba kana ta ce "Aini dai rakaka zanyi banason zaman gidan nan gaba É—aya su Ummi basa son gani na dan anga Mami bata nan kowa baya kulani kaima duka ka canza min yanzu ba ruwanka dani ko kaÉ—an baku rike amanar da Mami ta baku ba Allah ma yasa yau Mami da Daddy zasu dawo" Fahad tasar motar yayi batare dayace komai ba ya girgiza kai kawai yana yaba rigima irinta Su'ad yafara tafiya gate man ya buÉ—e mana kofa muka futa, saida Fahad ya fara tafiya saman kwalta sannan na futo da wayana na kunna data sakon Fu'ad shiya fara shugowa na buÉ—e da sauri ganin yana online

_"Princess kinyi kyau! bakiji yanda naji zuciyata ba dana ganni cikin mota zan bar gari batare dana ganki ba"_

_Tayaya zan bari farin cikina yatafi batare dana sake ganin saba zanyi kewarka_ É—agowa yayi yana kallona ta madubin motar yakashe min ido tareda murmushi mai narkar da zuciyar masoya, haka mukaita musayar zafafan kalamai nida Fu'ad har muka karasa airport É—in, zama mukayi muna jira sai nan da minti goma sha biyar jirgin da zaije garinsu zai tashi, Uncle Fahad ya zuba mana ido yana murmushi yace "Duk kun É—auki waya kunata chat kun manta dani awajan, Su'ad dawa kike chat ne?" FAHAD ya aika mata da tambaya yana kokarin leka screen na wayar tai saurin kifa wayar a kan cinyarta kana ta basa amsa
"Da Ameerah" Fu'ad ma wayar ya ajje suna ɗan taɓa hira har jirginsu yatashi raina duk ba daɗi haka muka koma gida.

Da yamma ina zauna inda nasaba zama na cikin gidanmu wata yar rumfa ce da'aka kawatata da shuke shuke kala kala wajan yanada daÉ—in zama ga iska dake kaÉ—awa, kamshin wajan kawai ya'isa yaja hankalin mutum ya zauna, Uncle Fahad ne yakaraso wajan cikeda damuwa yaja kujera ya zauna kusa dani yajima yana kallona batare da yace komaiba na kula yana cikin damuwa hakan yasa nace "Uncle lafiya kake kuwa" ajjiyar zuciya yasauke a fili tareda saka hannunsa ya shafi sumar kansa kana ya ce "Besty ina cikin damuwa sosai, wata yarinya nakeso amma narasa ta hanyar da zanbi na faÉ—a mata ina sonta, tsoro nakeji gani nake kamar bazata soni ba, besty bani shawara bakiji yanda zuciyata take kaunar yarinyar ba" saida nayi dariya sosai sannan nace "Wacce mai sa'ace wannan da har Uncle É—ina yake shayin gaya mata yana sonta! kasan me kafuto kawai ka faÉ—a mata na tabbata zata soka, kai kasan yanda ka haÉ—u kuwa ko wacce mace zatayi farin ciki ace namiji kamar kai mai tarin ilimi hankali da nutsuwa babban likita yace yana sonta na tabbata komai takeji dashi kafita, bama haka ba mazai hana kasami mahaifinta ka gaya masa kanason yarsa yabaka dama ka gana da'ita kaga shikenan in yayi na'am dakai itama dole tabi" kai kurum ya girgiza batare dayace komaiba yabar wajan.

Prince AMEEN Fu'ad lafiya yasauka airport na garinsu manyan motocin masarauta daya gani cikeda airport yasa ya dafe kansa cikeda damuwa yake takawa, Allah yasani baiso mai martaba yasan da dawowarsa ba shifa sam bayason rayuwar nan ko yaushe yana kusada sarki Allah ya sani baya ra'ayin sarautar nan, yana kokarin guje masu yaji muryar Chiroma yana dariya yace "Barka da zuwa magajin sarki" Fu'ad dafe kansa yayi🤦‍♂️ cikeda damuwa yake kallon Chiroma yace "Kaine ka gayawa Mai martaba yau zan dawo ko?" hmm yayi kwafa tareda cikin jibgegiyar motar da Sarkin mota ya buɗe masa, tafiyar yan mintuna takaisu gidan sarki, sosai ake murna da zuwansa musamman Deejah da Juhaina nan ya baje cikinsu sai surutu suke masa da kyar yasamu ya zille zuwa sashinsa na gidan mai martaban.

Kanol Usman na zaune cikin falonsa Fahad yai sallama cikeda ladabi yazauna saman carfet yana gaida Daddy sannan ya sunkuyar da kansa yana wasada yan yatsun kafarsa yafara magana muryarsa na rawa "Daddy daman ina son na ce" yanda yake magana a rarraɓe yasa Daddy yadakatar dashi da faɗin "Nutsu Fahad gayamin damuwarka kai tsaye yanda zakai magana da Amina kullum ina gaya maka karinkamin kallon nine yayanka ba Amina ba ina jinka" kasa Fahad ya kumayi da kansa kana yace "Daddy daman sonake kamin izini inason Su'ad sona gaskiyya inhar ka amince auranta zanyi! nafara zuwa kamin izini na nemi amincewarta" Daddy farin ciki ya lulluɓe zuciyarsa shi daman yadaɗe yana wannan hasashan cikeda farin ciki yace "Nabaka Su'ad Fahad na tabbata kai mai kaunarta ne, fatana ka rikemin ita amana kabata kulawa ko bayan raina! basai kayi mata magana ba kabarni da'ita kawai gobe insha Allah zanje karaye muyi magana da Baba Sunusi zan tsaida ranar auranku banason aja lokaci burina daman ako da yaushe naga na aurar da Su'ad kafin Allah ya karɓi raina kasan yanayin cutar danake fama da'ita ba lalle nasake shekara nan gaba a raye ba" Kanol yakarasa faɗa cikin damuwa "Insha Allah Daddy zama ka wuce hakan ai kanabin ka'idoji kuma kana kan magani" murmushi Kanol yayi tareda maida kansa saman kujera yana lumshe ido shi kaɗai yasan maiyakeji ajikinsa a jiya zuwa yau daya dawo Kano shi kaɗai yake jin matsanancin ciwon da cikinsa keyi.......✍🏻

07039793439
[6/4, 7:46 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA* 🌹

Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️

Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

5&6

Kanol yashuga É—akin Ummi da murmushi a fuskarsa, Ummi dake tsaye jikin madubi tana shafa humra tajuyo cikeda mamaki tana kallonsa, ba kasafai ya cika shugowa É—akin matansa ba kusan saidai su samesa a samansa, ajje humran tayi tazo kusa dashi gefan gado ta zauna, jawota yayi jikinsa suka kwanta saman gado yana dariya "Kanol da'alama yau kana cikin nishaÉ—i gayamin maiya saka farin ciki haka" sake rukota yayi jikinsa yana murmushi "Abin farin ciki yasamemu Dr yanzu Fahad yake gayamin yanason auran Su'ad harma nayi wayada Baba sunusi mun tsaida rana nan da sati huÉ—u masu zuwa gobe ma zanje karaye mu sake tattaunawa, ni uban ango shi uban amarya" Ummi da itama daÉ—i ya kumeta tasake kankame mijin nata tana faÉ—in "Kai naji daÉ—in zancan nan sosai Allah yasanya albarka amma Mami bata sani ba", "E sai gobe zan gaya mata na shuga É—akinta naga sunyi barci itada É—iyar tata" anan Kanol yai shirin kwanciyar barci Ummi tana mitar yatashi su koma samansa yace "Dan Allah Dr kibarni na kwana anan daga yau fa shi kenan bazan sake kwana anan ba" shuru tayi kawai taja masu bargo suka koma suka kwanta.

*MUTUWA YANKAN KAUNA*
Chapter 4 · 0% Book details