← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanaki uku mukayi muna zaman makokin Uncle, har sannan ba labarin Ameera,abinda ya kuma É—agan hankali kenan nakan shuga damuwa musamman idan natuna amanar da Ankul yabani hankalina yakan tashi, sosai yaya mukhatar yake tsaye kan case É—in, kwanan Uncle goma da safe ina zaune a main falo aka kwankwaso kofa naje na buÉ—e yan sanda ne guda biyu mace da namiji iso nayi masu zuwa ciki na kira Ummi da Mami É—an sandan ke magana

"Munzo daga stesion ne munason zamu tafida Amina matar Fahad zata amsa mana tambayoyi saboda zarginta da'ake dasa hannunta a kisan Fahad É—in"

Zumbur Mami tamike tareda dafe kirji tana salati tace "Daman ance ku yansanda kun fiye sharri yau kuma sharrin naku kan ɗiyata ya sauka ni na raini abata nasan halinta bazata taɓa goyan bayan zalinci bama bare takai ga kisan kai, kutashi ku futar mana daga gida tunban farfasa maku kafafuwa ba"

Ummi ta dafa kafaÉ—ar Mami tace "Kibari su tafi da'ita tambaya kawai zata amsa masu ta dawo", hannuna Ummi ta kamo tace "Gatanan kuje ni nasan ba hannun ta acikin kisan nan" Mami ciki ta shuge ta É—akko wayarta ta kira kwamishina ko gaisuwar dayake mata bata amsaba tace "Tayaya zaka turo yaranka suzo su tafi da yata"

"Kiyi hakuri Mami bincike ne yabiyo ta kanta, yaran da muka kama sunce matarsa ce ta aikosu su kashe sa saboda bashi take soba aka aura mata shi, bincikenmu yatabbatar da Su'ad batason Fahad dole akai mata
Mami ajje wayarta tayi ta saka hijab tacewa yan sandan "Naji kuje zankawota da kaina amma bazata shuga motarku ba" ba yanda suka iya haka suka tafi nidai har sannan ina tsaye ina binsu da kallo zuciyata wani irin zafi takemin wanne irin sharri ne wannan maye alakata da yan fashin nan wanne laifi namasu da zasumin wannan babban kazafin, hannuna Mami taja tana

FaÉ—in "Karki damu Su'ad wallahi nasan sharri ne tayaya zakisa a kashe Fahad tabbas akwai wata a kasa kodai akwai wanda suka sami matsala da Fahad yaturo aka kashe sa yakeson ya É—ora maki laifin ba komai kiyi addu'a insha Allah komai zaizo da sauki".

Bayan munje duk yanda Mami taso subata ni mutawo tare ki sukayi saima sakayani dasukai, ina kallon Mami tabar stesion ɗin ranta aɓace, duk yanda muke zaton case ɗin yawuce haka dan gaba ɗaya laifin kisan ni aka ɗorawa tuni yan sanda sun turamu kotu, yan uwana sai shuge da fuce suke ganin anbada belina amma sam D P O yaki, ranar Monday muka fara halartar kotu, nanma ba nasara saima tarin tambayoyi dasuka rinkamin danma lauyana yana bani kariya sosai saboda kwararran lauya Mami ta ɗaukarmin, Alkali ya ɗaga shari'a nan da sati biyu ya kuma umarci yan sanda da lalle su nemu damo wanda ake zargin shiyasan wacce ta turosu dan yazo yafaɗi gaskiyya.

___________******____________

Fu'ad yadafe kansa dayaji yana sara masa saboda damuwa gaba ɗaya yana cikin damuwa, shirye shiryan tafiyar sa England dayake yasa bayama da nutsuwa, sam baida labarin rasuwar Fahad duk da yakan tunasa lokaci zuwa lokaci, yakanyi mamakin wai duk yanda suke da Fahad amma saisu share fin wata guda ba wanda ya kira kowa gaba suke ba kawai kowa yanjin nauyine duba da abinda yafaru, badan ransa yasoba Abiee yatakura masa lalle saiya tafi da Baraka yarinyar da yau watanta guda kenan amma bai taɓa sakata a idonsaba, yau da wuri ya shugo gidan saboda yanason yakaita amata shirye shiryan tafiya, wani cost zaije wanda zai shafe watanni takwas a london, wanka yayi yaci abincin daya shugo dashi sannan ya koma falo ya kwankwasa kofanta ya koma saman kujera ya zauna.

Baraka dake zaune gefan gado tayi tagumi, zumbur ta mike jin bakon lamari yau wacce bakuwa suka samu a gidan har take bugo mata kofa, plate shoe ɗinta ta zura tareda yafa ɗan kwalin doguwar rigar dake jikinta ta futo, ba karamin faɗuwa gabanta yayi ba ganin Fu'ad a hakimce saman kujera da wannan ranar, kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kai yana taɓe baki, shi baiga amfanin wannan auran da'akai masa ba, waya gaya masu yana son farar mace shi sam arayuwa baya bukatar mace fara, kuma taɓe baki yayi ganin yanda ta zauna kasan carfet saida yamike sannan

Yace "Ki shirya akwai wanda zai kaiki kiyi pascort" ɗakinsa ya shuge ya kira direbansu na office yace yazo zai aikesa, yana zuwa ya haɗata suje ayi mata abinda yakamata, ba karamin haushi Baraka tajiba, ta kudurci aniyar saita cusawa Fu'ad soyayyarta kota halin kaka bata taɓa ganinsa ba sai yau akallo ɗaya kuma datai masa ta kamu da mugun sonsa ayan kwanakin dasuka rage masu ta fara futowa ta sabarwa kanta zaman falo wani bin tana nan yake shugowa tai masa sannu da zuwa amma ko kallon inda take bazaiyi ba zai shuge ɗakinsa, sosai take shuge masa har ɗakinsa takan shuga in yana ciki musamman da safe ta gaidashi, yau tana shuga tasame sa kwance ya kifa cikinsa yana sauke numfashi ya haɗa ubangumi duk da fankar dake yi a ɗakin, karfin fankar ta kara tareda kunna A c cikeda karfin hali ta hau saman gadon tana masa sannu, janyota kawai yayi jikinsa atake yafara aika mata da sakonni, bata wani tsaya jan aji ba tabada kai bori yahau😹 dan itakam daman ta jima tana son zuwan wannan ranar duba da shekarunta ayanzu zasu kai ashirin da tara zuwa talatin amma ta kame kanta zata iya rantsuwa da Allah babu wani namijin daya taɓa koda rike mata hannu, ba karamar azaba tasha ba a hannun Fu'ad dan da zafi zafi yake gabatar da komai bako alamar tausayawa, saima daya sami nutsuwa ne yaɗan tausaya mata ganin yanda lokaci ɗaya jikinta yai sanyi sosai bathroom ya shuga ya tsabtace jikinsa sannan ya haɗa mata ruwa zafi yace taje ta gyara jikinta kafin ta futoma har yayi barci, murmushi tayi ganin yanda yake sauke nimfashi ahankali ta sumbaci laɓɓansa ta fuce daga ɗakin tana murmushi, tun daga wannan ranar Baraka ta koma ɗakin Fu'ad da kwana bai hanata ba saima farin ciki dayai da hakan,ahankali suka saba saidai har sannan baya sakar mata fuska zata iya rantsewa bata taɓa ganin dariyarsa ba, dama shi can bayada fara'a tun bayan rabuwarsa da Su'ad sai abin yai gaba ga kuma damuwar wannan aure da'aka kakaba masa, ranar alhamis jirginsu ya ɗaga zuwa birnin londan, ko cikin jirgi tana lafe ajikinsa tayi barci ta tashi har jirginsu ya sauka, Usman abokinsa yazo tararsa saida yakaisa har gidan dazai zauna kana ya koma gidansa yakawo masu abinci shida tasa matar.

__________Ranar da muka koma kotu ta cika fiyeda zama na farko yan sanda kuma sunzo da damo wanda ya gudu a daran, sosai yakafe kan lalle nina sakasu kashe Ankul abinda yaja hankalin mutane sosai, Alkali na shirin yanke hukunci lauyana da baisami zuwa ba sai sannan ya turo kofar kotun yashugo yana neman afuwar alkali.

Yace "Ya mai girma mai shari'a inason na gabatar da shaidata wacce zata tabbatar da ba Amina Usman Karaye bace tai wannan kisan kan"

Alkali yace "Kotu tabaka dama"

Ganin Amira danayi yan sanda sun shugo da'ita ta tsaya tana kuka kamar bazata ce komai ba, gaba É—aya bata cikin nutsuwarta har saida alkali yai mata magana ta nutsu tayi magana sannan tafara magana

"Sunana Mariya Fahad Aliyu, ranar alhamis tara gawata da misalin karfe biyu na dare ina kwance a ɗakina naji tsayuwar mota a bayan gidanmu labulan ɗakina na ɗaga na lega windo dai dai sannan wannan ta nuna ɗaya daga cikin yan fashin ya hauro gidan namu yabuɗewa sauran gate suka shugo, yanda naga bindugu da wukake a hannunsu saiya tsorata ni hakan yasa nai amfani da wayar Anty na dake hannuna na kira Mami yayar mahaifina ina kuka na sanar mata yan gashi sun hauro gidanmu, Mami saboda tsabar kiɗimewa bata kashe wayar ba ta futa tana sanarwa da Ummi halin da'ake ciki, Ummi ita ta kira C p Mukhter tagaya masa, anan na kashe wayar ganin Mami bata kashe ba, sanda yan fashin suka shugo gidan ɓuya nayi can gaban gado ina jiyo abinda ke faruwa a falo amma tsoro ya hanani fitowa, sanda yan sanda suka shugo gidan wannan ta nunana damo ya shugo ɗakina ganin zanyi ihu ya toshe min baki, ya yage net ɗin dake jikin windon ɗakina wanda ya futo ta waje ya jefani sannan shima ya diro ya jani muka faɗa wani babban rami dake bayan gidanmu, wani yakira a waya bayan yaga wucewar motar yan sandan yazo ya ɗaukemu suka kaini wani gida suka kulleni a ɗaki sau ɗaya wani bawan Allah yake kawomin abinci da rana mai gadin gidanne yace yanajin tausayi na zai taimakamin na futa.
Ranar danayi sati a gidan mamata taje ta gayamin ita ta tura su damo su kashe Abbana dan tagaje dukiyarsa dan Allah na rufa mata asiri nace bazan iya rufe wannan asirin ba anan ta umarci damo da lalle in dare yayi nima ya aikani inda babana yatafi...🙆‍

Comment and share

Eid Mubaraka my lovely fans🥰😍❤️🌹
[6/9, 7:02 AM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹

Story and writtin by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️

Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

23&24

Ranar nayi kuka sosai sai dare wanda ke gadin gidan yazomin a tsorace yace na biyosa, tare muka gudo daga zariya da mukazo kano ya dankani a hannun yan sanda anan CP yaganni ya É—aukeni zuwa gida na gaya masa komai yanda yafaru sai yau nazo nan domin na shaidawa duniya cewa ba Anty bace ta kashe Daddyna ba Ummana ce" tana zuwa dai dai nan ta fashe da kuka tareda zubewa a kasa Ummi ta É—auketa suka tafi da'ita asibiti nan take Alkali yawanke ni sannan ya yankewa Zainaba da su Damo hukuncin kisa ta hanyar rataya mahaifiyar Zainaba dake cikin kotun itada Zainaba ganin yanda yan sanda suka kama Zainaban yasa ta yanke jiki ta faÉ—i nan take rai yayi halinsa.
Chapter 16 · 0% Book details