Sashe 14
In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bazanyi barci ba zan jiraka" hararanta yayi yajuya zai fita hanunshi da damke tace "dan ubanka saika bani danma ina lallabaka" kaman zaiyi kuka ya kalli yanda ta damke well ironed uniform dinshi yace "naji inna dawo zanbaki, ki saken to" sakinshi tayi tana dariya ta dungure mai kai tace "ja'iri barima ubanku yadawo yau zan mishi maganan aurenka ne, wlh koka fito da mata kona je kauye nahadaka dayar aminiyata Iyami" tsaki yayi tsabagen takaici baima tsaya yabata amsaba yawuce yafita daga sasan da sauri tabi bayanshi amma har yay wajen gate hakan yasa tai tsaki ta wuce part din su Hamida.
Da sallama ta shiga falon su Hamida tagani zaune a falon tanacin indomie data dafa da boiled egg tana kallon zee world tana ganin Kaka tai murmushi tana sunnar dakai, hararanta Kaka tayi tace "aikin kenan ki zauna ke kadai awuri babu kowa shine burinki a duniya miskilan banza, ni ina mamarki?" daidai lokacin Mama tafito daga kitchen rike da tray data debo wake dan gyarawa zatayi tana ganin Kaka tai murmushi tace "yau Umma a shashin mu" da sauri Kaka tace "eh nazo ne, kihada ma yarki kaya sasana zata dawo" turo baki Hamida tayi tana tauna abincin dake bakinta ahankali Kaka ta kalleta tace "ahap ai saidai ki mutu ingayamiki yarinya, yaushe zasu koma ma makarantan yama sunan hutun da sukaje?" murmushi Mama tayi tana karasa shigowa cikin falon tace "mid semester break" da sauri Kaka tace "yauwa shi yaushe zaku koma ke?" tai maganan tana kallon Hamidan dakecin abincinta, dan turo baki tayi tace "ranan Monday" kwafa Kaka tayi tace "saura wanan karan ma ki kwaso zero zero a makarantan kaman na wanchan karan, wlh cema Sama'ila zanyi bazai kara kashemiki koda sule biyar a makarantan ba, aure zamu miki, inyaki kuma nida kaina zan aurar dake" da sauri ta kalli Kaka, gyada mata kai tayi tace "eh kinjini da kyau, wlh aure zansa amiki inhar wanan karan ma kin fadi kaman wanchan tunda kedai bazaki saki ranki ki jona mutane kikoyi abuba, ba nannan zainaba ke zuwa makaranta karatu ba banda ke, malami na koya muku abu kina kakkare fuska kikasa kallon allo, yoto menene amfani Sama'ila yay ta bata kudi akanki har shekara hudu?
Kema kinsan naso keda Zainab da Ayush dakuna gama sakandire a aurar daku amma kuma sainazo na hakura da Sama'ila ya nunamin yanaso kuyi karatu amma kam wanan karan bala'i zanyi dashi dan wlh bazan bari dan kudin dayake samu a saida kaji, saida kajifa jama'a yazo yana batasu akanki ba, dan asarace, da'ace nine yabama uban kudaden danasan menayi dashi kuma Allah kaimu mondan, ni nan dakaina zan kaiki har Bayeron incema malamin ku wlh yazane min ke tunda dai kinki maida hankali kiyi karatu" tai shiru tana kallon Hamidan data daura hannu a fuska tana share hawaye, tsaki tayi ta kalli Mama data zauna kan kujera tafara gyaran wakenta ita yanzu bala'in Kaka baya damunta dan tsufa ce yamata yawa, cikin masifa tace "ai cewa nayi kibar gyaran waken nan kitasa keyanta taje dakinsu ta ciro kayanta daga sip dinsu, na Zainab da Ihsan kawai zaku bari a sip din ta tattaro tadawo Sasa na, nariga na share dakin dazan bata tastas, Allah kuma yakaimu Monday zakiga nizan kaiki makarantan na rantse miki saina sa malamin ajinku yamiki bulala goma hala hakan zaisa kifara karatu, kici jarabawa da kyau, kigafa tunda sukai hutun nan banga tabude littafiba fa, kullum tana nanike adakin su daga taci saita bacci sai shegen bacci kaman kaza, ki ajiye kwanon wanan tsutsan kampanin duksu kesaki bakida kyan gani, yarinya taci tuwon dawa da miyan kalkashi abinci mai Gina jiki bazata ciba sai tsutsan kampani" murmushi Mama tayi tace "Kaka indomie ce ba tsutsan kampani ba" cikin daga murya kaman zata fasa gidan tace "injiwa Haleematu" ta nuna plate din tace "ke bakiga yanda abin take a lankwashe ba, wani irin ziza ziza da ita, tsutsa ce saisu busar saisu barbadeta da fulawa fa asaka a leda a sayar" ta kalli Hamida dake share kwalla tana tauna indomie bakinta ahankali tace "ba dake nakeba dan gidanku, tashi kije mamar ki ta tayaki hada tulin kayan ki, dama gobe su Zainaba zasu dawo sa sami sarari adakin suma" tashi tayi ahankali tai hanyar corridor inda dakinsu yake, ajiye waken Mama tayi ta tashi tabita tana murmushi kasa kasa Kaka tabisu da harara kafin takarasa tadau plate din indomie tafice dashi tana hararan abincin takarasa wajen bolansu zubar da indomie tayi sanan ta wuce chan pampo ta ijiye kwanon ta wuce Sasan ta.
IN BANI
_Maman Abd Shakur_
12....
Tashi Abie yayi yadauko maganin shi da yawancin inya fara surutai haka shi ake bashi ya dauko da sauri yadawo kan gadon ya dagoshi yana mikama Mami maganin yace "tashi kasha to saimuje wajen She" gyadama Abie kai yayi yana kuka ahankali yana yatsine fuska, zuba maganin Mami tayi ta mikamai ahankali yabude baki ya shanye maganin da kyar kullum yake yarda yasha amma yau yasha da kanshi, yanasha ko two minutes baiyiba bacci yay gaba dashi, gyaramai kwanciya Abie yay da kyar yaja bargo ya lullubeshi ya tofamai addu'a yajuyo ya kalli Mami dake share kwallan dake xubo mata, tasowa yayi ahankali yadawo bakin gadon kusada ita hanunshi yasa ya rungumota batare dayay magana ba, ahankali ta saukar da kanta kan kafadarshi wasu sababbin hawayen na gangaro mata kumatu tace "Abie why this?
Why we?
Why our Son?
Shekaru talatin da biyu kenan muke fama, Abie please kafadamin what else dazanyi da yaronmu zai sami lafiya, banda burin daya wuce nabude idanuna naga Aadil kaman kowani namiji aduniyan nan, kaman dan uwanshi, Abieee" taja sunanshi cikin kuka, kiss yama forehead dinta yanadan shafa bayanta shima idanunshi sunyi ja, zaiyi magana wayarshi dake aljihun jallabiyar shi ta shiga ringing, riketa yay da hannu daya yasa hannunshi a aljihu ya ciro wayar yana kallon screen din, dan juyowa yayi ya kalleta yace "Baba ne" da sauri ta share hawayen datake yi tana mishi alamu daya dauka, daukan wayar yayi cikeda girmamawa harda dan dukar dakai yace "barka da safiya Baba" daga tachan bangaren tsohon da akalla xaikai shekara 80 yace "da Abdullahi nake magana ko?" yay maganan a natse kuma dadaddaya kaman yanda tsofaffi ke magana, cikeda girmamawa yace "eh Baba nine" a natse yace "to, to, to Masha Allah, ya kuke?
Ya sana'ar taka tachan?" murmushi yayi yace "Alhamdulillah Baba, sana'ar munakan yi kuma ana samun riba daidai gwargwado" ahankali yace "masha Allah, Allah ya taimaka, Maryama fa?" murmushi yayi yace "gatanan Baba bari nabata wayan" ahankali yace "tsaya tukunna" cikeda girmamawa yace "to Baba" dan shiru yayi kafin ahankali yace "ina Hassan da Hussain?" kallon Mami yayi suka hada ido sanan ya maida hankalinshi kan wayan yace "Alhamdulillah suna lpy, Hussain na Nigeria yanzu haka yana Lagos ya...." cike da fada yace "Hussain na Nigeria shine baizo gidaba?
Abdullahi dagakai har Maryama inda kusan bazaku iya bama jikokina yan biyuna tarbiya mai kyau ba dakun banisu na rainesu sun girma sun taso anan wurina, amma yaro ace yana kasar iyayenshi munan bamamu da labari yana gari, kenan inda ban kirakaba da bazaka fadi mini ba" cikin kwantar da murya yace "kayakuri Bab..." da sauri yace "bannemi wanan daga gareku ba, yau kwanan shi nawa?" ahankali yace "kwanan shi tara Baba, wani assignment yajeyi a Lagos amma dama..." katseshi yayi ta hanyar kiran sunanshi.
"Abdullahi" da sauri cikeda girmamawa yace "na'am Babana" ahankali yace "kafadama Hussain yakamo hanya yazo kano yauyau dinan gidan kakanin shi banason naji wata magana, sai magana nabiyu dayasa na kira" yadanyi shiru yana hutawa, a natse yace "ina Hassan, yaya jikin nashi?" dan juyawa yayi ya kalli Aadil dake bacci har lokacin yace "Alhamdulillah Baba, jikin nashi da sauki" cikin dan kakkausar murya tsohon yakira sunanshi.
"Abdullahi" ahankali yace "na'am Baba" shiru yayi nawurin minti biyu kafin yace "kaima kasan nabaku lokaci mai tsawo, na tsaya sanan na zuba muku ido ina kallon ku dakai da Maryama, nasan ku nasan halinku na yaran zamani, sanan bankuma tauye muku hakkin ku ba a matsayin ku na iyayen yaraba, na barku babu kasashen duniyan nan dabaku zaga da Hassan ba tun yana dan mininin shi neman mishi magani, to kanajina?" da sauri yace" eh Baba ina jinka" cikin yar shakakkiyar muryanshi ta tsofaffi yace "masha Allah, abinda nakeso daku shine, ka tattaro yinaku yinaku ka kawomin jikana nan kano, ku kawomin shi nan kano afara mishi maganin gargajiya, zamu jaraba mugani abinda Allah zaiyi, bazan zuba muku ido ku karar min da rayuwan jikana a hanyar asibiti ba, burina shine ya warke namai aure naga tattaba kunnena kafin mai afkuwa ta afku wato mutuwa, ku kawomin jikokina Kano zan nema mishi magani da kaina, ku kawomin su, ku zaku iya komawa indanta Hassan ne zan daukomai babban nurse ko Nani dazai dinga kulanmin dashi" yay dan shiru yana Tari da sauri yace "sannu Baba" saida tarin ya lafa sanan yace "kuyi shirye shiryen dazakuyi, ku kwasan mai duk wani abu dayake so gudun karya muku kuka a jirgi inya gaji da zama, ku hada komi kutaho Nigeria gobe, kufadima Hussain ina jiranshi shikuma yauyau dinan" ahankali yace "to Baba" "yauwa ka gaidamin da Maryama" "to Baba zataji" ahankali yace "Allah yamuku albarka dukan ku, Allah yabama Hassan lafiya, Allah ya kiyaye hanya yakawoku lafiya" da sauri yace "Ameen Baba" "yauwa to, nabarku lafiya" ya katse wayan.