← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 69

Sashe 38

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ja'irar yarinya tatafi bata dawoba sun barni nikadai naketa aiki, ai wlh duk kudin dazasu kawo gobe sisi bazasu ciba nikadai nasha wahalata nizan mori kudina, Hamida tasami gidan hutu miji pagal kaman ita chan su karata sa warkar da juna" tai maganan tana tura kujeran falon ta jikin bango ta tsaya tana kallo yanda dakin yay kyau sosai tace "masha Allah komi yay tsaf tsaf, sun gogu kujerun jibi yanda suke kyalli gobe dazaran sunzo shashina zan kawosu darat ayi magana in yanke musu sadaki, sati hudu zan saka biki, babu kyau jan biki yay tsawo ga yaro ma ba lafiya, yar buzuwa ma kudin ta rabi zan bata sai bayan biki zan cika mata rabin, wayyo Allah na bayana" tai ihu tana kokarin zama akan kujera dan tagaji iya gajiya, ko minti biyu batayi da zama ba bacci yay awon gaba da ita.

IN BANI
Maman Abd Shakur
34 - 35
_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi pay anan or pay achan_
_in kinason novel dinan zaki turo 300 acess fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_
_you can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461 for those da basu da account sainai adding dinki a group din danake posting kullum_
Da asuban fari Kaka ta tashi tana mitsike ido tana salatin annabi ta wuce bandaki tayo abunda zatayi tafito daure da alwala tadau charbin ta tasaka hijabi tahau kan sallaya ta kabbarta salla, saida gari yay haske sanan ta sallame ta ijiye hijabin kan kujera tafito tabude kofar sasan ta tafita tai dayan sasan indata tarar da Hamida da Zainab suna sharan compound din, Hamida ce tafara gaisheta tana murmushi tana sunnar dakai.

"ina kwana Kaka" ballamata harara Kaka tayi tace "rike gaisuwar ki munafika" dariya Zainab tayi itama tace "ina kwana Kaka" kallon Zainab din Kaka tayi yanda takema Hamida dariya tana washe baki tace "ke dalla chan rufe mana wanan bakin mai kama da rubabben shadda" wani irin ware manyan idanunta Hamida tayi kaman ba itaba tawani irin fashe da dariya tana kallon Zainab din tana yatsine hanci tace "hmmm saisa naji wari" wani irin gudu Zainab din tayi tabita, da gudu Hamida ta saki tsintsiyar akasa tana ihu tana dariya tana kwalama Mama kira Kaka tace "Allah ya wurgo ubanku gidan yaga abinda kukemai kulllum agida inya tafi masallaci" tasakai ta shige falon tana Kwalama Mama kira, fitowa Mama tayi daga dakinta rike da charbi tace "ina kwana Umma" daure fuska Kaka tayi ita a dole fushi take tace "lau, ba gaisuwar ki nazo najiba nazone nafada miki ki kira Lami tazo ita da mijinta, sanan kuyi hadadden girki, baki zanyi da sassafen nan, girki mai rai da lafiya fa" ahankali tace "to Umma" juyawa tayi zata fita saikuma tajuyo tace "ina Ihsan banganta ba?" "tana daki ne, tari take da mura shine nace kartai sharan" "maganin shan ruwan sanyi, babu randa bana wakar subar shan ruwan sanyi amma saisu nuna nai kadan, anjima tazo ta amshi zuma da tafarnuwa awajena tasha zatasami sauki, tarin zai lafa" ahankali Mama tace "to Umma angode" yaye labulen tayi tafice daidai Baba na bude gate yana shigowa sanye da farin jallabiya da hula akanshi da sauri su Hamida suka gaidashi amsasu yayi da sauri ganin Kaka yasa yataho dadan saurin shi yasamu ya lallabata, shan mur Kaka tayi ta dauke kai kaman bata ganshi ba tai hanyar Sasan ta, da sauri ya cin mata yasha gabanta cikeda damuwa kaman zai mata kuka yace "haba Umma inata gaidake kinki amsani wai har yanzu baki huce ba eh?" hararanshi tayi tace "gafara kabani sasana zan shiga ko" matsawa yayi hakan yasa tabude kofa ta shiga yabi bayanta da sauri ta shiga falo ta zauna akan kujera da sauri ya zauna kusa da ita ya daura kanshi akan kafarta ko kadan ya tsani yaga Kaka na bata rai dudda yasan ba'a mata komai kawai itake kirkiro rigima da kanta amma baya taba barinta ta dinga fushi for long, ta riga ta tsufa d fact dat she's very strong bai zama guarantee na cewa wani ciwon bazai kamata ba saisa yake lallabata dan yawan fushi zai iya jawo mata hawan jini ko ciwon zuciya, ahankali yace "kiyakuri Umma na bazan kara ja dakome zaki ceba, kowani hukunci zaki yanke kinyi daidai bazan kara cewa wani abuba Umma kinji" sosai zuciyarta yay sanyi amma saita daure tace "kai alkawari bazaka kara ja da hukunci naba?" da sauri ya daga kanshi jintamai magana yace "eh Umma kome kikafada daga yanzu hakan take kuma haka za'a bita bazan kara cewa wani abuba" kallonshi tayi saikuma ta kece da kuka taja bakin zaninta ta daura akan fuskanta tana share hawaye, arude yace "dan girman Allah Umma kidena kuka, wlh, wlh, wlh Umma kinji na rantse miki bazan kara, bazan kara ja da maganan kiba ke zaki dinga yanke hukuncin komi daga yanxu" cikin kuka sosai tace "baka sona ka tsaneni Sama'ila gani kake takurama nakeyi dankaga kai kadan karagemin aduniya baban Faruku mai sona maijin maganata ya rasu, wayyo Allah na, kaduba fa da baki daya nacemai yasaki shegiyar matar nan nashi Maman Faruku ya saketa amma kaiko kullum nunamin kake ban isa dakaiba, banjin dadinka ko kadan, agaban matarka, yayanka, kai agaban duk duniya ma kake nunawa niba komi bace agareka ba, nasan inda ace kasan guban dazaka sakamin a abinci naci namutu da tuni kasamin naci na mutu danka gaji da wahalata da matsalata so kake ka huta" "innalillahi wa innailaihi raji'un Umma, Umma dan yarasullullahi kiyakuri wlh bazan taba iya kashe uwata ba uwardata haifeni ba" tadan hujin yatsun data daura akan fuskarta take kallonshi yanda taga yay kaman zaiyi kuka dukya tsure yasa tai wani irin murmushi jin dadi aranta dan tasan ko yaji abinda ta aikata anjima bazaice kalaba sabida fargaban karta sake irin abin nan, share hawayen tayi tass tass tai tagumi tai shiru tana kallon sama kaman wacce akama rasuwa, ahankali yace "Umma, Ummana dan Allah ki kalleni" kallonshi tayi sai shar saiga hawaye, rudewa yayi gwanin ban tausayi yatashi tsaye daga kan kujeran yasa hannu a aljihu yaciro yan bandir din dari biyar biyar da wani makocinshi yanzun nan bayan sallan asuba yabiyashi kudin kaji guda dari daya saya, yadaura mata kudin acinya yace "gashi Umma sukenan gareni yau, nabaki kome zakiyi dasu kiyi amma dan Allah kiyakuri kinji" washe baki tayi kaman ba itace tagama kukan ba tadaga kudin tana kallo tace "kai Sama'ila wayan nan sababbin kudaden fa nawane?" "dubu dari da hamsin ne" murmushi tayi sosai tace "a'a baza ai hakaba, bandai dubu hamsin din saman kaika rike darin ko, Allah ampana" tai maganan tana kwance robalin ta kirgo dubu hamsin ta cire ta tura a lalita sanan ta mikamai sauran tana murmushi tace "Allah shi maka albarka, Allah karo kasuwa agidan kaji, Allah ya tsaremin kai yakaremin kai daga shairin mahassada kaji Sama'ila Sama'iloli yaci kafan bunsuru yahana Kaka bacci" murmushi yayi sosai aranshi yace Umma da son kudi yarasa uban me zatai da kudi haka hatta lipton shiyake kawomata ko tsinke bata siyafa amma sai masifar son kudi, "kanajina" da sauri ya kalleta tace "yau bazaka fita gidan kaji da wuri ba zamuyi manya manyan baki ne" da sauri yace "su waye Umma?" dariya tayi tana ballan goro tace "in sukazo zaka gansu, ka kira Mijin Lami yazo dakuma limamin unguwa, sanan kayoma Haleematu cefane nace ta girka haddden abinci wanda zamu tarbi bakin dashi, ka siyo lemukan kwali kaji" ahankali yana kallonta yace "to Umma shikenan" murmushi tayi sosai tana washe baki tace "yauwa dan albarka na, tashi katafi tun jiya banga Faruku ba baizo yasha furan shiba shegen goran" dariya yadanyi yace "kina kewan abokin fadan nakine kenan anjiman nan nasan zaizo wurinki" dariya Kaka tayi tace "wanan shegen goran ne zanyi wani kewan shi Allah kyauta, nidai yi sauri kaje kayi abubuwan dana saka" to yace yafice yanama kiran Abban Ra'is sukace suna hanya dan Mama takira, anty Lami na zuwa itada Mama da yaran su Hamida da Zainab suka fara girkin bakin Kakan, sukuma su Abba suna falo suna hira, wuraren tara da rabi suka gama komi Kaka dataci gayu cikin wani lashin hadari lace best lace dinta kenan tunna aurenta ne, bata saka lace dinan sai occasionally, tashigo kitchen din sai albarka take samusu, bakaramin Mamaki sukayi ba ganin kaka da kayan dan sunsan sai akwai babban abu take sawa, Zainab data gimtse dariyan ta tace "Kaka wlh hadari lace dinan baya miki kyau" dudda ta mata abaya Hamida ta sunnar dakai tana murmushi, Kaka tace "dan ubanki lashin nan ya girmi ubanki, tunna akwatina shegiya yar baka rubabbiyan yarinya kawai" turo baki Zainab tayi tawuce ciki Hamida tabi bayanta sum sum Kaka tabita da kallo.

Kujera taja ta zauna a tsakar gidan, Allah Allah take suzo so kawai take dazaran taji sallama ta shigo dasu, wani almajiri karami ne yabude gate ya shigo da sauri ta tashi tace "kai baki suka aiko ka?" da sauri yace "a'a Hajiya sadakan biyar ko goma nasai omon wanki" wani irin dogon tsaki taja takoma ta zauna sanan ta chusa hannu a lalita tace "zo ungo" tamikamai naira hamsin karba yayi yanata mata addu'a sanan yajuya yafita daga gidan, ba'a wani jimaba wani yaro ya shigo shiru tayi tabuga tagumi batason tasa ranta awanan karan.

"Salama Alaykum wai ance ana sallama da masu gidan" da sauri Kaka ta mike tana murmushi sosai ta kwalama Abba kira.

"Sama'ila, Sama'ila kufito ku shigomin dasu" fitowa Abba da Abban Ra'is sukayi da sauri Kaka ta nuna musu gate tace "kuna bata musu lokaci tun dazufa sukazo, shashina zaku kawosu" tawuce shashinta sukuma su Abba sukai gate wondering who could bakin Kaka be, bakaramin mamaki sukayiba dasukaga mutanen jiyaba amma duk suka boye mamakin nasu suka gaisa sosai cikin mutunci sanan sukai musu iso.
Chapter 38 · 0% Book details