← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 69

Sashe 9

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata karasa maganan zucin ba taji sauka iska akan idanunta ba shiri tabude idanun a mugun rude tana kallonshi, shima kallonta yake ahankali yadan matsa hanunta dayake rike dashi har lokacin yana kallon kwayar idanunta yace "how are you feeling now Jewel?" zaro ido tayi arude tana wani irin kallon shi kafin tafashe dawani irin kuka ta fizge hanunta daga nashi da sauri arude ta yunkuro zata tashi kanta da nashi suka gware, wani irin ihu tasaki da saida ya mike tsaye da sauri yana shafa gaban goshinshi yana kallonta yanda take kuka tarike gaban goshinta tana shafa inda ta bugen yasa da sauri ta dira daga gadon batare data lura da drip din hanunta ba dudda batajin karfi sosai saida tai gaba zata gudu tai wurin kofa, wani irin jiri ne ya debeta tai baya zata fadi da sauri yatareta hakan yasa tafado jikinshi, wani irin ajiyan zuciya yayi yana kallon fuskarta yariketa gam gam, zaro ido tayi hawaye na zuba daga idanunta tana kallonshi bakinta na rawa sosai shima kallonta yake calmly da lumtsatsun idanunshi, saukar da idanunta tayi tana kokarin fizge jikinta daga nashi amma takasa sabida yanda yariketa, sake dago ido tayi dasuka cika da hawaye sosai ta kalleshi koina na jikinta rawa tama kasa magana, ahankali yadan sauke ajiyan zuciya kafin ya dagata ya zaunar da ita akan gadon da sauri ta dau filo tana kare fuskarta dashi jikinta na rawa sosai, dan matsowa yayi kusa da gadon ganin yanda ta rude saukar da muryanshi yayi sosai yace "Hey Jewel calm down, am not gonna hurt you, you are safe okay" kare fuskarta tai da filon sosai hannayenta na rawa daidai lokacin nurse tabude kofan ta shigo sabida ihun dataji, arude Hamida tasaki wani irin kuka tana kara rufe fuskarta da filon tana neman inda zata shige bakinta har rawa yake ta damke filon sosai tace "Ma...ma, Mama, wayyo Allah na Mama!" ta kwalama Maman su kira, ahankali nurse din takaraso gaban gadon ta kalli Aabid dayay folding hannu yana kallonta tace "Sir your patient ta tashi, hello Jewel stop crying, am your nurse, nurse Kuburat, how are you feeling now, meke miki ciwo?" tai maganan tana fizge filon hanunta cikin dabara, fashewa tayi da kuka sosai tana komawa karshen gadon tasa hannu ta daura akan fuskarta tana kuka sosai tana kakkare fuskarta arude tace "pls Mama, ina Mama na?" cikin rarrashi nurse din tace "don't worry Mama zatazo yanzun nan, but for now ga maganin ki kisha, inhar kinsha kinji sauki gobe da safe zamu sallameki, saikije kiga Mama, you drown a ruwa and Sir brought you here" tai maganan tana nuna mata Aabid, ahankali tana hawaye sosai tadan juyoda kai ta kalleshi hada ido sukayi da sauri ta sake dukar dakai tana kakkare fuskarta da hannu daya tana share hawayen datakeyi da bayan dayan hanun, maganin nurse din tazuba a marfi 5ml takai saitin bakinta tana murmushi tace "yauwa to open your mouth kisha ba daci" ahankali tadan juyo dakanta jikinta na rawa har lokacin tadan bude bakinta da sauri nurse din ta zuba mata maganin, hadiye maganin tayi hawaye na gangarowa, murmushi nurse din tace "good" ta kalleshi tace "Sir taci abinci please, I will come back anjima nai checking vitals dinta" tajuya tafita daga dakin, saukar da kanta tayi kasa tana kuka sosai tana gogewa da bayan hannu, kara jan kujeran yayi ya zauna tareda daukan takeaway dayayo mata yabude fried rice din yasa spoon aciki ya mika mata yana kallon fuskarta, kawad dakai tayi chan gefe tana kare fuskarta da kyau, dan murmushi yayi yace "take d food and eat kona duramiki, kinsan menene force feed?" yay maganan yana dage mata gira daya, adan rude tafashe dawani kukan tadan juyo ta kalleshi, hada ido suka sakeyi da sauri takara juyar dakan tana goge fuskarta da hannu, dan matsar da kujeran baya yayi zai tashi hakan yasa tadanyi ihu ta yar da filon ta mikamai hannunta dake bari da sauri, bata abincin yayi yana murmushi takarba da sauri tana goge fuskarta da bayan hannu, murmushi yasakeyi dan hakanan yaji yarinyar na burgeshi, abincin ya kalla ya kalli yanda takeyi da hannu taki diba taci, murya chan kasa yace "nabaki dakaina?" da sauri ta girgiza mai kai batare da ta kalleshi ba tadebo kadan takai bakinta taci, hanunta dake rawa sosai yabi da kallo yace "what's your name Jewel?" dan dago kai tayi ta kalleshi da sauri ta janye idonta dan kasa jure kallonshi tayi saima kirjinta data fara bugawa danji tayi zata kware abincin ya tsaya mata a kirji da sauri yadau bottle water ya bude marfin yamika mata, karba tayi da sauri tasha kadan hakan yasa ya mika hannu ya karba yana kallon fuskarta tareda karban takeaway from her ahankali yace "ya sunanki" yay maganan yana debo fried rice din a spoon yakai bakinta.

IN BANI
_M.

Shakur_
8....

Kara zaro idanunta tayi duka tana kallonshi tana wani irin kallon abincin daya kawo bakinta yanajira tabude yasamata aciki, dan lumshe ido yayi yabudesu ahankali ya sake daurasu akan white oily eyes dinta, cikin wani irin dense voice yace "open your mouth Jewel" ja baya tafarayi akan gadon arude yana binta rike da spoon din harsaida takai bangon gadon tafashe da kuka tana kare fuskarta da hannu, ahankali ya zauna kusa da ita ya mika hanunshi yakama hanun datake kare fuskan dashi yakai spoon din mouth dinta yana wani irin kallonta batare dayay magana ba, da sauri ta bude bakin yasaka mata rice din ta karba zata fizge hanunta yakara rikewa gam gam, ahaka yacigaba da bata abincin hartaci kusan 5 spoons sanan ta kauda kai tace "na..na koshi" rufe abincin yayi ya ijiye a inda yake yadau bottle water yabata, ahankali ta karba tasha kadan tabashi ya karba ya ijiye yana kallon yanda gefen bakinta ya baci da oil din food din, hanunshi ya zira a aljihu yaciro clean white handkerchief dinshi mai taushi da kamshi yakai saitin bakinta yana wani irin kallonta, arude ta yunkura zata koma baya da sauri yasa hanunshi yakama waist dinta yana wani irin kallonta, kwalalo ido tayi tana wani irin kallonshi adaburce kaman wacce ke shirin suma, ahankali batare daya yanke eye contact dinsu ba ya daura handkerchief din gefen bakinta yana share mata ahankali harya gama yana kallon kwayar idanunta, zare handkerchief din yayi batare daya saketa ba yana rike da ita har lokacin yace "what's your name Jewel?" kulle idanuwanta tayi da sauri dan bazata iya jure kallon dayake mataba, ita tunda take bata taba ganin namiji mai eyes irin nashiba, yatsarshi yadaura kan nose dinta yana kallon long eyelash dinta yace "what's your name Jewel?" wani irin nishi tayi dan sosai yatsarshi ke mata wani irin sanyi a hanci hakan yasa tasaki wani irin ajiyan zuciya tace "Amatullah" murmushi yayi sosai dayawani irin karamai kyau maidan sauti hakan yasa ta bude idanunta, kallonta yasakeyi yace "your name is very cute just like you Ama" sake ware idanunta tayi ta kalleshi adan tsorace, gyadamata kai yayi yace "yes, you're beautiful Jewel" saukar da idanunta tayi kasa da sauri hakan yasa ya sanya hannu yakama habarta ya daga fuskarta ta fuskance shi, sosai zuciyarta ke neman dena aiki sabida yanda yake kallonta, da sauri ta sanya hanunta tana tura nashi daya rike mata habanta dashi muryanta na rawa sosai tace "s...stop touching me" da sauri yace "why?" tabe baki yayi yace "ba kyau ko?

In UK is a normal thing" shiru yayi yana kallon yanda har lokacin hawaye ke fita daga idanunta and he could feel yanda jikinta ko'ina yake rawa sabida riketan dayayi ahankali yace "kinaso na sakeki?" da sauri ta dagamai kai batare data kalleshi ba, dan murmushi yayi yace "okay to stop crying and listen to me, I wanna talk to you, inba hakaba I will hold and touch you again" da sauri ta sanya hannu ta share hawayen nata tass tadan kalleshi irin kallon nan na antursasani ne, ahankali yajanye hanunshi daga waist dinta ya saki habarta yadan koma baya da ita kadan dan yasan inhar yana kusa da ita he will touch her again and yanaso he wants her to be comfortable, gyara zama yayi ya kalleta murya chan kasa yace "Amatullah" da sauri ta dago kai ta kalleshi dan sosai yanda ta kira sunan ya daki ranta danko kadan a gida ba'a saba kiranta da Amatullah a gidaba dan sunan Kaka ne, babu wanda ya isa yakirata da sunan.

"where are you coming from, tayaya kikai drowning?

Kinje Beach ne?" shiru tayi tana kallonshi kafin cikin siriruwar muryanta tace "bikin Anty Ayush" da sauri yace "who's Anty Ayush?" ahankali batare data kalleshi tace "My sister" "aruwa kuke bikin?" gyadamai kai tayi tace "yes d husband is navy a jirgin ruwa suke party" da sauri yace "to tayaya kika fada ruwa basu ciroki ba?" cikin wani irin muryan kuka tace "jiri" da sauri yace "jiri kika dinga gani?" gyadamai kai tayi batare datai magana ba, shima shiru yayi yana kallonta, dan dago kai tayi ta kalleshi suka hada ido da sauri ta saukar da kanta tana share hawayen daya zubomata tace "I thought na mutu ma" murmushi yayi yace "no, I was the hero, I saved u Jewel, am your superman Jewel" batare data kalleshi ba tace "my name is not Jewel stop calling me that" murmushi yayi maidan sauri yakamo hanunta yace "you're my Jewel, I found you a water, and bazan barki ba Jewel, I just li..." hawayen dayaga tana sharewa yasa yadanyi shiru yana kallonta, dago kai tayi ta kalleshi adan tsorace ahankali tace "zan kira Mama na" dan yatsine fuska yayi kaman wani karamin yaro yace "I don't want them to come and carry you now Jewel" duka hannayenta tadaura kan fuskarta tana share hawayen dake zubo mata sosai wanan wani irin mutum ne haka, wani asibiti ne wanan, tasan su Anty Lami da Ayush kowama ana chan ana neman ta, tasan hala yanzu ma har an kira su Baba da Mama harma Kaka duk an sanar dasu ta bace, hanunta taji yakamo ya matsa.
Chapter 9 · 0% Book details