← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 69

Sashe 33

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"baki taba sanin yan biyu bane bako?" taji magana akanta da sauri ta dagokai Mami ce ta shigo dakin wayansu masu aikin gidan biye da ita guda biyu suna dauke da tray a hannu, nuna masu gabanta Mami tayi tace "ku ajiye anan" ajiyewa sukayi suka wuce suka fita daga dakin sukamaida kofa suka rufe, ahankali Mami ta zauna a gefenta taidan murmushi ta kalli fuskar nata tace "twins ne wanan ne babba shine Hassan" ta nuna Aadil dake bacci tadan shafa kanshi tai shiru jin jikinshi da zafi, ahankali ta janye hanun tace "dayan kuma shine Aabid, dukansu haka sukeda zuciya barin ma wanan" ta nuna Aadil tace "yauma bansan meya faruba, dan Aabid dawuya kiga fushin shi, inata miki surutu ko baki fadamin ba ya sunanki?" ahankali kanta akasa tana wasa da yatsun ta dan hakanan taji tanajin kunyan matan tace "Hamida" ahankali Mami tace "suna mai dadi amma asalin sunanki kenan?" girgiza mata kai tayi tace "sunana Amatullah" "masha Allah wat a nice name, wani mataki kike a karatu?" wasa ta shigayi da yatsunta tace "100 level Islamic studies" "masha Allah, oya ci abinci karya huce kinji daughter na" gyada mata kai tayi ta kalli uban tilin abincin tarasa mema zataci da kyar ta mika hannu tadau spoon ta dau plate hanunta na rawa takasa diba, ganin haka yasa Mami ta karba tace "kawo nai serving dinki tunda kunyana kikeji" zuba mata white rice din Mami tayi a plate tazuba pepper soup din asama ta mika mata ahankali ta karba tace "Allah amfana" murmushi Mami tayi dan taji dadin addu'an tace "Ameen Amatullahi" diban abincin tayi tai Bismillah takai baki duk Mami na kallonta tana yaba natsuwan yarinyar da kyar ta iya tai 5 spoon sanan ta ijiye ta dau ruwa tasha batare data taba juice din wurinba tace "nakoshi nagode zan tafi" "kai dan Allah daughter bakici dayawa ba" girgiza mata kai tayi tace "nakoshi" gyadamata kai Mami tayi tace "Tom ina zuwa bari nazo saimuje mu saukeki daganan mayima iyaynki godiya" gyadamata kai tayi gabanta na faduwa, fita Mami tayi daga dakin ba jimawa yan aiki suka shigo suka kwashe kayan abincin, juyawa tayi tasake kallon Aadil dake bacci hakanan taji bataso ta tafi ta barshi tasan idan yatashi saiya nemeta, kafeshi tayi da ido tana kallonshi daidai lokacin Mami tabude dakin da sallama ta shigo kallon Mami tayi, Mami takarso ta mika mata wani hadadden black gyale tace "gashi ki yafa" karba tayi kanta akasa tace "nagode Mum" murmushi Mami tayi batare datace komiba, ahankali tamike tsaye ta yafa gyalen kaman yanda taga su Zainab nayi sosai gyalen yamata kyau Mami tace "masha Allah yako miki kyau, muje" gyadama Mami kai tayi Mami tai gaba tana binta abaya harsunkai bakin kofa takasa daurewa saida tajuyo ta kalli Aadil din dake bacci sosai da sauri ta goge hawayen dake neman zubo mata tasakai tafice tarufo kofan ahankali suka fito tsakar gida sai sunnar dakai take Mami ta bude mata bayan mota ta shiga ta zauna Mami ta zauna agaba Abie yatada motar yaja sukabar gidan, sosai gabanta ke faduwa itato ina zata kaisu yanke shawara tayi gidan Anty Lami haka tadinga nuna musu hanya har zuwa gidan Anty Lami dake ta wuraren gwamna road har zuwa kofar gidansu suka sauko daidai lokacin ana kiran sallan magrib fitowa sukayi daga motan Abie yarufe motan ya kalli Mami yace "ku shiga ciki bari in shiga masallaci" ya mikama Mami key dan akwai abubuwa acikin boot din, yanda ta tsaya gefen Mami kanta akasa tana wasa da yatsunta yasa Mami tace "muje daughter" gyada mata kai tayi tabude kofar gate din ahankali ta shiga Mami biye da ita.

Babu kowa a hadadden tsakar gidan sai tulin textbooks dake kan wani table da alamu yaran homework suke sun tafi masallaci, sallama tayi ahankali tabude falon ta shiga babu kowa ciki ta kalli Mami dake tsaye tana kallonta tace "ki shigo Mum" gyadamata kai Mum tayi tai sallama ta shiga ta zauna akan kujera hakan yasa tai ciki da sauri sallama tayi agaban dakin Anty Lami daidai lokacin anty Lami na sallame salla ta juyo da sauri ta ware ido tana kallonta daga sama har kasa takama haba cikeda mamaki tace "Hamida!" kasa amsawa Hamida tayi saima kasa datai da kanta tana wasa da yatsunta, cikin mugun takaici Anty Lami ta tashi daga kan dadduman tana gyara daurin zanin jikinta tace "ba magana nake mikiba kinyi shiru tun safe mahaifiyar ki ke kirana taji kokinzo nan bakizo ba Hamida, ina kikaje kodai mazan kika farabi da gaske?

Ina kikaje Hamida" girgiza matakai tayi ahankali tasa bakin gyalenta ta share hawayen dasuka zubomata, tsayawa kallonta Anty Lami tayi ta rungume hanunta akan ciki cike da mamakinta tace "hala namiki wani abune dakike min kuka?" girgiza mata kai tayi ahankali.

"to menene?" cikin muryan kuka tana goge ido tace "ana nemanki a falo" zaro ido Anty Lami tayi tace "wakika kawomin gida?" tai maganan tana zuwa hanyar falo da sauri ta yaye curtain ganin kamilalliyar mace cikin shiga ta alfarma zaune akan kujera tana fira da yaranta maza guda uku su Ra'is dasuka dawo daga masallaci tana murmushi yasa tasaki labule da sauri ta kalli Hamidan dake gefen ta tace "ke wacece wanan ni yatsu?

A ina kika samo wanan hajiyan Hamida?" ahankali tace "nima bansan suba, maman yaron ne" da sauri Anty Lami tace "yaro?

Au wai wanda aka ganku tare?" gyadamata mata kai tayi ahankali da sauri Anty Lami ta yaye curtain tafita fuskarta cikeda murmushi tace "barka da zuwa" dagokai Mami tayi da sauri ta mike tsaye, da sauri Anty Lami ta nuna mata kujeran tace "please sit, ki zauna dan Allah" zama Mami tayi ahankali tace "ina yini ina gajiya" cikeda fara'a Anty Lami tace "Alhamdulillah, maraba, sannu dazuwa, Hamida" ta kwalama Hamida kira ta kalli yaran nata dake kallon cartoon tace "kutashi kutafi dakinku, ku kiramin Hamida daga nan" tashi sukayi sukai ciki ba'a jimaba Hamida tafito kanta akasa Anty Lami tace "je kawo drinks da snacks mubama bakuwar mu ko" da sauri Mami tace "haba haba wlh bakomi dama har gida nazo namuku godiya akan karamcin da Amatullah daku kukama d'ana mara lafiya nagode, nagode, ubangiji Allah saka da alkhairi" daidai lokacin mijin Anty Lami ya shigo tareda Abie aka zazzauna ana gaggaisawa Hamida da kanta ke kasa ta kawo drinks ta ijiye da snack takoma ciki, ruwa kawai Mami tasha Abie kuma sai hira yake da mijin Anty Lami kaman sunsan juna nan Mami tabama Anty Lami labarin yanda Aadil din yafita daga mota haryasa tai hatsari, sosai Anty Lami ta tausayama yaron dudda bata ganshi ba sai bayan sallan Isha sanan sukai sallama Anty Lami ta kwalama Hamida kira.

"Hamida" fitowa tayi kanta akasa Anty Lami tace "zasu tafi" dan dagokai Hamidan tayi ta kalli Mami a kunyace tace "Allah ya kiyaye hanya Mum" murmushi daga Mami har Abie sukayi sukace "mungode Hamida" suka wuce suka tafi har gate suka rakasu sanan suka dawo ciki ko minti daya basuyi da zama afalo ba wasu yara suka fara shigo da kaya niki niki wasu manyan ledoji ne guda uku na hadaddun turare da gyaluluwa, saikuma na atampopi guda uku da lace guda uku, dayan kuma na su chocolate da lot of cookies da sauri Anty Lami tace "inaa gaskiya bazamu karbaba haka akeyi" binsu akayi da kayan amma har sun tafi haka aka dawo da kayan.

Wanka tayi adakin Anty Lami takawo mata wani free doguwan riga blue tace "gashi nan kisa inkin gama kizo dakin Abban su yana nemanki" tajuya tafita, ahankali takarasa gaban madubin dakin tadau man Anty Lami ta lakato da hannu ta kalli Madubin zata shafa fuskar Aadil tagani ajiki yana turo mata baki yace "why did you leave me?" da sauri ta juyo ganin babu kowa a wurin yasa taji wani irin sanyi ajikin ta, jikinta yay wani irin sanyi taji jikinta dukya mutu, ahankali ta juyar da kanta tafara shafa man ajikinta kaman ance ta kalli madubin, Aadil tagani ta madubin yana mata kuka ahankali yana mata alamu da hannu datazo cikin kuka sosai yace "please come back Hamida my wife, I need you in my life, u promise you will not leave me" da sauri tasake waigawa ta kalli bayanta babu kowa a wurin wani irin fadawa kan kujeran gaban madubin tayi ta kifa kanta akan slap din madubin jikinta yay wani irin sanyi, kwala mata kira da akayi yasa ta dago kanta da sauri tace "gani nan zuwa" man dabata shafa ba kenan ta tashi ta dau doguwar rigan ta zira tafita.
Chapter 33 · 0% Book details