← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 69

Sashe 39

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffa ne da yaranshi maza uku su sulaiman sai kuma limam dawani amininshi duk sunci manyan fararen kaya suja shigo, ta window Zainab da Hamida da Ihsan suke lekawa sukace su waye wayan nan ita Hamida bama ta ganesu ba wlh hakan yasa suka dinga lekensu har suka shige sasan Kaka.

Zama akayi dayake falon Kaka da girma fes ya daukesu harda wani enough space dazai dau kusan mutane goma ma, gaisuwa akai ta mutunci suka gaishe da Kaka sosai ana raha ana dariya kaman ansan juna nan Anty Lami da Zainab suka gabatar da aban sha da kulolin abinci, ba laifi sunci abincin sosai suka sha lemu sanan aka tattara komi Baffa yabude taro da addu'a ya kalli su Abba yana wani irin murmushi mai nuna tsantsan farin ciki yace "bazan taba mantawa da karamcin ku da alkahirin ku aduniyan nanba, kun taimake ku kun share mana hawaye, ba kowani musulmi zai iya abinda kukayi ba saimai karfin imani da taqwa, kuma inamai tabbatar muku bazamu taba wulakantar muku da yarku ba da izinin Allah, xamu riketa amana sanan ina mai shaida muku da in sha Allah Hassan dinma yakusa samin lafiya yanzu haka zamu faramai na gargajiya ne dazaran yasami lafiya an sallameshi daga asibiti kuma munasa ran za'a dace in sha Allahu, yanda kuka taimake mu kuka sharemana hawaye ubangiji Allah ubangiji ya share muku hawaye kuma ranan gobe kiyama, shi aure dakuke gani yana tattare da dunbin rahma da ni'ima damu bazamu taba sanin mai Allah ke nufi da auren nan nasuba sai nan gaba domin kuwa komi dakaka yafaru aduniyan nan kaddara ce kuma da dalilin faruwanta, fatan mu shine ubangiji Allah ya basu zaman lapiya Allah yakuna albarkaci abinda muke kokarin hadawa ayanzu" atare duk akace Ameen dudda dai Abba bai gama gane kan zancen ba he's a lil bit confuse, gyara zama Kaka tayi tana murmushi tace "yauwa to Alhamdulillah komi daka gani kaddara ne, mun hadu ta alkhairi insha Allahu mun daura kenan yanzu sai afara gabatar da kayayyakin dana fada muku jiyako, kudin kun gani kunaso, kudin gaisuwan iyaye, kayan sarana dakuma kudin sadaki" wani irin kallonta Abba yayi zuciyarshi na neman bugawa, dauke kai tayi kaman bata ganshiba Abban Ra'is kuma yadanyi tapping cinyar Abban ahankali alamun karyay wani abu dazaisa suji kunya hakan yasa yay relaxing wearing a smile, murmushi Baffa yayi yace "to Hajiya" ya kalli su Suleman da Muhammad yace "Bismillah" tashi sukayi suka fita daga dakin basu jimaba suka fara shigowa da kaya niki niki tareda wasu yara yan anguwan akwati set biyu suka kawo guda shida shida na Louis Vuitton, sai manya manyan tabarma guda biyar, dasu goro jaka goma, su dabino sai wasu kwalayen hadaddun sweet da chocolate katon goma, sai su kwalin biscuit saikuma kudi yan dubu wrappers na dubu daidai da bama tasan na nawa bane sai harba ido take shiko Abba da Abban Ra'is shiru sukayi suna kallon ikon Allah, aminin Baffa ne yasake bude taron akaro nabiyu da addu'a yace "ga kayan nagani ina so dinan, gakuma kayan sa ranan, munaso ayanke mana sadaki sanan asaka ranan ko to Bismillah Alhaji" yay maganan yana kallon Abba da miyan bakinshi gabaki daya ya kafe ya bushe, hadiye miyau yayi ahankali ya kalli Kaka data zuba mai idanu irin kallon nan na kace bazaka karamin jayayyaba, dan gyara zama Abba yayi Anatse yana kallon kayan yace "wanan kaya haka Alhaji kaman muna sayar da yarinya agaskiya sunyi yawa, banda haka wanan akwatin ai babu bukatar su awajen sa rana ko?

Kawai abarmata su amatasayin akwati kar akawo wan..." "kaga yaron nan nawa bai iya komiba haryau" Kaka tafada tana dariya ganin Abba na neman mata bukulu tace "ko yayyin Hamida gabaki dayansu nina aurar dasu saisa baisan kan abubuwan al'adun mu na hausawa ba, yanzu dai maganan sadaki muke ko?" tai maganan tana hararan Abba ta kasan ido ahankali ya saukar dakai, tace "yauwa sadaki" tace "yauwa sadaki kubada dubu dari, kudin kun gani kuna so dubu dari, sanan kudin gaisuwan iyaye dubu dari" innalillahi wa innailaihi raji'un Abba kawai yake fadi aranshi wace irin uwa gareshi dakeda shegen son kudi haka sabida taga masu kudi ne takeson siyar da yarshi haka dan anasu Ayush duk batai abinnan ba, patting cinyarshi Abban Ra'is yayi hakan yasa yasake murmushi, abokin Baffa yace "to Masha Allah" ya dauko wrap na yan dubu daidai guda uku duba dari uku kenan yamikama Abba cikeda ladabi, asanyaye Abba yamika hannu ya karba yana murmushi Kaka ta saki buda.

"ayiriririi" Abba ya kalleta ganin yanda take murna yasa ya kalli Baffa yace "nabaku ubangiji Allah ya kaimu ranan yaja mana rai" Ameen duk akace Kaka tace "sati hudu, nan da sati hudu biki, asabar din dazata fado ana sati hudu ne biki da izinin Allah" takara sakin musu guda dayasa su Baffa dariya sosai nan aka kachame ana hira Abba yadan saki jiki yana basu amsa wuraren karfe daya suka tattara suka tafi bayan sunma Kaka kyautan ragowan kudin wai tarabama jikoki aiko Kaka harda rawa tarakasu har gate saida taga tafiyar su sanan suka shigo gida ta daure fuska rass dan karma Abba yakawo mata wata maganar ta kwalama Mama da Anty Lami kira tace "kuzo mu bude akwati muga abin ciki".

Tai sasan ta Abba yabita da kallo zaiyi magana Abban Ra'is yace "kayakuri iyayen mune, babu yanda zamuyi dasu sai hakuri kawai, ko zaka mata ba yanzu ba, kabari anjima koda da daddare ne saika mata magana kaji" gyadamishi kai kawai yayi Abban Ra'is yace "muje gidan kaji kawai" fita kawai sukayi waje suka shiga mota suka tafi..

Zama Kaka tayi akan kujera tana kallon kayan daidai nan Mama da Anty Lami suka shigo, da mamaki suke kallon kayan Anty Lami tace "kayan waye wayan nan haka Kaka?" cikin tsananin murna Kaka tace "dukna Hamida ne wlh, mai sunana nada kashin arziki wlh, mutanen jiya nakirawo suka dawo dan sunban tausayi nabasu auren Hamidan ansa rana sati hudu, wanan akwatunan fa duk na sa rana ne, akwai na asalin aure na nan zuwa gab da biki" shiru daga Mama har Anty Lami sukayi dan maganan ta mugun basu mamaki bama tasan tayaya zasu amshi maganan ba.

"dalla kuzo kuyatayani bude akwatin" ahankali suka shiga Mama ta kakalo murmushi Anty Lami tafara bude akwatunan suna dubawa kayane hadaddu bana wasaba, Kaka tabasu su sweet da dabino da goron tace "gashi nan a kulla a aikawa makota sati hudu, akwatin anan shashina za'a barsu ni yanzu fita zanyi akwai abinda zanje nayi" tai maganan tana Jan babban gyalenta dake kan kofa Lami tace "Allah kiyaye" ameen tace tafice, ahankali Mama ta share hawayen daya zubomata ta tashi fuuu da sauri Lami tarike mata hannu tace "zonan Maman Ayush ina zaki?" cikin fushi da Anty Lami ta dade bataga Mama cikiba tace "haba Anty, haba Anty dan sunga nai shiru komi ina kawaici na dauki Kaka a matsa yin mahaifiyata saisu nemi su takani, nice mahaifiyar Hamida inada right akanta haba Anty yarinyar da gata sai ahankali ne bamata da baki shine zasu dauka subama mahaukaci, wlh bazan yarda a cucen min Hamida ba, tausayin yarinyar nan nake bana wasaba, duka duka guda nawa take, shekaran ta ashirin fa, ki barni naje nakira mahaifinta Allah yau zaiga bacin raina bana wasaba" riketa gam Anty Lami tayi hakan yasa tafashe da kuka tafada jikinta, rungumeta Anty Lami tayi tace "calm down yanzu ranki abace yake don't take any decision a haste, am sure ko Abban Hamidan baiso hakan ba, Bakiga uwar tashi bane, jarababbiyar uwa taga kudi, kiyakuri kinji ki tsaya kiyi tunani kibari har anjima yadawo saikimai maganan kinji" Gyadama Anty nata kai tayi ahankali trying to calm herself down ta zauna kan kujera zama gefenta Anty Lami tayi tana shafa bayanta hartai shiru sanan Tace "bari na gyara kayan ko saimu kwashi goron da sweet din mutafi dashi karya zama wani abin maganan kuma" gyadamata kai tayi ahankali, hakan yasa Anty Lami ta tattara ta gyara kayan ta kawshi sweet din dazata kwasa da chocolate daidai ta kalli Mama dake kallonta asanyaye duktai wani iri sanan tace "muje" tashi Mama tayi ta tayata rike wasu suka fita daga dakin suka rufo kofan suka fice sukai sasan su Hamida suka samu daf Zainab dake wasa da filon kujera sai dariya suke Ihsan na tsalle, da sauri Hamida ta yarda filon ta kalli Mama da manyan eyes dinta da kitson kanta dasukai shegen tsufa tace "Mama kinga Anty Zainab na tsokanana ko" hararan su dukansu Mama tayi ta wuce tai ciki dan ranta abace yake duk sukabi Maman nasu da kallo, Anty Lami ta ijiye su sweet din tace "Zainab dagake har Ihsan kuzo kutaya Hamida tsefe shegen kitson nan yay tsufa dayawa" da sauri Zainab da Ihsan sukazo duk suna kallon su chocolate din hanunta batare dasun rokaba dan anhanasu roko tun suna yara, ajiyewa tayi ta bude ta debo dayawa ta basu suka karba suna murmushi sanan tawuce ciki wajen kanwarta sukuma sukai zamansu a falo suna kallo amma bini bini Aadil ke fado mata arai bana wasaba tarasa mesa takasa mantawa dashi.

Bayan la'asar Kaka ta shigo gidan tareda yara sun kwaso mata kaya a ledoji, kwalama Hamida kira tayi.

"Hamida, Hamida" dakama Hamidan duka dake bacci zainab tayi hakan yasa tabude ido ahankali ta kalli Zainab din.

"Kaka na kiranki" tashi tayi daga kan gadon ta sauko tafito daidai Kaka takaraso bakin kofar su ta kalleta tace "uwar bacci wuce kije kiyi wanka ki shirya kici gayu kifesa turare yanzun nan zanyi salla nafito, fita zamuyi" gyada matakai tayi ahankali tana murza ido sanan tawuce Kaka ma tabita da kallo kafin tasaki labulen tawuce sasan ta.
Chapter 39 · 0% Book details