← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 24

Sashe 13

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe shida dai dai jirginsu Suwaiba ya sauka a garin legos ikko ikon Allah cunkus ɗakin tsumma😹itada kawarta ne hotal suka kama suka ɗan huta bayan sallar mangariba Suwaiba ta wuce gidan Fu'ad, ta tarar baya nan hakan yasa tasa makulli ta buɗe karamar kofar shuga gidan ta shuge ciki ba kunya, ɗakuna biyu ta gani cikin falon ta murɗa handling na kofa ɗayar tajita a rufe hakan yasa ta nufi ɗayar tana murɗawa ta buɗe ta shuga, wanka tayi ta shirya cikin wasu shegun kaya kanana masu masifar kyau da fusgar hankali, ta feshe jikinta da kalolin turarukanta da wanda Anty Jameela tabata wanda ta karɓo daga wajan boka🤭

Takwas dai dai Fu'ad yashugo gidan bakinsa É—aukeda addu'ar shuga gida harda sallamarsa kamar wanda yabar mutum a gidan, ajje ledan abincinsa yayi saman kujera yana shirin shuga É—akinsa yaji an rungumosa ta baya ba karamin tsorata yayi ba saboda shidai yasan shi kaÉ—aine agidan, bai ankare ba yaji an soma shafa jikinsa ana kokarin É—ora hannu kan J É—insa, afusace ya jiyo yana karanta ayatul kursiyyu domin azatonsa gamo yayi saidai wazai gani inba gizo idanunsa sukai masa ba Suwaibace wannan a fusacen dayake ya danki wuyanta yana faÉ—in

"Malama maiya kawoki gidana maiya sake dawo dake rayuwata bayan yaudarar da kikamin saboda kin maidani sha sha sha shine yanzuma kika dawo ki yaudare ni?",

Suwaiba da idanunta suka furfuto tafara hango mutuwa saboda yanda ya rike mata makogwaro tace "Ka sakeni zangaya maka wanda ya turoni" bai saketanba saima kara rike mata makogwaro dayai idanunta dayaga ya firfito tana kakarin mutuwa yasa ya wurgata ta bugu da kujera tasaki ihu bai tausaya mata ba yasa kafa yatake hannunta

"Zaki gayamin ko saina haÉ—aki da hukuma" kanta take girgizawa tama kasa magana sabida azabar da hannunta da kanta keyi,wayansa ya É—akko ganin yana shirin kiran yan sanda yasa ta magantu

"Anty Jameela ce ta turoni na shugo rayuwarka muyi rayuwa na zama karuwarka saboda batason kazama sarkin bare" dafe kansa yayi ya koma saman kujera ya zauna kamar kuma wanda aka kunna yamike ya fara jan kafafun Suwaiba bai tsaya da'ita saida yakaita kofar gate can waje ya wurgata ya koma ciki ya É—ebo sauran kayanta ya watsa mata

"Wannan yazama na farko kuma na karshe dazaki kuma shugomin gida, ki gayawa wacce ta turoki insha Allah nafi karfinta itada duk wani sharrinta, kar nake kallonta a tafin hannuna,harya juya zai koma ciki yadawo yamika mata hannu

"Ina kika sami makullin da kika buÉ—emin gida"

"Anty Jameela ta bani a sashin Abie É—inku ta É—akko" murmushi mai ciwo Fu'ad yayi yamika mata hannu

"Bani makullin" tamika masa yakoma ciki yana sauke ajjiyar zuciya.....✍️

Saura kiris pages su daina fitowa na daina posting É—in book É—in nan a kowanne group sai group É—in Kukan zuciya real fans indai har kinsan kinason cigaba da bin labarin nan to masa yimin magana ta wannan lambat nai adding É—inki a group 07039793439
[6/4, 7:48 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹

Story and writtin by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️

Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

17&18

Dakyar Suwaiba ta koma hotal ɗin data sauka saboda wani azababban ciwo da wuyanta yake mata lalle ta tsallake rijiya da baya a irin rikon dayai mata tabbas zai iya kasheta tasan inya kasheta yakashe banza saboda ba wani gata ne da ita ba, iyayanta bawasu masu hali bane tasan kasar nan tamu anaji ana gani sai a rufe maganar tunda shi ɗan manya ne bakaramar nadama tayi ba data bari kawarta ta ruɗe ta harta karɓi wannan aikin na Anty Jameela datake ganin bashida wani wuya.

Yau da nishaÉ—i muka tashi kasancewar sunday ne Uncle yana gida bai fita hospital ba kamar yanda muka saba tare muke komai na gidan yanda Uncle yake kula dani yasa gaba É—aya nama manta da Fu'ad gaba É—aya na mallakawa Uncle zuciya na, bayan munyi sallar azahar wanka mukayi tare muka fito danning zamuci abinci, ina sanye cikin doguwar rigar atamfa A shape wacce ta matukar zaunawa a jikina ni kaina nasan nayi kyau saboda yanda nayi kiba na kara haske, ga wani É—auri danayi sosai Uncle ya yaba da kwalliyar tawa sai bina yake da kallo, jerowa mukai zuwa wajan danning É—in ina tsokanarsa ina dariya tare mukaci abincin kamar yanda muka saba ciyar da juna, falo muka koma ya kunna kallo ni kuma na kwantar da kaina saman cinyarsa ina shirin barci, buga kofar da'akai yasani mikewa zanje na buÉ—e kofar

"Besty keda kika soma barci ki zauna ni na buÉ—e" harara nai masa irinta masoya nace

"Saidai ayi riga rigayan zuwa"kafin na rube baki yatafi da sarsarfa nima na take masa baya ya rigani zuwa saidai ganin waÉ—anda suke bakin kofar yasa shi yin turus kunya duk ta kama sa ganin kayan dake jikinsa Mami suka shigo falon da sallama itada Ummi a
kunyace yadawo falon yana wani sinkuyar dakai kamar wanda yaiwa sarki karya🤭

Ina jikin Mamina na makalkaleta Ummi sai bina take da kallo nasan itama cewa zatayi nayi kiba, danko ni nasan ba karamar canzawa nayi ba, Mami data kasa daurewa tace "kai masha Allah Dota É—ita nayi murna sosai Allah ubangiji ya inganta nasan wannan kiba bata haka nan bace mai dalili ce da'alama nakusa samun jika" da gudu na mike na shuge kichin na kawo masu lemu da cake Allah yasa inada abinci hakan yasa na haÉ—o masu dashi, Ankul yana gama gaisawa dasu ya koma ciki danba karamar kunya yajiba yanda suka gansa.

Su Mami sunjima sosai sai bayan sallar mangariba suka tafi.

Anty Jameela na tsaye gaban dinning tana shiryawa Abie abinci da lamun dayasha magungunan data amso a wajan boka, wayarta dake ajje kan dinning tashuga ruri ganin Suwaiba ce mai kiran yasa ta saurin ɗagawa tareda jan kujera ta zauna, jin abinda Suwaiban ke faɗa mata yasa ranta yaɓaci bata jira futawar Abie ɗinba ta wuce ɗakinta ta kule can ciki bayan ta dannawa ɗakin key
Wayan boka ta kira tana sanar masa abinda Fu'ad yamata

"Kinga ki futa hanyar yaron nan ba abinda zamu iya akansa tsaye yake kan addu'a da azkhair gashi yana yawan karatun kur'ani gefe kuma ga watanan datake kara masa addu'ar kariya, kinsan aljanu nawa natura suna dawomin nikam na futa hanyar yaron nan bazai kassarani ba"

Anty Jameela ranta ɓace ta futo daga ɗakin nata saurin saita kanta tayi ganin Abiee zaune bisa dinning yana aikawa cikinsa lemu, zama tayi kusada shi tana kara masa sannu da hanya, saida yagama cin abinci yabita da kallo

"Narasa maiya zaunar dake agarin nan kinki komawa kaduna" taɓe fuska tayi

"Ni kawai garin yafuta araina nafison zaman nan kaima kabar aikin nan ka dawo nan ka amshi sarautarka" murmushi yayi kawai yana danna wayarsa.

"Niko Alhaji nace maizai hana yaron nan Ameen asama masa wata a aura masa shekarunsa kullum daÉ—a ja suke yakasa ajje iyali"

"Kamar kin shuga raina abinda yake cimin rai kenan ko jiya nai masa magana amma sai cewa yayi shi bayanzu zaiyi aure ba shekarunsa fa yanzu Talatin da shida, inaga zanyiwa mai martaba magana a haÉ—asa da Juhaina ta wajan mai martaba" da sauri Anty Jameela tace

"Ai kuwa karkayi haka yarinyar nan rannan naji suna hira da Khady tana faÉ—a mata É—an wazirin gombe ke sonta" shuru yayi baice komaiba, jin alamun bazai sake cewa komaiba yasa Anty Jameela tace

"Ni badan kar'ace naso kaina ba sai nace inba damuwa a haÉ—asa da Baraka kanwata kaga itama taki futar da wani tsayayye suje can su sasanta kansu" nan ma shuru Abiee yayi baice komaiba sai can yace

"Tabbas kinyi hange mai kyau gobe zan tura makama su tambaya mana inta amince ni banida damuwa da Ameen lamarinsa yafara bani tsoro aure zan masa saidai kawai atura masa matar legos" yana gama faÉ—ar haka yamike yafuta.

Washe gari tana ganin Abiee yafuta itama ta fuce zuwa gidansu gargaÉ—in Baraka tayi akan indai aka tambayeta tanason Fu'ad ta amsa da E kuma karta sake tasa soyayyarsa aranta dan bazama ne zai kaita ba aiki zatai mata karta sawa kanta wata soyayya.

Wasa wasa saiga batun auran yakankama tuni har an tsaida rana abinka da manya duka sati biyu aka sanya bikin, ango yanacan baisan abinda ake ba, dan tunda yasa kafa yabar garin bai kuma zuwa ba mai martaba yana kai masa ziyara akai akai haka Abiee É—insa Umma ko suna waya kullum, yau tun safe yana kwance bashida lafiya wani azabanban ciwon ciki yake kamar zai mutu, wayar abokinsa Usman yakira yana sanar masa bayada lafiya, Usman ya shaida masa baya gida ya shuga makaranta yanada class, Dr Haris yakira yace gashi nan zuwa yadubasa.

Saida yagama aunasa yakoma ya zauna cikeda damuwa

"Gayses kana cutar da kanka dayawa, kanada bukata amma kaki ajje mace saboda wani banzan dalilinka, inma bazakai aure ba maizai hana kasami wacce zatana sauke maka bukatunka ga matanan dayawa a gari sai wacce ka zaɓa, kanada kuɗi kanada kyau babu macan dabazaka iya mu'amala da'ita ba, amma ka tsaya kana neman kashe kanka" murmushi kawai Fu'ad yayi

"In ka gama sharhin bani maganin dazan sha ka fucemin daga gida dankai kana abu dolene saina bi ra'ayinka kai barima na maka ta mahaukaci duk matan nan kallon maza nake masu, tunda na rasa Princess banajin akwai sauran wacce zata sake burgeni"

"FaÉ—a kake amma ka bani dama wallahi yau saina kawo maka wacce zata É—ebe maka kewar Princess É—in" É—agowa Fu'ad yayi yana kallon Haris batareda yace komaiba, magani Haris yaje yasiyo masa ya kawo masa sannan yayi masa sallama.

Washe gari yana office saiga Haris dawata kyakkyawar yarinya kallo ɗaya Fu'ad yayi mata ya kauda kansa yana ta'awizi, zare glass ɗin idanunsa yayi wanda yazame masa jiki ko yaushe ka gansa yana manne da idanunsa wanda ba karamin kyau yake kara masa ba, kallon Haris yayi tareda haɗe gira ya ɓata rai afusace yadakawa yarinyar tsawa wacce tasata fucewa da sauri jikinta yana rawa.
Chapter 13 · 0% Book details