← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 69

Sashe 42

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"wayyo" tarike wuyan riganshi da kyau sabida yanda tafin hanunta kemata wani irin shocking, da sauri da sauri yake lasan soft kumatunta kafin ya birkito da fuskarta ahankali yana kallon fuskarta yanaji kaman kanshi zai tarwatse, lips dinta dake shining din man bakin data shafa ya kafe da ido baisan lokacin daya wani irin daura bakinshi akan bakin ba ya shiga kissing dinta da sauri har wani nishi yake yana sauke ajiyan zuciya shi kanshi baisan meyake yiba kanshi kawai ke directing dinshi yake abinda yakeyi, da duka karfinta tasa hannu ta ture kirjinshi ganin kaman zai cire mata baki hakan yasa yasake a tsorace, cikin fushi ta waska mai mari da karfi tana hararanshi sabida bakin cikin abinda yamata da sauri yadafa wajen yana kallonta, goge bakinta tayi tanaji kaman tai ihu hawaye na zuba daga idanunta kafin ta kalleshi shima ita yake kallo hanunshi dafe da kucinshi, harara tasake ballamai tama rasa mezatace mai tajuya da sauri zata fita daga dakin dan ko ina na jikinta rawa yakeyi, wani irin fashewa yayi da kuka yana girgiza mata kai cikin kuka sosai yace "don't go please" tsayawa tayi chak tajuyo ta kalleshi batare datama san meya hanata tafiyan ba, sakin mata wani irin kuka sosai yayi daya wani irin narkan da zuciyanta yana girgiza mata kai cikin kukan yace "please don't leave me again" karasawa ciki tayi asanyaye batare data sake kallon fuskarshi ba taja plastic chair ta zauna tareda daukan furan ta rufe ta ijiyemai akan saman drawer sai kallonta yake soyake ya shige jikinta kozaiji dadi but he's scared bayaso tamai fada kota sake marinshi, baiso yaga tana fushi, dan kallonshi tayi ganin yanda yay wani irin zuru zuru sai goge kwalla yake yasa tadan sakin mai murmushi da sauri ya sakin mata murmushi yana clapping hands da sauri hawaye na zuba daga idanunshi yace "Hamida my wife is smiling" murmushi tasake mai tai shiru tana kallonshi dan wani irin mugun tausayi yake bata zataso taji yanda yafara ciwon nan, zataso taji labarinshi, zataso taji ya akayi shi baida lafiya and dan uwanshi is fine, hakanan takeji zata iya komi dan kawai taga yadawo kaman kowani babban namiji, sosai takejin Aadil aranta kuma tarasa mesa hakan, bude kofan da akayi yasa duk suka dago kai, Baffa ne ya shigo tareda Kaka sai Mami da Abie da Aabid dake tareda Mami dan sun shirya yanzu duk yay wani iri, ahankali ta saukar da kanta kasa tana wasa da yatsun ta, Kaka ta kalli Aadil din dake kallon Mami yana mata alamu datazo tace "sannu da jiki, Allah sarki ya rame sosai, idanunshi sun kode alamun ciwo, ya jikin?" kallonta yayi saikuma yaturo mata baki tareda mata fari da ido yace "fine" sanan ya kalli Mami batare daya kalli Aabid daketa kallonshi ba cikin tsananin farin ciki yamata alamu datazo yana mata pointing Hamida yace "Mami come and see My Hamida, tazo" ya kalli Baffa daketa murmushi yana kallonshi ganin yanda yay kaman bashiba yace "come and see her grandfather" Mami ce takaraso kusa dashi yawani irin fada jikin Mami cikin tsananin murna yana nuna mata Hamidan da hannu yana wani irin cute smile dake karamai wani irin mugun kyau, murmushi Mami tayi tace "naganta amma yanzu Hamida zata tafi itada grandma dinta she will come tomorrow okay kaga yamma tayi" kallon Mami yayi da sauri kafin ya make mata kafada yace "no i don't want her to leave me again" ahankali Mami tace "please Aadil zata dawo kaga magrib tayi ko" make mata kafada yayi kafin yasaki kuka ahankali, Mami ta kalli Hamidan data kasa dago kanta tace "tashi kutafi daughter kinji" sakin Mami yayi yarikema Hamidan hannu da gudu yana kuka yana bubbuga kafa da sauri Kaka ta share hawayen dake neman zubo mata ta girgiza kai, kai wanan yaro na bata tausayi bana wasaba wlh, hakan yasa ta matso kusada Mami tace "kinga maman yan biyu barshi kinga sai kuka yake kar zazzabin yarufe shi kuma, anjima inyay bacci matafi" da sauri Baffa yace "a'a baza ai hakaba, magrib tayi Hajiya in aka biye tashi ba yanzu zaiyi baccin nan ba" yay maganan yana dogara sanda yana kallon fuskan Aadil din daya rirrike hanun Hamida yana kuka sosai yana bubbuga kafa, wani irin jin kukan nashi Hamida take har akasan ranta amma takasa dago kai balle ta lallashe shi sabida kunyan su Mami gashi saijan hanun nata yake yana kuka, ahankali Baffa ya dafa kafadarshi yace "zokaji" magana yamai a kunne da sauri ya kalli Baffan cikin kuka sosai yace "are you sure?" gyadamai kai Baffa yayi cikin lallashi yana sharemai hawayen, ture hanunshi yayi ya tsugunna agaban Hamidan ya daura hannayenshi akan cinyarta ya leka fuskarta hawaye nafito daga idanunshi jiyake kaman zaiyi hauka, hada ido sukayi da Hamidan, ahankali cikin kuka yace "is it true zamuyi video call?" gyadamai kai tayi dudda bamata da waya, girgiza mata kai yayi yace "please don't go and leave me zan mutu" yanda yay maganan yana kuka saida yataba zuciyar kowa adakin da sauri Abie yafita daga dakin ya shiga restroom dayake hanyar dakin, ya shiga wani bayi da sauri yarufo kofa yaciro handkerchief daga aljihun shi ya daura akan idanunshi yahau kuka, kuka sosai bana wasaba.

"wani irin kwadayin duniya yakaini na jefa d'ana wanan halin dayake ciki yau?

Banrasa ci ba, ban rasa shaba, ban rasa sutura ba, inada su Suleman dasuka daukeni a matsayin dan uwan su, inada mahaifin su daya daukeni a matsayin danshi, ina da aiki na, ana biyana daidai na level din karatuna a kamfanin Baffa what push me?

Wani irin greed yakaini nafada wanan halakan?

Aadil na cuceka, na cuce ka bana wasaba, nacuce ka my son, i can't forgive myself, i can't forgive my self, my son has been suffering yanzu for more than 30yrs all because of me ya zanyi?

Tayaya zan bulloma wanan tsaka mai wuyan danake?

Tayaya zan hana Aadil auren nan?

Tayaya zan ciremai son yarinyar nan?

Tayaya zan rabashi da yarinyar nan" yabata kusan rabin awa abayin yana kuka sanan ya wanke fuskarshi ya share tass sanan yafito.

Fitowa yayi daga bayin daidai lokacin Mami tafito daga dakin hada ido sukayi da sauri ya saukar da idanunshi kasa dan bayason tagane yay kuka, hakanan kawai yaji yana wani irin jin nauyin ta dan ya mugun yaudaranta, ya cuceta itada yayan su, hanunshi dayaji an kama yasa yadago kai suka hada ido da ita, tattausan murmushi ta sakin mai tasa hannu ta shafa sajenshi cikin muryan kwantar da hankalin miji down tace "kadena damuwa Abie, Aadil dinmu zai warke da izinin Allah, watarana duk wanan abin labari zai zama kaji" gyadamata kai yayi asanyaye hakan yasa tai murmushi tace "zomuje office din Dr, kaina fito na nema dama Aadil yay bacci, Dr yace muganshi, ni inaso a sallameshi ma gobe kawai dasafe mukoma gida mai maganin da Baffa yakiramai yazo afara gwada maganin gargajiyan kafin bikin nashi ko, let's see what Allah has install for us and banda hakama aure rahama ne let's just team up and be praying for our children ko Abie" gyadamata kai yayi yama kasa mata magana sabida yanda jikinshi yay mugun sanyi, yasha attempting yafadi mata gaskiya but bayataba iyawa he loves Mami so much da he's afraid of losing her, bayaso yafadi mata gaskiyan wayeshi ta tsaneshi taki zama dashi, his heart cannot bear that, ahaka suka bude office din Dr suka shiga shiga sai tunane tunane yake.

Gari yafara dan duhuma dan gab da isha'i suka isa gida, Mama kadaice a tsakar gidan tana nannade tabarma zata shiga daki, da sauri Hamida tai wurinta tafada jikinta tana murmushi tace "Mama mun dawo" dan murmushi Mama tayi dan sosai take fushi ta kalli Kaka data karaso wajen tace "sannu da zuwa Umma, ina yini" "yauwa Haleematu, lpy lau ina sauran yaran?" Kaka tafada tana daure fuska ta kalli Hamidan tace "ke wuce mutafi akwai gyaran dare dazan miki" tai maganan tanajan hanunta tai gaba da ita Hamida tajuyo da sauri tana kallon fuskar Mama data shige daki abinta, Kaka tawuce sasan ta da ita, akwatin falon ta nuna mata tace "ga akwatunan kayan sa ranan ki nan keda Aadil sati hudu baban ki yasaka, shi suka kawo dazu da safe shine ubanki yace na dauke ki nakaiki ki gaida yaron, ashe haka yaron ke sonki yarnan?

Jibi yanda yadinga babbaka kuka dazaki tafi, Allah dai yakaimu bikin mu auramai ke yahuta da wahala wlh yaron na masifan bani tausayi" da sauri Hamidan ta kalleta dan bakaramin faduwa gabanta yayi da maganan ba ahankali bakinta har rawa yake tace "ni Kaka?

Nace muku ina sonshi ne?

Ninace zanyi aurene?

Ba Anty Zainab za'a aurar ba kafin niba" mugun harara Kaka ta watsa mata tace "kisami ubanki kimai maganan ja'ira rasakunyan beran tanka, ai bani nabada auran nakiba, wuce kije kiyo alwala kiyi salla akwai abinda zan hadamiki kici, kuma wlh aure bafashi saisa daga yanzu andena ganin murmushi na balle wani shege ko shegiya takawomin maganan banza a gidan nan, bazan bude ido inaji ina gani kumin bukulun gidan hutuba, arziki inaji ina gani kumin bakin cikin samuba" taja tsaki tawuce tabude dakinta ta shige tana ihu tace "kuma wlh nabaki minti goma kiyi salla kizo nan wurin, gobe yar buzu zata zo tafara miki gyaran jiki" da gudu Hamida ta shige dakinta tafada kan gado wani irin kuka neyazo mata sai maimaita kalman aure take abakinta tama kasa yarda wai ita za'ama auren, to wani irin aure ma, Aadil, ita ta shirya aure ne yanzu?

Tayaya zata auri Aadil ma?

Haka taci kukanta takoshi saida Kaka ta kwala mata kira sanan ta tashi ta shiga bayi ta daura alwala tafito tahau kan dadduma tai salla sanan tawuce dakin Kakan tana goge kwalla.
Chapter 42 · 0% Book details