← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 69

Sashe 21

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aadil dina yamutu?" kaman wacce tasami tabin brain ta kalli yatsunta kaman yanda Aadil keyi tafara kirgawa cikin sambatu tace "Aadil was counting his fingers playing while I was driving, all of a sudden ya cire sitbelt yabude kofan mota yafice, yabuge yafadi sosai a kasa, matching brake nayi arude na kalleshi daganan bansan meya faruba, tell me!" tai wani irin ihu tana kama rigan Abie dake kanta tace "Abie meya sami d'ana wlh inkamin karya zanyi fushi da dukanku kafadamin" alamu yama Aabid dake zaune yana kallon Mami yamatsa, zama yayi ya bata one side hug yadan jijjigata yace "in sha Allah nothing will happen to Aadil, zamu nemeshi zamu bada cigiyarshi, and we will get d police involve inma d accident was a well careful plan accident dan ayi kidnapping nashi we will know, calm down okay karwani ciwon yakama ki, I swear, I swear to you zan nemo mana danmu" cikin wani irin kuka mara kara tace "promise me Abie u will find my Aadil for me" shima idanunshi sunyi jajir jijiyoyin kanshi duksun fito yace "I promise you Mum Aadil" tashi yayi da sauri yay hanyar kofa su Suleman zasu bishi yay murmushi irin na tashin hankali yace "karku damu am coming, in baku ganni dawuri ba get d police involve" da sauri Suleman yace "ina zaka Abdullahi?" Juyawa kawai yayi yana kokarin hana kanshi hawayen dazasu zobomai yace "ina zuwa kawai Yaya" ficewa yayi da sauri Mami ta fashe da kuka tai hugging Aabid tace "Son where is your brother?

Idan ban ganshi ba mutuwa zanyi wlh, you and Aadil are my entire life, please So.." tafashe da kuka sosai, ahankali yadago kanta daga jikinshi yasa hannu ya share mata hawayen, da muryanshi data dishe sosai yace "stop crying Mami, I will find my Bro okay" gyadamai kai tayi tana kuka, Big Mum ta kwantar da ita tace "kwanta ki huta ruwan ya shiga jikin ki da kyau" tashi Aabid yayi yafita shida Yayin mamanshi.

Sosai Abie ke zuba wani irin uban gudu akan hanya, bini bini yake share yan hawayen dake zubomai, sosai yay tafiya kaman zaibar garin kano sanan ya yanki cikin wata yar karamin kauye yadinga kutsawa cikin kauyen nan da jeep dinshi haryakai wani babban farm house, a kofar gidan yay parking yafito rike dawata yar jaka yarufe motar, yaciro wasu key yabude gate din ya shiga, gidan ciyayi sunma soma girma kota ina, ya karasa har gaban wani flat dake compound din ya shiga yar barandan dazai sadashi da daki rike da makullin da wayarshi, ciro key yayi yabude kofan ya shiga ciki, babban falone dayay dan kura da alamu an dade ba'a shiga gidan ba, wani dan corridor yayi hanunshi har rawa yake yabude wani katoton makulli dake makale jikin kofan ya bude sanan ya zare ya ijiye key yabude kofan amugun hankali ya shiga dakin, dakine da komi nacikinshi ja, kaman dajan kyalle aka zagaye bangon dakin, kasanma wani irin jan carpet ne ja sosai a shimfide kota ina, ahankali ya shiga dakin da yay dan kura ya maida kofar ya rufe yasaka sakatan sama data kasa sanan ya shigo ciki ya ijiye jakan daya dauko akasa duk da sauri sauri yake komi ya zage jakan ya bude wasu jajayen kayane suka bayyana da sauri ya kwabe manyan kayan jikinshi ya ijiye kasa sanan yadau jajayen kayan yasaka babban bubun rigane dake jamai har kasa da sauri ya tsugunna ya kwashi kayan daya cire ya maida cikin jakan yaciro ashana daga jakan ya daga jakan ya jinginata da bango yatashi yaje gaban dakin inda wani manyan gumaka suke da aka musu zane a fuska kaman da chalk, kafafunsu daure dawasu irin bangles sai kuma jajayen candles guda shidda suma, kneeling yayi ahankali agaban gumakan sanan ya kyasta ashana ya kunna duka candles din sanan ya hura tsinken ashanar ta mutu ya yar a gefe, shiru yayi yana tunani yana kallon gumakan kafin ahankali ya dukar da kanshi yahade hannayenshi biyu agaban gumakan yace "Ozo the tittle holder, Ozo the tittle holder, Ozo the tittle holder, macukubelebele kaino kaino, macukubelebele kaino kanooo" shiru yadanyi zuciyarshi namai wani irin azababben zafi, ahankali cikin wani irin dishashiyar murya yace "Ozo ka bayyana agareni inada bukatar ka, I summon you Ozooo" bai karasa kiran sunan ba wasu mutane guda uku suka bayyana a dakin a tsaye da ba'a ganin fuskokin su suna sanye da jajayen dogayen riguna daya rufe har kafarsu sai babban su dake sanye cikin black doguwan riga shima kanshi akasa yana rike dawani karfe dakeda Kwai kaman kwan jimina asaman karfen, cikin wani irin magana mai echo sukace.

"mesa kake neman Ozo" kaman jira yake ya rarrafa da gudu yaje gaban me bakaken kayan yay kneeling yana hada hannayenshi yace "great one Ozo, Ozo nakiyaye kowace irin dokan ka, wanan zoben" yanuna babban zoben yatsarshi arude yace "kaman yanda kace bantaba cireta daga yatsata ba, Ozo nasan ni mai laifine tun kafin na shigo kungiya aka fadamin sharuddan kungiya wacce shine d'a namiji dazan fara haihuwa a duniya nakune shine sacrifice dazan...." yay shiru hawaye na zuba daga idanunshi sosai da kyar cikin wani irin asalin tashin hankali yace "great Ozo bantaba sanin haka abin yakeda mugun wuya and tough ba saida na haifo yan biyuna mazaje kyawawa" yadanyi shiru yana goge hawaye sanan yace "great one Ozo da gudu nabarosu a asibiti nadawo gida na shiga boyayyen daki namaka kira ka amsani, ka bayyanan min, naroki afuwa da alfarma akan karku daukemini Hassan wanda yake na farkon, karku kashemin shi, great one Ozo nasan kamin adalcin da baka taba yima wani a kungiyan nan ba, kabani zabi biyu masu sharudda sabida yanda ka tausayamin kakuma Soni, zabin shine ko kukashe shi kusha jini, koku shanye min shi, da ranshi amma shida yaro basuda bambamci, da gudu na yarda tsabagen yanda nakeson Yan biyuna, gakuma wani irin special son Hassan din da Allah ya dauramin danshi nafara dauka a hannuna a tsumma kafin na dauki dan uwanshi Hussain, na yarda da Hassan mutu gwara kunsaka ranshi a kwalban kunyi duk yanda kukaga dama dashi daku kashemin shi na yarda dari bisa dari ku maidashi yaron kusa ranshi a kwalban bakomi, sai kuka fara koromin sharuddan zabin danayi na karya mutu, kace duk wani ciki da Maryama zatayi tun cikin na wata biyar zaku shanye cikin, haka na yarda cikin da Maryam ke dauka dai, dai, dai, har sau uku Maryama nayi duk kuna shanye wa tana bari duk sabida karku kashemin abin kaunata Hassan ban damuba har mahaifanta ya sami matsala tsabagen wankin ciki da ake mata tadena samin cikin, bayan haka kuka bani sharadin cewa ko bayan shanyayyen dan nawa yay girma bazai sake yay aureba shima na yarda to tayaya ma mara lafiya yaro mai kwakwalwan yara zaiga mace yace yanaso duk na yarda, kun hanani cin naman rago duk banaci, kun hanani cin dabino shan zuma duka banyiba dukdan karku kashemini Hassan, mesa yanzu zaku chanza komi ki daukemin farin cikina eh bayan na kiyaye kowace doka da sharuddan ku eh Ozo the great one?".

IN BANI
Maman Abd Shakur
18....
_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan_
_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_
_masu fitarmin da novel waje, please kindly stop_
Sosai Abie yafashe dawani irin kuka ya kife kanshi akasa yana kuka sosai yana hawaye, shi karan kanshi baisan wani irin so yakema Aadil ba, Allah yaga abinda yagani ne ya jarabce shi da mugun son yaron, Aadil nada wani irin shiga rai fiye da tunanin kowa saika zauna dashi zaka gane hakan, son Aadil yake bana wasaba, idan har Ozo ne ya daukeshi hala mutuwa zaiyi dan baijin zai iya rayuwa babu yaronba.

"Tursoso!" yaji an kiranshi dan bayan ya jona kungiya sunan da Ozo the great one yasamai kenan, da sauri ya dago kanshi yana goge hawayen daya gama wanke mai fuska idanunshi sunyi ja sosai, cikin wani irin murya dake echo adakin mai bakaken yace "bayan kasan ka kiyaye sharudda, me a tunanin ka zaisa mu daukema d'a?

Bama dauka saidai mu tsotsa agabanka, bama dauka saidai mu tsotsa kaman yanda muka tsotse cikin matarka agabanka haka zamu tsotsemai jini agaban ka ya mutu babu jini ko digo a jikinshi" yaydan shiru sai chan cikin wani irin murya mai firgita zuciya yace "babu hanun mu abatan danka saidai zamu gargadeka akan abu daya" yasakeyi yin shiru yace "ba danka ba aure Tursoso, ba danka ba aure Tursoso, ba danka ba aure Tursoso" gyadamai kai yayi hankalinshi yawani irin kwanta kaman an yayemai wata irin bakin tsoka daga kirjinshi yay murmushi yace "nagode, nagode Ozo the great one" wani irin nishi Ozo yayi irin na matsafa yace "shikenan matsalan ka ko akwai wata?" murmushi yayi cikin jin dadi yanda Ozo keji dashi yace "dama Ozo naga jiya yakamata zobena yamin aman kudi, jiya lahadi amma baiyiba, shine nace maisa baimin ba?

Ko wata laifin nayi?" dariya Ozo yayi irin dariyan matsafan nan.

"ha ha ha hmmm, Tursoso anchanza ranan aman kudin ne, gobe ne zaimaka aman kudin" da sauri yay murmushi yace "to Ozo nagode" batcewa sukayi bat da sauri ya hure candles din duka ya tashi yaje ya chanza kayan ya maida asalin wanda yasa yamabar akwatin a wurin sanan yacire sakatan kofan yabude kofan yafita daga dakin yarufe kofan da katoton key dinshi sanan yawuce yay tsakar gidan yafice ya shiga mota yaja yabar wajen.
Chapter 21 · 0% Book details