← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 69

Sashe 58

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai bayan ta idar da isha sanan tai shafa'i da wuturi ta tashi daga kan dadduma ta linke ta tube kayan jikinta ta linkesu dan basuyi dattiba ta maida wardrobe taciro rigan baccin dazata saka ta ijiye akan gadon tana tunanin Aadil, bathroom tabude ta shiga ahankali tana share kwallan daya zubomata, brush tafarayi sanan taja shower cap tasaka sanan tafara wanka da ruwan zafi sosau, tadan dade tana wankan sanan tafito tadau towel pink tadaura daya kusan kaimata guwiwa ta daura ta zare shower cap din daga kanta ta ijiye tana kallon fuskarta, share hawayen dasuka zubomata tayi danko kadan jitakeyi bataso tafita daga bathroom din batare dataga Aadil ba azaune kan gado yana washe mata baki ba, lallasan kanta tayi kafin tajuya tana tafiya kaman wacce kwai yafashewa aciki ta murda door handle tabude kofa tafito daga bathroom din tai gaban mirror ta tsaya tana tsane fuskarta da towel din, karan dataji na faduwan abu kwan yasa ta juya ta kalli kasa dan tasan bata taba komiba tome yafadi, zoben dazu tagani akasan dakin harzata dauke kai saitaga kaman zoben yakara girma fiye da dazu da sauri tasake kallon zoben tana ware manyan idanunta, gani tayi zoben yay girma kaman anhuramai iska da sauri ta dafe kirji tace "innalillahi wa innailaihi raji'un" kaman daga sama taga kwalliyan dake gaban zoben yakara girma saitaga ya dare yarabe biyu yabude baki yay katoo sosai, wani karamin paper tagani yafito daga bakin zoben yafadi akasan dakin saitaga paper yay wani irin girma shima taga yakoma kudi dubu daya sabuwa dal, wani irin faduwa gabanta yayi jikinta yafara rawa bakinta yafara rawa tana kokarin furta addu'a takasa, gani tayi bakin zoben yafara fiffito da kananun papers din dayawa suna zuba akasan dakin suna komawa yan 1, 1k note sababbi dal dal, wani irin ihu tabuga afirgice.

"Mamaaaa!" tai wurin kofa da mugun gudu tabude kofan tafita kaman wacce ta zare tana ihu.

"Mamaaa, Mamaa" ta kwalama Maman su kira ta kwasa da mugun gudu tai hanyar gate ta runtse idanunta gam dan zoben take gani a idanunta yana aman kudi zoben aljanu, bude gate tayi tafita dawani irin azababben gudu daidai kan wata mota Lexus ta danno yana shirin horn azo abudemai gate, ganin fuskar dabazai taba mantawa ba ko amafarki daure da towel kafafunta ba takalmi idanunta akulle dan gaban gidansu akwai manya manyan Street light bauuu sun haska ko ina yasa da sauri ya kashe motar yabude door yafito yana gyara zaman suit din jikinshi bude kofar gate dinsu yayi ganin babu kowa a compound yasa yawaiga da sauri ganin tana gudu yasa da sauri yabi bayanta, daidai tana shirin shiga titi yawani irin fizgo hanunta tadawo baya yariketa gam yana binta da kallo ganin idanunta a rufe ruf jikinta nawani irin rawa.

"Mama Mama, Mamaaaaa!

" tasake kwalama mamansu kira yasa ya jijjigata tareda kiran sunanta.

"Amatullah" ko kadan kwanyanta baya aiki a lokacin sai kiran Mama Mama mama take ta datse idanunta gam, da hannu daya yarike ta yacire black jacket din jikinshi dake kamshi sosai ya daura mata akan kafadarta ya jijjigata tareda kiran sunanta.

"Amatullah look, look, hey relax is me, open your eyes menene?" jin murya kaman ta Aadil sama sama yasa ahankali tabude idanunta dasuka kankance jikinta na rawa, Sanye yake da farin long-sleeve shirt wuyanshi daure da nicktie gashin kanshi a kwance yay wani irin mugun kyau yana rike da ita gam gam yana kallonta ganin ba lafiya tattare da ita, fashewa tayi da kuka sosai tafada jikinshi ta rungumeshi tace "My Aadil you are back" cirota yayi daga jikinshi da sauri fuskarshi adaure yace "where are you running off to daure da towel batakalmi ba hula are you okay" rikeshi tayi gam jikinta ya dauki ruwa tana kokarin sake shigewa jikinshi yahanata tace "som....something in...a..dakin" luuuu tayi baya zata sume da sauri yariketa ya dauketa yay hanyar gida da ita, bude gate yayi mai gadi yafito mugun kallo ya watsamai yace "bakasan aikin kabako how can be our security idan baka taking note of who goes in and out of this house eh?

Anyway banda time dinka call Mami for me kace ta taho da Dr" yay hanyar shashin su Hamida dauke da Hamidan, bude kofar dakin yayi wani hadadden kamshin turaren wuta yadaki hancinshi kwantar da ita yayi akan kujera yatashi yay hanyar dining dan daukan bottle water dayagani daidai lokacin Mami da big Mum dasu Baffa da Suleman suka shigo dan duk suna tare ana maganan Abie inda yakai Aadil Mai gadi yace suzo Hamida ba lafiya, da sauri Mami takaraso ciki da gudu tana kallon fuskar Hamidan tace "maiya sameta Aabid?

Kafafunta butu butu haka, wat happen son?" bude bottle water yayi yace "i don't know Mami dawowa na kenan naga tafito daga gate da gudu ahaka idanunta akulle i was trying to talk to her kuma saitai passing out" karban ruwan Mami tayi da sauri tana surutai.

"na shiga uku wai meke faruwa ne ni Maryama" shafa ruwan tayi a fuskarta wani irin ajiyan zuciya Hamida tayi tabude ido tana kallon duka dakin, ahankali Mami tace "Hamida na kinajina?" kallon Mami tayi saikuma tajuya tana kallon duka yan dakin kafin idanunta ya sauka kan Aabid dayay folding hand akirji yana kallonta tashi tayi azubure tafashe da kuka tafada jikin Aabid tace "take me out of this place kaji My Aadil akwai wani abu adakin chan, akwai wani abu yanata girma am scared ka kaini wurin Mama dam Allah ku kaini wurim Maman mu da Kaka" takire Aabid gam, da sauri Suleman yace "to kodai tanada aljanu ne?

" komawa bayan Aabid tayi tarikeshi gamgam jikinta narawa tace "abun na dakina chan bedroom pls take me out of here, zai fito yakamani i carried it dazu" tafashe da kuka sosai da sauri Mami ta tashi zatai magana Baffa yadaga mata hannu bayan yagama nazarin Hamidan yace "kubarta yarinya mai natsuwa haka dole akwai abinda ya firgitata bakuga bata hayyacinta ba, Sulemanu kumuje muduba dakin mugani" da sauri Suleman yace "to Baba" big Mum tace "ku dauko adduna incase maciji ne ko kunama" hararanta Baffa yayi yace "babu reptiles agidan nan ana fumigation ai" sukai hanyar dakin harda su Mami Aabid zai bisu tasake fashewa da kuka tana rikeshi tace "don't leave me kaji Aadil" juyowa yayi ya kalleta kafin ya dauke kai ganin she's not okay, ihun su Big Mum dayaji dakuma salatin su Baffa kowa nakiran sunayen Allah yasa da sauri yay hanyar bedroom din yana rike da hanun Hamidan gudun karta kara fita, kutasawa yayi ta tsakakanan su Big Mum dayaga jukunansu narawa duk suna kallon dakin ya kutsa kai ya shiga dakin, chak ya tsaya kyam jinin jikinshi ya tsaya kyam, ganin abinda tunda yake aduniya baitaba ganiba, wani katoton huge zobe yagani akasan dakin yana aman kudi yan dubu daidai sababbin kudi nafita daga bakin zoben, kudin sun cika kasan dakin har wasu sun soma hawa kan gadon sunyi himm, daidainan Abie ya buga kofan falo ya shigo dakin rai abace Aadil biye dashi.
_hello lovelies, due to high demand na next page am introducing VIP readers, in bakison suspense kinason kiji next page always koda yaushe all you need to do is subscribe for VIP and be my VIP readers, for those interested all you need to do is pay 1k, for more enquiry 07012181461, chat me up and know more.

I love you
51.....
_karki karanta in baki biyaba in kika karanta ina binki bashi pay anan or pay achan_
_Zaki tura 300 kota card kota bank sai nai adding dinki a group din danake posting, 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461, you can also send MTN card to watsapp number na 07012181461_
_masu fitarmin da book kuda Allah_
Hanyar bedroom Abie yayi ganin babu kowa afalon straight cikin fushi yana daga murya yace "ina take zoki barmin gidana, mai bakin jini, mai kashin tsiya daga auroki kindawo mana bala'i" Hamida dake baki bakin kofar bedroom dinne tafara juyowa jin hayaniya da sahun tafiyan mutane, tana ganin Abie tareda Aadil daya fara tsalle zaiyo kanta gabanta yawani irin mummunan fadi sabida wani mugun kallo da Abie yake mata kaman zai chaka mata wuka, batasan lokacin data rike hanun mutum din dataji kusada itaba, hanun big Mum takama tarike gam da
sauri big Mum ta juyo jin anrike mata hannu ganin Abie da Aadil da yarike gama yasa tace "Baban yan biyu yauwa zokaga ikon Allah" daidai lokacin Baffa daya gama kiran liman din masallaci dan d whole scene looks spiritual da jinnish ya kalli Suleman da Muhammadu dasuke kafe a tsaye suna ganin abinda basu tabaganiba aduniya yace "kuje ku shigo da liman koma menene wanan abin ayar Allah yau zata kona manashi" da sauri suka jujjuya suka fita daga dakin ganin Abie a corridor rike da Aadil dayake kokarin fizge kanshi yana kuka yasa sukace "jeka gani kaima Abdullahi, abin mamaki" matsawa Mami databi Abie da kallo asanyaye tayi ganin yafara tafiya big Mum ma ta matsamai suka bashi wuri abakin kofan, sakin hanun Aadil yayi ganin yakaraso kuda da Mami da wani irin gudu Aadil yay wani irin tsalle ya rungume Hamida data makale ajikin big mum yace "oyoyo My Hamida" fashewa da kuka tayi sosai ajikinshi ta kankameshi tama kasa magana but she just miss him, jin muryan Aadil yasa Aabid yajuyo da sauri hada ido sukayi da Aadil daya rungume Hamida yana mata kuka ahankali itama tana kuka, ganin Aabid acikin daki yasa yasaki Hamida da sauri yawani irin ware manyan idanunshi yace "Bid" wani irin tsalle yayi ya shigo dakin batare daya lura da komiba yay wani irin jumping ya rungume Aabid kaman zai kadashi yace "oyoyo Bid" kyam idanunshi suka sauka akan ring din dake aman kudin har lokacin daidai lokacin Abie shima ya shigo cikin dakin, yanda gabanshi yafadi saida dan gajeren fitsari yazubomai daga wando yana tuna warning din OZo aranan da akabashi zoben kudin nan.
Chapter 58 · 0% Book details