← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 69

Sashe 28

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani hadadden daki Aabid ya shimfidar da ita kan makeken gadon dake dakin yana kallon fuskarta, tsugunnawa Aadil yayi gefen gadon yana kallonta shima idanunshi yay jajir, ahankali Aabid yajuyo da kanshi yana kallon yanda Aadil ke kallonta yana leka fuskarta, runtse idanunshi yayi da karfi yanajin ciwo aranshi sosai, daidai lokacin Mami ta shigo dakin karasawa tayi gaban gadon ta zauna ata saitin kafafun Hamidan tana kallon fuskarta tace "ga Dr nan zuwa ya dubata Baba yakira shi, Aabid stay with her karta tashi bakowa" ta kalli Aadil dake wani irin kallonta tamikamai hannu tana murmushi tace "come Aadil, muje kai wanka and change this cloth, kaima Dr zai dubaka inyazo duba friend dinka" make mata kafada yayi yana hararanta a shagwabe yace "she's my wife" shiru Mami tayi tana kallonshi saikuma tai murmushi tace "naji, muje kayi wankan to kafin kafito nahada maka abinci" tashi yayi ahankali kanshi narawa yana kallon Hamidan tashi itama Mami tayi taja bargo ta lullubeta dashi tarike hanun Aadil suka fice suka rufo kofan, wani irin runtse ido Aabid yayi yafuzar da iska kafin yadaura hanunshi kan zuciyarshi yana dukan zuciyarshi yay hakan kusan na 2min sanan yadawo daidai, zama yayi agefen gadon yay shiru yana wani irin kallon fuskarta, dawani irin murya mai rauni sosai yace "tayaya kika hadu da brother na Jewel?

I'm the one for you Amatullah" yay shiru yana kallon fuskarta, knocking da akayi yasa yatashi yay wurin kofan bude kofan yayi Dr ne da Baffa suka shigo dakin, Baffa yace "yauwa gatachan likita adubata" karasawa Dr yayi bakin gado yaduba ta sanan yaciro drip daga katon jakan hanunshi yamata fixing yay allura aciki wurin 15 minutes yabata akanta sanan yajuyo ya kalli Baffa yace "fever ne kawai, i guess tsoron kune yasta ta suma, yanzu dai komi lpy dazaran drip dinan ya kare aciremata and yanzu dai bacci take zuwa anjima chan haka zata farka" murmushi Baffa yayi yace "masha Allah itace taga jikana ta taimaka mai, muje kadubamin jika" wucewa sukayi suka fita daga dakin Aabid yadawo ya zauna.

Duba Aadil Dr yayi yarubuta magungunan daza asayomai sanan yamai allura da kyar ya yarda akamai, yaci abinci nan wani baccin gajiya da wahala yay gaba dashi shima.

Saida yay bacci sanan Mami tarufa mai bargo takashe wutan dakin nasu tarage karfin Ac tafito, dakin da Hamida take tawuce ahankali tabude kofan har lokacin Aabid na zaune agefen gadon yazuba mata ido, budewan kofan dayaji yasa yadago kai, murmushi Mami ta sakinmai takaraso ta zauna kusada shi, ahankali yadaura kanshi kan kafadarta ya sauke ajiyar zuciya, shafa kanshi Mami tayi tace "menene Son?" dan murmushin yake ya kakalo mata yace "babu komi Mami na" dagashi tai daga kafadarta ta kalli fuskarshi jin yanda yay maganan danta tabbatar da abinda ke damun shi, lumshe ido yayi da sauri dan yasan tsaf Mami zata gano da damuwa a idanunshi, ahankali kira sunanshi.

"Aabid" bude idanunshi yayi ya kalleta, nunamai Hamida tayi da ido tace "you called her Amatullah dazu kasanta ne daman?" shiru yayi yana kallon fuskar Mami kaman bazaice komiba saikuma yace "eh nasanta a Lagos nataba ganinta tafada ruwa nacirota nakaita asibiti daganan bankara ganinta ba saiyau" murmushi Mami tayi tace "Allah sarki, hala saisa itama ta taimaki Aadil maybe tazaci kaine" murmushi tasakeyi tasake jan kumatun shi tace "tashi muje kaci abinci idan ta farka sai a gaggaisa da kyau amata godiya saimu maidata gidansu ko" gyadama Mami kai yayi yatashi suka fita daga dakin, dining ta kaishi tazubamai abincin kadan ya iyaci sanan yakoma ya zauna a falon yana kallon CNN amma gabaki daya hankalinshi nakan dakin da Hamida keciki.

Kiran sallan azahar dayaji yasa yatashi yafita masallaci hakanan yakejinshi wani iri yarasa mesa kalman da Aadil yafada saimai yawo yake a kunne.

"Hamida my wife" runtse ido yayi da karfi da kyar ya lallaba ya shiga masallaci yaje yay salla sanan yadawo ya bude kofar dakin datake har lokacin bacci take, maida kofar yayi yarufe yakoma kan kujera ya zauna har akai la'asar yasake dawowa ya lekata har lokacin bacci take yakoma kan dogon kujera yasake zama yana chanza tasha zuwa tashan kwallo.

Bude kofan da akayi yasa yadago kai Aadil ne ke saukowa yana sanye da plain white t-shirt dakuma wani black 3quater sai uban kamshi yake yay wani irin kyau da inka kallai saika kara, hanunshi rike da manya manyan chocolate guda biyu acikin ledan su, Aabid daya gani azaune yasa ya washe baki yataho da sauri yana tsalle tsalle, shiru Aabid yayi yana kallonshi shi kanshi baisan meka damun shi ba hakanan yaji yanajin haushin shi bana wasaba yakasa manta kalman Hamida my wife dayafada aranshi, inda dane all this tsalle tsallen dayake yi idan yaganshi yanajin dadi amma yau sosai yakejin haushin shi, fadowa jikinshi da Aadil din yayi yasa yadan fuzar da iska yatureshi kadan, dago kai Aadil yayi yaleka fuskarshi yana murmushi, dan murmushin yake Aabid ya sakan mishi ya lumshe ido batare dayacemai komiba, hakan yasa da sauri Aadil ya kalli chocolate din hanunshi dudda ya daukoma kanshi ne da Hamida amma saiya mikamai daya da sauri yace "Bid" dan bude ido Aabid yayi ya kalleshi ya kalli chocolate din dayake mikamai, girgizamai kai yayi yatureshi murya chan kasan makoshi yace "stand up from my body" kin tashi yayi yay shiru yana kara leka fuskanshi kaman maiso gano abinda ke damun shi wani irin tsawa Aabid ya dakamai tareda tureshi da karfi daga jikinshi yace "nace katashi daga kan jikina ko" yay maganan yana tureshi dawani irin fushi yafadi akasa, atsorace Aadil ya kallai dan idan da abinda ya tsana a duniya yakuma kejin tsoro bai wuce tsawa ba, tsaki Aabid yayi cikin fushi yatashi yana kakkabe shaddar jikinshi da Aadil ya yatsine yawuce yafita daga dakin, binshi da kallo Aadil yayi idanunshi nataruwa da kwalla sosai, ahankali ya lankwashe kafa anan kasan falon ya shiga kuka yana share ido yana kallon kofan, kukan shi da Abie yaji yasa ya shigo dakin da sauri dan shigowan shi kenan gidan, karasowa yayi inda yake zaune akasa arude dan kowa nagidan nan ya tsani yaga abu nadamun Aadil yace "menene?

Why are you crying" kasa bama Abie amsa yayi sabida yanda Aabid yaturashi kemai ciwo baitaba mai hakaba, da sauri Abie yaciro handkerchief daga aljihun shi ya sharemai bakinshi da fuskarshi yace "wai menene?

Why are you crying haka?" kasa magana yayi sai kukan dayake yi sosai, sallama Baffa yayi ya shigo shashin da sauri daidai lokacin itama Mami tafito dan dama wanka take, da sauri Baffa yakaraso yana dogara sanda ya kalli Abie yace "me kuka mishi wai?

Yaufa yadawo harkun fara sakashi kuka, dan Allah kome yakeso kudinga mai gobe za'a faramai maganin, daga sokoto mai maganinshi dana kira zaizo" ya zauna akan kujeran dake saitin Aadil din dake kuka sosai yake yadafa kanshi yace "menene?

Waya tabamin Hassan iyye?" makemai kafada Aadil yayi cikin kuka yana turomai baki yace "my name is Aadil right Mami" dariya dukansu sukayi harda Baffan yace "dan tselen uwa gadai ubanka nan katambaye shi da aka haifeka Hassan aka yanka rago aka sakama, yanzu dai dena kuka kaji, zomuje mu baga basket ball" yay maganan yana zazzago glass din idanunshi cike da tsokana, Mami murmushi tayi ta tashi ta wuce kitchen dan kawomai fruits din data yankamai ta sakamai a fridge.

Makema Baffan kafada yayi yana turo baki yana goge hawaye da bayan hanunshi dayake rike da chocolate da sauri Abie ya karbi chocolate din yace "kawo nan karka tsole idanunka dasu" turoma Abie baki yayi sanan ya kalli Baffan dake kallonshi yana murmushi ya makemai kafada yace "you don't know how to play basket ball bazan buga dakai ba, i will only play with Bid ko Abie" ya kalli Abie dayay shiru yana kallon d'an nashi feeling wani irin guilt, murmushi Abie yayi ya mikamai chocolate din yace "hakane, nabude ma chocolate din?" gyadamai kai yayi ahankali hakan yasa Abie yabude mai daya ya mikamai, karba yayi yakai bakinshi ya gutsura yanaci kallonshi Abie yayi kafin yatashi ya shafa kanshi yawuce yafita dan yanda yakeji yasa bazaima iya shiga gidan ba yawuce ya shiga motarshi yafita daga gidan, binshi Baffa yay da kallo ganin damuwa akan fuskarshi amma bai kawo komiba dan yasan damuwan bazai wuce ta Aadil bace, taba keyan Aadil yayi hakan yasa Aadil yajuyo ya kalleshi, gefenshi Baffa ya nunamai hakan yasa ya murgudamai baki sanan yatashi ahankali ya zauna a kusa dashi, hannu Baffa yamika mai yace "bazaka sammin ba" wanda yakeci ya mikamai hakan yasa Baffa ya makemai kafada kaman yanda yakema mutane yace "ni kabani wanchan sabon shi nakeso" makemai kafada Aadil yayi sosai yace "this one is for Hamida my wife" zaro ido Baffa yayi cikeda wasa yace "wife kuma Hassan" gyadamai kai yayi da sauri yana washe baki yace "yes i will marry her, she will be my wifeee, just like Abie and Mami" yakarashe maganan awani irin sangarce yana murmushi yana fari da ido sosai, shiru Baffa yayi yana kallonshi yama kasa magana tashi Aadil yayi daga kan kujeran yasa chocolate din a bakinshi ya ballomai yakamo hanunshi yasaka mai aciki yace "bye bye Oldman, lemme go and see My Hamida, Mami" ya kwalama Mami kira kaman zaiyi kuka yace "my fruits" fitowa Mami tayi daga kitchen tamikamai bowl dake cike da sliced fruits dasukai sanyi sosai da fork ya karba da gudu yana tsalle tsalle yay hanyar dakin Hamida Baffa yabishi da kallo har lokacin maganan da Aadil din yayi na ringing akanshi saikuma yay murmushi yaciro wayarshi daga aljihu yatashi yana dogara sandarshi yafice daga dakin yaje rumfan da akamai musamman ta zama ya zauna yay dailing wata number.
Chapter 28 · 0% Book details