← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 69

Sashe 31

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kafin mahaifiyarshi ta rasu, akwai lokaci ta tattaro yinata yinata ta dawo birni gidanshi da zama tareda wani marayan yaron makwabcinta a kauye mai suna Abdullahi (Abie), Abdallahi yarone mai natsuwa da hankali wanda akalla zai girmi babban dan Baffa Suleman da shekara daya ko biyu.

Tunda tadawo gidan da zama da Abdullahi ta damkama Baffa shi tacemai tanaso yarikeshi amatsayin danshi, gashinan amana, iyayen shi sun rasu, karya bambamtashi dasu Sulemanu, tabashi shine sabida koda tafadi ta mutu tasan yana hanunshi da zama, Baffa baimata musu ko jayayya ba ya karbi yaron dan yaron badai natsuwaba, nan Suleman da Abdullahi suka shaku suka zama abokan juna suna zuwa makaranta tare both boko da islamiyya dudda sun fishi aji.

Bayan wasu yan shekaru sun gama makaranta alokacin Baffa kuma yanso yay retire saiya daura Suleman baban daddanshi shugaban kampanin shi duka ukun, yasa sauran yaranshi maza biyu da Abdullahi duk a kampanin yabasu office suna aiki ana biyan su duk karshen wata makudan kudi, abin bakaramin ciwo yama Abdullahi ba yaso ace shine zai Baffa yabama shugaban kampanin dan yafi Suleman kai a business, banda haka yanada mugun sha'awan yaganshi yazama shugaban kampani, hakanan ya tattara ya watsar da zancen amma abin na nan ranshi ras duk idan yatuna har kuka yakeyi a boye yace wato sabida shi ba danshi bane saisa baibashi shugaban kampanin shiba ko bakomi shima zaiyi kudi wataran, ana haka wani irin soyayya ya kullu tsakanin Abdullahi da Mami bana wasaba, Allah ya dauramai wani irin soyayyan Mami bana wasaba.

Akwai ranan da Baffa yay order wasu hadaddun motoci toyota camry alokacin ana yayyin su yabama duka yaran nashi daidai as end of the year prayer gift amma banda Abdullahi yacemai shi tashi bata isoba, kuma harga Allah bata iso bane dan Baffa yaso yay surprising dinshi ne yatabaji yana hira da Suleman yacema Suleman shi yanason babban mota arayuwan shi jeep na burgeshi hakan yasa Baffa yaso yay surprising nashi kodan jarumtar shi a kampani yabashi shi jeep amma sai tashi bata isoba dan ba'a gama yima motar custom duty ba harsai next week, nan fa bayan komi yadan lafa Abdallahi yasaci hanya yafita daga gidan yatafi kampanin su yadinga kuka yanajin bakin ciki sosai yana zagin rashin kudi da zama a karkashin wasu, dafashi yaji anyi da sauri yadago kanshi wani inyamurin gateman dinsu ne yagani yana sanye da hadadden suit baki, murmushi yamai yace "kasoma gane basu sonka ko Sir?

Kawai amfani suke da talent dinka suna making money a kampanin nan" da sauri ya kalleshi yace "ya akayi ka sani?" murmushi yayi ya kalli ko ina na wurin kafin yaciro wata yar Kati daga aljihun wandonshi ya mikamai yace "inhar kanaso yau yau dinan rayuwarka ta chanza from this poor man dakekeci a gindin wasu kana musu boyi boyi kaima kai kudin bala'i, kudin da sunema zasu rokeka, inhar kanason money and fame, kanason dukiya, kanaso kafada aji kahana ahanu, kanaso kadawo yaro mai gari a hannu to ka kira number nan da kagani ajikin katin nan, Ozo zai biyama bukataun ka, zakai kudin ban mamaki, kudin dasu kansu saisun koma suna rokon ka kudi.
_Manage this guys, nai typing duka ya goge, da kyar na iya nai wanan yanzun nan, gobe kuna bina bashin daya in sha Allah_.

IN BANI
Maman Abd Shakur
27....
_Cigaban labari_
Baki yasaki yana kallon gateman cikeda mamaki yama kasa cewa uppan, murmushi gateman yayi yace "kaga tafiyata dama resignation letter na nazo nabasu kai baka ganni ba level don change, nima wani yamin hanya wanan harkan, dazaran ka shirya kaima kawai kiran number kadai zakayi, nina gayama har gidana zakazo kamin godiya sabida gatan danama, sai anjima" yawuce yay gaba yana wani irin tafiya irin na masu kudi dinan Abie yabishi da kallo kasa tashi yay daga wurin sai kallon katin yake yana jujjuyawa har aka kira sallan magrib yatashi yaje yayi yajira har akai isha'i yayi daganan yakoma gida ranan kasa baccin dare yayi sai tunane tunane yakeyi yakira ko kar yakira, shidai harga Allah yanason yyi kudin nan kodan yanuna Baffa baidamu da kudin suba hasalima saidai su sudinga begging nashi, har gari yawaye yatafi masallaci baibar tunane tunane va, arana na uku ne ya yanke shawara zai kiradai kodan yaga me gateman kecewa idan ma karyane yagano, Motar gida daya sabaja yadauka yafita daga gidan ya gangara chan wajen gari yay parking motarshi ya kashe sanan yaciro wayarshi yadau katin ya kwafe number jiki yay dailing number, ringing daya wayan yayi kawai saiyaga wani irin duhu a idanunshi daganan kuma bai karasanin inda kanshi yakeba yadai farka yaganshi a wani jan daki yana sanye da jan riga akwance akasa, saiga wasu mutane sun zagayeshi daga cikinsu harda gateman suna rike da jajayen candle dake ci da wuta suna wasu irin wake wake suna zagayeshi, kasa koda motsin kirki yayi tsabagen yanda jikinshi yahau rawa yamugun tsorata kaman daga sama yaji ankira sunanshi.

"Abdullahi yakira Ozo, Ozo ya amsa mishi saki jikinka kafada ma Ozo mekake so" tashi yayi zaune daga kwanciyan ya kankame jikinshi ko ina na jikinshi narawa sosai yama kasa daga kai ya kalli kowa hanunshi nawani irin rawa jikinshi na kakkaurwa yace "dan Allah kuyakuri dama inaso nayi kudine amma yanzu nafasa, banison kudin tsafi dan Allah kumaidani gida" wani irin dariya akayi kaman zai fasa dakin saikuma akai wani irin nishi kaman na zaki.

"ba'a kira mana Allah anan ka kiyaye, dazaran mutum yakirani babu gudu babu komawa baya ka shiga ka shiga ne baka isa kafita ba, inda kasan bakaso da tun aranan ka yarda katin baka kiramu ba" hanunshi yakai baki jikinshi narawa sosai yace "natuba, natuba, ayakuri, amin afuwa, wlh banison kudin tsafi" wani irin dariya akayi dake kama da tsawa akace "nine Ozo duk wanda yakira ni yanemi sanan yace yafasa to motar nan dakasan ka kirani aciki, anan yan uwanka suzo su dauki gawanka tsotse jinin ka zamuyi tsaf dama ga jininka nan mai karni ne jinin virgin, daman irin wanda nake nema kenan jinin musulmi virgin" abun dayaji yana zuba daga ka sanshi yasa yabude ido da kyau yaga ashe fitsari yake, "Abdullahi" a firgice yadago kanshi yace "na...na'am" dawata irin murya kaman nayar jaririya yaji ance "step forward" gabaki daya organ din jikinshi karkadawa suke yay nadaman dailing number dayayi ahankali yamike tsaye kafarshi bankarewa sukeyi tsabagen tsoron dayake ciki yana tafiya kaman wani kwashoko yay gaban dakin yakasa daga kanshi haryakai gaban dakin da candles kenan dayawa da gumaka kanshi akasa.

"ka daga kanka" yaji anfadi cikin wani irin kakkausar murya da sauri yadaga kanshi wani kwarangwal yagani agabanshi yamikomai wata yar karaman kwarya da abu keciki ja kaman jini, ihu yayi zaikoma baya yaji kafafunshi sunkasa motsi kaman yataka gum, yafashe da kuka cikin wata irin murya mai echo yaji ance "karba kasha" kasa mika hanunshi yayi tsabagen tsoron kwarangwal din mai jajayen idanu, hanunshi yaji ana kaiwa saitin karyan yadaiga ya karbi kwaryan amma baisan tayaya ba yadaiga hanunshi ya amshi kwaryan yakai bakinshi wani irin yatsine fuska yayi yanajin wani iri amai natasomai haka yaga abun kaman ana controlling dinshi yabude baki da kyar yafara shan jinin hawaye nafita daga idanunshi, ahaka ya shanye na kwaryan tass, wani irin sanyi yaji cikin jikinshi tundaga yatsarshi har cikin kwakwalwanshi kafin idanunshi suyi wani irin ja yazaro su saikuma sukadawo farare, dariya dakin yadauka sauran mutanen sukace "welcome to the family, money and fame duka nakane ayanzu" shiru sukayi sabida wani hadadden zobe da kwarangwal din yadauko yakawo saitin hanunshi, ahankali yamikamai hanunshi yanajin wani irin farin ciki yasakamai ring din jikinshi yay wani irin kara saikuma yadawo daidai, daga sama yaji magana.

"welcome to the family Tursoso, kudi saidai idan kaine kace sun isheka, Ga zoban kanan koda yaushe ka bukata zai maka aman kudi, wanan cult din mai adalci ne babu bukatan wani abu babba kuma bamu tsanan tawa kasani cewa duk randa ka haifi d'a namiji, danka nafarko namune, namune, namune " nan yace ya yarda haka yakoma gida ya shiga dakinshi ya kulle ya xauna akan gado yanaso ya gwada ya kalli zoben yatsar tashi yace" kudi", ko gama ambata baiyiba zoben yafaramai aman kudi dahar saida yaji tsoro ya tsugunna yana tumurmusan kudin yana ihu yana murna yana mamaki yanzu wanan duka kudin shine, nan ya tatatra kudin yazuba a ghana masgo kusan biyu ya cika yafara tunanin karyan dazai shigo yafadi cewa ya sami wani aiki ne, wani paper ne yaga an wurgo akanshi da sauri ya chabe yaga job offer letter ne nawani kampanin sport cars ihu yay najin dadi yace thank you Ozo the great one, washe gari ya nunama Baffa sosai duka yan gidan sukaji dadi nan Baffa yace tunda hakanr za'aska ranan bikin shi da Mami kafin yatafi haka aka saka wata biyu yatafi UK abinshi yana fanchakala da kudi yabude wani durmemen kampanin motoci inda har kira motoci akeyi aikuwa fame yasamu dan kusan kowa na UK din saida ya sanshi lokacin bikin shi yakoma ya auro Mami yadawo suna zama na soyayya dan sosai Yakesan Mami yanadai ta addu'a kartasami ciki, bayan shekara daya.
Chapter 31 · 0% Book details