← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 69

Sashe 11

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bid we found our Jewel, I love her too, love at first sight ko" gyadamai kai yayi yana share hawayen dayake yi yace "yes, love at first sight my Dil" da sauri yana share kukan dayake yi yace "to when are we going to get married to her?" murmushi yayi sosai jin yasoma dawowa daidai yace "I don't know Dil, she don't like me" da sauri yace "give her roses, plenty plenty rose like kaman a movie" murmushi yayi yace "okay Dil, yanzu kaci abincin da Mami tabaka, go and eat your food and take your drugs okay, anjima your Dr will come" gyadamai kai yayi kaman karamin yaro yace "okay, tell her I love her" dariya yayi sosai yace "rascal okay" dariya shima yayi yatashi yana tsalle akan gado yace "I will tell Mami na kacemin rascal again batahanaka ba yaro kawai" da sauri yana murmushi yace "wayace ma ni yarone zan haihu innai aure dankaji" da sauri shima yana share miyan daya zubanmai awuya yace "me to, nima zan haihu dan kaji, plenty plenty babies" dariya yayi sosai yace "okay naji go and eat your food to" turomai baki yayi yace "the food is peprish Bid" shima turo baki yayi kaman yanda yayi yace "eat small okay and be taking water d pepper will go" dariya yayi yace "Bid I've gotten two friends on my messenger, Anty Hamida and Ihsan, can I be their friend Bid?" yay maganan yana lankwasa kai yana turamai baki, dan dariya Aabid yayi yace "yes chat with them but don't tell them who you are okay" da sauri yace "okay I will not, and...and..and" da sauri Aabid yace "and wat" da sauri yace "my Skype is not working kuma" dan shiru yayi kaman mai tunani yace "I will check it for you inna dawo" da sauri yace "okay, tell her I love her, bye am hungry" da sauri yace "okay I will, oya run, run jekaci abincin ka, finish everything okay" da sauri ya gyadamai kai yana katse wayan, yay tsalle ya dira daga gadon yafita daga dakin yana tsalle sosai yana sauka daga stairs din, da sauri Mami ta tashi daga kan kujera tace "stop jumping Son karka fadi" washe mata baki yayi yataho dawani irin shegen gudu yafada jikinta yace "oyoyo Mami na" yamata kiss a kumatu kafin yatashi da gudu daga jikinta yay dining yaje ya zauna ya bude abincin ya cillar da marfin kasa yadau spoon yafara ci rabi na zuba cikin plate din da dining rabi na shiga bakinshi, sosai Mum ta kafeshi da ido taji hawaye zai zubo mata da sauri ta hadiye kukan ta taso ahankali tazo inda yake taja dayan kujeran kusa dashi ta zauna ta karbi spoon din daga bakinshi, dago idanunshi yayi saikuma ya turo mata baki yace "feed me Mami" debo rice din tayi yabude mata clean mouth dinshi tazuba mai tana murmushi tace "very Good Son" hadiye abincin yayi da sauri yana mata fari da ido kaman wata mace yace "kuma I will not tell you something da Bid yafadamin taaaa" yamata gwalo, murmushi tayi takara kaimai abincin baki tace "fadamin mana Son, haba my one and only Aadil" washe mata baki yayi shinkafan bakin na zubowa waje tana sharemai yace "no I will tell you when Bid is back, but Mami" yakira sunanta yana zare manyan fine lulu eyes dinshi yace "I love her too Mami yeeee" yay maganan yana lumlumshe idanunshi kafin yay luuu zai kwanta akan plate din abincin da sauri ta janye plate din abincin ya daura kanshi kan table yay bacci, shiru tayi tana kallonshi kafin ahankali ta ijiye plate din a gefe ta daura hanunta akanshi tana shafa soft gashin kanshi dayasha gyara dayan hannu ta kuma tana cire rice din daya bata kumatun shi tana sharemai oil din, ahankali tama forehead dinshi kiss kafin takira sunanshi tana bubbuga bayanshi.

"Aadil, Son, Son get up muje ka kwanta adakin ka" cikin bacci ya make mata kafada yana turo baki yana tsotsan bakin, kyaleshi tayi tana kallon agogo dan nan da 15min Dr shi zaizo ya duba shi as usual idan yazo yatashi dole.

IN BANI
_M.

Shakur_
10....

Gyara zaman kujeran motan yayi yadan kwantar da kujeran ya rungume wayan sosai a kirjinshi yana tunanin dan uwanshi, shi karan kanshi he's missing him, he miss his twin Brother so much, tunane tunane yadinga yi harwani irin bacci mai dadi yay gaba dashi acikin motan.

Kiran Sallan asubahi dayaji yatayar dashi daga baccin dayay awon gaba dashi, ahankali ya bude ido gabaki jiyayi duka jikinshi namai ciwo, yana kallon inda yake yatuna acikin mota ya kwana, dan gajeren tsaki yayi yabude motar yafito ya rufe ya fita daga asibitin ya sallaka titi dan masallacin yana ta dayan side of d road ne.

Saida yajira rana tafito yasakeyin raka'a biyu sanan yafito daga masallacin, wani dan mini supermarket dake gefen mosque din ya shiga yasai brush da tooth paste yafito ya tsallako yadawo cikin asibitin yana tafiya ahankali yay wani irin kyau yana lumlumshe ido alamun bacci bai isheshi ba, shigowa cikin asibitin yayi yy hanyar dakin da aka kwantar da ita, da sallama ciki ciki yabude kofar dakin datake, babu kowa adakin saima gadonta da aka gyara, anyi mopping tiles din kasa sun bushr sai sheki suke, karasawa ciki yayi yana karabin ko'ina da kallo yaja kujeran ya zauna yana kallon TV dakin dayaga an kunna yana tashar CNN, karan bude kofan bathroom yasa yadago kai da sauri wata nurse ce daban tafara fitowa tana kallon cikin bayin, shima kofar bayin ya tsare da ido ya kosa ya ganta, ahankali tafito kanta akasa tana wasa da kumbunan hanunta dasukai wani irin haske, kana ganinta kasan wanka tayi an bata doguwan riganta da aka wanke mata a laundry tasaka yamata kyau sosai, fuskarta babu komi looking natural, kanta babu dan kwali dan nata tun aruwa yabata, kafafunta na cikin wani white slippers dasuka bata tasa, tai wani irin kyau cikin sea blue gown din kaman wata amarya, tunda tafito idanunshi ke kanta bayako kyafta ido harta karaso wajen gadon kafafunta na harhardewa, jitake kaman zata fadi, nurse dince ta kalleshi tace "good morning Sir" gyadamata kai kawai yayi batare dayace komiba, ta kalleta yanda ta tsaya bakin gadon tana wasa da kumbunan har lokacin tace "ki zauna magani zan baki" ahankali ta zauna kaman wacce ke tsoron zama akan gadon, daukan magungunan tayi nurse din tabata tasha da kyar sanan tadau coffee da asibitin suka hada ma patient dinsu dayake arufe yanada zafi sosai ta bata tace "finish it okay" gyadamata kai tayi hakan yasa tai murmushi ta kalli Aabid dake kallonta kaman zai cinyeta tace "Sir your wife is very beautiful" wani irin murmushi yayi yana kallon fuskar nata harda dan kada kafa yace "oh yeah she is, right Jewel?" da sauri tasa hannu tana sosa idonta ko kadan batajin dadin yanda suketa kallonta batada dan kwali batada hijabi jitake kaman ta nutse akasa sabida kunya, murmushi nurse din tayi dake kallonta tace "shy, shy" ta kalli Aabid tace "Dr is coming, he will examine her first before discharging her, dama you've cleared all d bill babu abinda zaka biya kuma kawai sallaman ki zaiyi" gyadamata kai yasakeyi batare dayace mata komiba tajuya tafita daga dakin ta rufo musu kofan.

Juyo dakai yayi ya kalleta yanda har lokacin take rike da cup din coffee sai sunnar dakai takeyi, ahankali yatashi daga kan kujeran ya matsar da kujeran baya yay kneeling akasa agabanta har kafafunta na gogan kirjinshi da sauri ta daga kanta ta zaro ido cike da tsoro, murmushi yamata ya zare cup din coffee daga hanunta ya ijiye akan side drawer yana kallon fuskarta, hanunta yakama ahankali kaman yana kama kwai da sauri zata fisge hanunta yarike gam da sauri yana girgiza mata kai yace "no please" yay maganan yana kama dayan hanun yana kallon fuskarta itama shi take kallo kirjinta nawani irin bugawa idanunta sun cicciko da kwalla, murya chan kasa yakirata.

"Amatullah" marmar tai da idanunta dake shirin fitar da ruwa, ahankali yace "your brother is on his way to come and pick you, and I don't want you to go batare dana bayyana miki sirrin dake rainaba" shiru yayi yana kallonta itama shitake ta kallo he could feel yanda kirjinta ke bugawa daga veins din hanunta, kara kwantar da murya yayi yace "I love you Amatullah" wani irin bugawa da kirjinta yayi yasa tafashe da kuka sosai dan ko kadan ta tsani soyayya ita babuma abinda ta tsana irin aure, tsoron maganan aure ma take barinma soyayya, ko wanan ma daya ganta haka sa'a yaci batada lpy kuma batasan ina takeba da tuni tasan yanda tayi ta sabe, hanunta yadan matsa yana kallon yanda take kuka da muryanshi datai rauni sosai yace "I just saw you jiya and am completely blown away, I love every single thing about you Amatullah tunkafin ma ki bude ido, the way am connected to sunrise tun ina yaro I've always said maybe akwai wani abu da Allah ya tanadan mini a irin lokacin ne, wen I was small nasha mafarki na tsinci my Jewel acikin ruwa, ashe hakane, the first time I saw you was d yamma, the first I saw you acikin ruwane, your face was glittering yana wani irin haske as bright as the moon acikin ruwan nan, and right there, just right there nasan you are mine, nasan you are the one, deep down I felt this force of attraction dat keep pulling me towards you, I fell for you the very first time I set my eyes on you, please Jewel I know you are not married cus u don't look married, will you give me that honor to become your life partner?
Chapter 11 · 0% Book details