← Book details Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 24

Sashe 10

Kukan Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fahad yadafe kansa cikeda damuwa ya ce "Dr narasa yanda zanyi Baban karaye yadage kan maganar nan halin yanzuma fa harya tsayar da rana gaskiyya inaga barin garin nan zanyi inkomai ya dai daita na dawo" "Kaje ina?" yaji muryar Ummi tana faÉ—a tareda shugowa É—akin "Wallahi kasani ko mutuwa Su'ad tayi sai an É—aura auran nan an kaita gidanka inyaso daga gidanka a wuce da'ita kabari, Mami ko kallon inda Ummi da Fahad da suke magana batai ba gaba É—aya hankalinta naga Su'ad ganin yanda take sauke nunfashi a hankali yasa hankalinta kwanciya.

Da kuka sosai Nafarka lokacin ɗakin ba kowa sai Yaya Fatima Ummi da Mami sun futa, Yaya Fatima ta hararw ni kamar zata kaimin duka cikin masifa ta ke faɗin "Su'ad yanzu abinda kika zaɓarwa kanki kenan mai Fu'ad yakeda shi wanda Fahad bashi da? dan Allah ki kwantar da hankalinki ki rungumi kaddararki, a rayuwar nan fa kowa kika gani da kalar kaddarar sa" Kuka nake sosai nace "Na hakura da Fu'ad tunda harya iya karya alkawarinmu yatafi yabarni bayan munyi alkawarin duk runtsi duk wuya muna tare amma ya iya tsallake ni yatafi ya barni na hakura Yaya na karɓi zaɓin Daddy na zan cika masa burinsa bayan ransa zan tabbatar da wasiyyar sa daya barmin koda kuwa hakan na nufin tarwatsewar zuciyata da tabbatuwar kunci a rayuwata,"

"Insha Allah ma bazakiyi kunciba a gidan Fahad zaki samu farin ciki da walwala fiyeda kowacce mace dake gidan mijinta nasan irin son da Fahad yake maki kema kuma kinsan hakan kawai soyayya da kauna ce suka rufe maki idanu kika kasa tantance Aminci zaki zaɓa ko kauna"

"Na zaɓi Aminci nabar Kauna da Soyayya bari nahar abada bazan sake soyayya ba nayi banji da daɗi ba nabarta har karshen numfashi na, ki gayawa Fahad a maidani gida ni naji sauki"

*Ina bawan Allah Fu'ad*

Yana futa a gidan yatare nape ko gaya masa inda zai kaisa baiyi ba ya kifa kansa saman kafafunsa shi kaÉ—ai yasan maiyake ji a zuciyarsa, saida suka hau babban titi kana mai nape É—in

Yace "Ranka yadaÉ—e ina muka dosa" batareda Fu'ad yaÉ—ago ba yabasa amsa da

"Fara kaini Atm dake kusa na ciri kuÉ—i sannan ka karasa dani airport" basu jima suna tafiya ba mai nape ya faÉ—a masa gasu a Atm Fu'ad yafuta yacuro kuÉ—i sannan suka cigaba da tafiya, suna isa airport ya saka hannu a aljihu ya ciro dubu huÉ—u yabawa mai nape É—in

"Yallaɓai ɗari biyar ne kuɗinka" hannu kawai yaɗaga masa batareda yace komaiba yasoma tafiya har ya shuge cikin airport ɗin mai nape ɗin na kallonsa, haka kawai yaji tausayin bawan Allah daga gani yana cikin damuwa "Allah ya magance maka damuwarka yahaɗaka da farin cikin duniya dana lahira yabaka duk abinda kake nema" mai nape yafaɗi haka yana share hawayan fuskarsa rabonsa dan gidansa tun bayan sallar azahar ya futo nema ko abinda iyalansa zasuci da rana bai basu ba mashin ɗinma ba nasa bane na haya ne, gida ya koma yabawa matarsa dubu biyu yace suyi cefane sannan ya cigaba da aiki, Fu'ad yana shuga airport ɗin baisha wahalar samun jirgi ba saboda yasaba da ma'aikatan wajan a recepsion ya zauna kasancewar sai nan da minti goma sha biyar jirgin zai tashi, shirun dayayi tunanin Su'ad yake har sannan yana jin ihunta sanda take faɗin _"Fu'ad come back please"_ ya share hawayan idanunsa yazaro glass daga aljihunsa yasakaya a fuskarsa suka ɓoye jan da idanunsa sukayi.

Anty Jameela wacce guguwa tai sama da ita bata ajjeta ko ina ba sai gaban wata yar karamar bukka wacce a ido idan ka ganta bazaka taɓa zaton ko kaza zata iya shiga ta zauna ba bare mutum, bukkar ko kofar shiga babu amma tana tsayawa a gaban bukkar ta buɗe ta shiga da sauri tana kwalawa bokan kira harta zauna gaban sa inda ya bayyana "Ranka ya daɗe gashi na aiwatar da duk abinda kace" karɓar abinda ta mika masa yayi tareda wurgasa ya shuge cikin wata kwarya wacce abin yana shuga kwaryan takama da wuta, wani ihu Boka yayi tareda kecewa da dariya

Yace "Burinki ya cika Fu'ad zai zama yanda kike so kallesa nan" lekawa Anty Jameela tayi cikin yar tukunyar dake gaban bokan zaune taga Fu'ad a wani waje da'alama recapsion na filin jirgi ne fuskar nan tasa ba walwala, É—agowa tayi tana kallon boka bakinta har rawa yake wajan faÉ—in.

"To maiyakeyi anan É—in? kuma ina zashi tsoro nakeji karya bar kasarnan ban gama aikinba"

"Ba'inda zaije gidama zai dawo yana kano daga gidansu wata yarinya yake wacce yake masifar so, nasoma ace itace zata mana aikin nan so ba yanda zanyi yarinyar tanada addini sannan babarta a tsaye take akanta da addu'o'i sau uku ina tura aljanu na suna dawomin da konan nan jiki shiyasa na haÉ—a aikin da tsohuwar budurwarsa Suwaiba duk yanda zakiyi kiyi dan ganin yaje legos sun haÉ—u da'ita dan itace cika makon aikin mu, ya cilla mata kullin magani wannan ki tabbatar yasha a cikin lemu zamu saka masa a zuciyarsa ya zarto nan gidanki ke kuma kina zuwa kije sashinsa ki buÉ—e lemu ki zuba a ciki dazaran yasha zance yakare" "To boka ina godiya amma inna buÉ—e lemu na zuba wani abu ai zai nuna alamar an buÉ—e"
"Baki yarda da aikinmu ba, kenan kina shakku akai" da sauri ta girgiza kanta alamar A'A kafin tayi wata magana taji an watso ta wajan bukkar ta zura takalmanta ta soma tafiya sai da tayi nisa kana ta juyo fili ta gani fetal ba alamar bukkar ta ɓace ɓat🙆‍♀️

Prince rai ɓace ya sauka a garinsu, kai tsaye G R A ya wuce gidan mahaifinsa bayason a masarauta asan yadawo yasan halin mai martaba da sakawa zuciyarsa damuwa akan lamuransa shiyasa bai doshi gidan ba so yake saiya dawo dai dai tukunna, can kasan ransa yana son zuwa masarauta yaga Umma amma ji yake kamar ana fisgarsa zuwa gidan Abie.

Anty Jameela ta gama zuba maganin kenan a cikin lemu ta futa shi kuma ya shugo gidan, haka kawai yaji kamar wanda ake jansa zuwa sashinsa inda baima cika zama ba, yana shuga ya buɗe fridge ya ɓalle murfin lemu yakafa kai yasha bako bisimillah😰kuskuren dayayi kenan, wani irin juya yaji kansa yanayi hajijiya ta ɗebesa luuuu yafaɗa saman kujera ya soma barci,

Alhamdulillah Su'ad ta sami lafiya harta koma gida mun bar hospital na daina kuka a fili na rashin Fu'ad sai KUKAN ZUCIYA danake na goge komai na Fu'ad daga wayata kama da lambar sa hotunan sa duk wani abu da nasan zai tuna min da Fu'ad, ganin hankalin Su'ad ya kwanta yasa Mami da Ummi suke ta shirya shiryan bikin Su'ad da Fahad, haka shima Fahad tuni yasai sabon gida anan sharaɗaG R A katon gidane daya cikasa da kayan alatun more rayuwa duk wani abu dayasan Su'ad tanaso saida ya zuba a gidan a ɓangare guda ba karamin lefe ya haɗaba kamar wanda baisan ciwon kuɗi ba haka yake kashe su har saida Ummi tai masa magana, Mami da yaya Fatima sukaje suka dawo da santin gidan Yaya tasami Su'ad wacce yanzu batada inda take zama samada ɗaki sabida karta ga Fahad, har sannan banajin sonsa kawai zanyi biyayya ne "Kinga gidanki kuwa kamar na wata yar shugaban kasa gaskiyya ba karamin so Uncle ke maki ba, da mukaje faɗi yake Fatima dan Allah kalli gidan nan kiga in akwai abinda kikasan Su'ad tanaso wanda bansa ba dan Allah ki faɗamin nasaka" taɓe baki nayi ina juyawa yaya baya

na ce "Daman zai faÉ—i haka mana tunda yasan yariga yagama da rayuwata, yarabani da farin cikina"mirmushi Yaya tayi ta futa daga É—akin, tana aikawa da Su'ad harara

Wasa wasa sai gashi yau alhamis saura kwana biyu É—aurin aurena da Fahad har sannan bansakejin É—uriyar Fu'ad inata dai saka idanu zuwansa tunda yace zai zo É—aurin auranmu nasan tabbas zaizo É—in, ba wani taro za'ayi sosai ba kuma ma É—aurin auran a karaye ne shiyasa tun ranar juma'a da yamma Mami dasu yaya fatima sai wasu matan yayun ummi suka wuce karaye.

Da yamma ina zaune nida fadila yar wan ummice kawata ce sosai tun yarinta haka kawai nakejin faÉ—uwar gaba wacce narasa ta maice na É—ora kaina saman kujera ina jiyo Fadila tana waya dasu Mami kamar daga sama naji kamshin turaransa ban buÉ—e idona ba har sanda naji sallamar Ankul wanda ko tantama babu nasan tare suke da Fu'ad, ilaiko muryarshi najiyo yana gaisawa da Ummi data futo daga É—akinta, muryarsa fes kamar bayada wata damuwa, banbuÉ—e idonaba har saida na tabbatar da sunbar falon zuwa sashin Ankul sannan na buÉ—e na É—auki wayata na shuge É—akina inajin yanda kirjina da kaina suke bugawa "Ameen maiyasa maiyasa zakazo ayanzu so kake ka hanani karasa biyayyar danake shirin yiwa mahaifina kanason tarwatsa zuciyata ne" kwanciya nayi lamo har sanda naji wayata tana kara koda bansan wake kiranba amma na tabbata Mami ce dan ring É—inta daban yake a wayana

"Dota kinci abinci kuwa"

"E!" nabata amsa ina sauraron abinda zatace.

"kaiwa Ankul wayanki zamuyi magana na kira tasa baya shuga ko baidawo ba?"

Inama zan iya yiwa Mami karya danace mata bai dawo ba, amma bazan iya ba dole na mike nabi hanyar zuwa É—akinsa, da sallama na shuga suna zaune su biyu da'alama magana suke mai mahimmanci ganin yanda hannunsu yake sakale cikin na juna, banko kalli inda Fu'ad yake ba namikawa Ankul waya nace "Mami ke kiranka, bansan maita gaya masa ba nidai ina tsaye naga ya fuce da sauri ko wayar tawa bai bani ba, na fara tafiya zanbar É—akin naji Fu'ad ya ruko hannuna, na juya ina kallonsa hawaye na zarya a fuskata na tausayinsa ganin yanda ya zabge lokaci É—aya kamar wanda yai jinya banyi aune ba kawai naji na fashe da kuka hannu yasa ya toshe bakina murya kasa kasa

Yace "Princess rufa mana asiri so kike Ankul É—inki ya jiyomu" da sauri yasa hannunsa a cikin jakarsa ya ciro karamin akwati mai É—an karan kyau yasakamin a hannuna ya koma saman gado ya kwanta ni kuma na futa daga É—akin da sauri, banga Ankul ba da'alama baya gidan.
Chapter 10 · 0% Book details