← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 69

Sashe 26

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"fo, fo, fo" Cikin tsananin fushi Kaka tace "kagani ko Sama'ila Hamida tadawo karuwa, kutashi ku fitarmin daga gida" tadau tsintsiyar kwakwa dake gaban dakin Hamida tayo kansu, da sauri Aadil yasaki hanunta yaja Hamidan yasata ajikinshi yamata rumfa yana kuka sosai cikin turenshi dayafi kwarewa akai yace "stop beating my wife, stop, stop, mugu, mugu" rufeshi da duka sosai Kaka tayi da tsintsiyar tana haki yana ihu, tako ina take kaimai dukan yaki sakin Hamidan, Hamidan itama tana kuka dan yanda Kaka ke dukanshi yana kuka har cikin zuciyarta takeji, cikin fushi sosai Kaka tasaki dan ragowan tsintsinyan daya rage a hanunta dan dukya katse a jikinshi tace "kubarmin gidana, kutashi kubarmin gidana, kubarmin gidana" Kaka ta hankadashi, da kyar ya mike tsaye yana rike da Hamidan har lokacin yana kuka ba'a taba dukanshi haka a duniyan nan ba, Kaka tawani irin tura keyanshi tana dukan bayanshi tarakasu da duka har wajen gate suka fita daga gidan.

Binsu da kallo yan mutanen anguwan dake waje sukayi sabida yanda Kaka ke dukansu sanan tajuya takoma cikin gida ta rufe gate taciro wani karamin makulli daga lalitar ta ta kulle gate din tana masifa tana haki tace "inga mai fita daga gidan nan yau" taja kujera ta zauna anan gaban gate din tana karkada kafa tana kokarin ballan namijin goron data ciro daga lalita saikuma tafashe da kuka tana nuna kanta tace "Hamida, Hamida" tai kwafa tace "kinma kanki, uwarki kika cima mutunci bani ba".

Ahankali tazare jikinta daga nashi cikin kuka sosai tawarware dan kwalin kanta dakeda girma sosai ta yafa ajikinta, hanunta yakara rikewa yana kallo yasa dayan hanunshi yagoge hawayen dayake yi dayaki dena tsiyaya yace "you are hurt, u are bleeding, those people are wicked" ahankali ta share idonta ta kallai yanda yake kuka sosai gashi sai kallonsu ake, ahankali cikeda jarumta tace "stop crying, am fine" kallonta yayi da jajayen idanunshi itama shitake kallo asanyaye, lumshe ido yayi wasu hawayen suka sake xubowa yace "i will tell Mami and Bid saisun rama miki" yasake kai hanunshi kan idanunshi yana kuka sosai, murmushi tamai taji wani irin tausayinshi tace "stop crying people are looking at u, let's go" gyada mata kai yayi ahankali miyau na xubowa, sosai yawani irin bata tausayi ga wuyanshi da kafadarshi duk shatin tsintsiya, ahankali tasa bakin gyalenta takai saitin bakinshi ta share mai miyan bakin, lumshe ido yayi hawaye suka zubomai, asanyaye tazare dan kwalin daga wuyanshi tace "i said you should stop crying" gyada mata kai yayi yabude idanun dake cike da kwalla ya daurasu akanta da sauri ta dauke kai sabida yanda taji idanunshi sunsa gabanta yafadi sosai ta daga kafa zatai gaba yariko hanunta gam da sauri ta juyo ta kallai suka sake hada ido yasakin mata wani irin kuka mai tsuma rai, da sauri tace "menene why are you crying?" kallonta yayi cikin kuka sosai kanshi da kirjinshi namai zafi sosai baimasan meyake jiba yakasa magana, dan matso wa tai kusadashi tace "menene?

Tell me" kafeta da ido yayi yana kuka batare dayah magana ba, cike da damuwa idanunta sun ciko sosai da kwalla tace "tell me Aadil menene?" ahankali yana kallonta da idanunshi dasukai ja suna kyallin hawaye yace "I love you Hamida my wife".

IN BANI
Maman Abd Shakur
22....
_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi pay anan ko pay achan_
_in kinaso novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_Zaki iya turo MTN card 300 ta watsapp number 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_
Ko motsi kasawa tayi jin abinda yafadin mata saima wani irin kallon idanunshi datakeyi, ahankali yakamo hanunta yana kuka yana lumlumshe mata ido gwanin ban sha'awa yace "i love you Hamida, and we will marry just like Mami and Abie right?" shiru tayi takasa magana jikinta yay wani irin shegen sanyi tundaga yatsar kafarta, lumshe ido yayi yasake budesu ya kalleta araunane kafin yasakin mata wani irin kuka, ta tsani taga yana mata kuka, sosai kukan shi ketaba mata rai, da sauri ta gyadamai kai tace "yes" wani irin ware mata manyan eyes dinshi yayi yace "yes Hamida my wife, she will marry me like Abie and Mami na yay" yay maganan yana mata fari da ido yana juyawa, tsayawa tayi tana kallonshi sosai taji tana wani irin tausayin shi to wai mutunmin dayake da lafiyan shi meya dawo dashi hakane?

Meya maidashi haka?

Hanunta taji ya fizgo yace "lets go, bazamu koma dat mugu house bako" ahankali ta karbe hanunta daga rikon dayamata suka cigaba da tafiya, batamasan inda zasuba gashi ko naira daya batadashi tafiya kawai suke yana mata surutu yana kirga hanunshi yana nuna mata yana murmushi, sosai yake wani irin farin ciki yana murna sabida tacemai yes sai tsalle tsalle yake akan hanya yana kallon fuskarta, duk in sukazo wuce bishiyan fulawa saiya katso yabata, karba kawai take tana murmushi amma matsalan datake ciki yawuce tunaninshi.

Gidan data boye jiya sukaje, atare suka shiga yana tsalle tsalle, pure water data gani awurin tadauka da sauri ta bude tai alwala, Aadil dake tsalle tsalle shima yazo da sauri ya tsugunna yana kallonta sai leken fuskarta yake, turo mata baki yayi yace "me too zanyi alwalan" zaro ido tayi ganin saura dan kadan ruwan, mikamishi tayi da sauri ya karba yana murmushi yace "thank you my wife" yafada yana nuna kanshi yana wani irin fikifiki da idanunshi dimples dinshi na lotsawa, tashi tayi da sauri batason tana kallonshi inyana mata irin abubuwan nan dan wlh wani irin kyau da kwarjini yake mata bana wasaba, karasawa dan filin dakin tayi ta gyara kasan wajen da hanunta sanan ta yafa dan kwalin kanta da kyau ajikinta ta kabbarta salla sai alokacin taji zuciyarta yarage mata nauyin dayake mata na kunci da azaba sosai, yay wani fayau kaman an kawad da damuwanta, salla tayi tai addu'a Allah ya bayyanar da yanuwanshi burinta kawai bai wuce yaga yan uwanshi yatafi gidaba ita saita tafi gidan Anty Lami yayar Mama, zuwa yayi shima ya tsaya a gefen ta yafara sallan murmushi kawai tayi tacigaba da addu'oin datakeyi.

Jinginar da bayanta tayi da bango ta daura kanta akan guiwowinta tai shiru idanunta sun cika da kwalla sosai, alamun mutun dataji akanta yasa tabude ido ahankali, hada ido tayi da Aadil daya leko da kanshi yana wani irin kallonta, ganin yanda hawaye yacika idanunta yasa duk yabi ya damu, zama yay a gefenta ya daura hanunshi akan kadadarta yawani irin dago kanta daga jikin kafafunta da karfi, kallonshi tayi shima kallonta yake ya daure fuska sosai, akumbure yace "why do you want to cry?" dan lumshe ido tayi da sauri tana kokarin ture hanunshi daga kafadarta takasa sabida yanda yarike ta gam, jiyayi kanshi yadau zafi da sauri ya fada jikinta yakai fuskarshi saitin nata, arude tabude idanunta dake gab da zubar da kwalla tace "Aadil kadena stop, kasakeni" makemata kafada yayi yakai hanunshi ya daura akan saman idanunta yana leka idanun kaman maison gano wani abu, murya chan kasa yace "you want to cry" girgiza mai kai tayi zuciyarta namata rawa sosa tace "n...no Aadil am not cr..crying, kaga....ni" saikuma tasaki kukan da karfi sosai sabida yanda zuciyarta kemata zafi, bamatasan tasaki kukan ba kawai kukan ne yazo uncontrollably, Kaka ta koreta daga gida batada gida ina zata, rudewa Aadil yayi sosai dan yatsani yaga ana kuka barinma na Hamida dayakeji har kasan zuciyan shi, wani irin rungume yayi yasata ajikinshi yana jijigata muryanshi shima narawa sosai yace "d...on't cry, i will call police for them, they will arrest them, they beat you and injury you i will go with police and beat all of them, stop crying Hamida" yanda yake maganganu dabama ta ganewa dan dukya rude muryanshi narawa sosai yana breaking kaman shima yana shirin kukan yasa tai shiru tana tureshi tana kokarin tashi daga jikinshi, make mata kafada yayi yana kallon idanunta dasukai jajir sun kumbura sosai, hanunshi dake rawa sosai yakai kan fuskarta yay cupping face dinta yana share mata hawayen dake kan fuskar yana yana turo baki kaman zai fashe da kuka yace "i will beat them for beating you, stop crying, don't cry again kinji" gyadamai kai tayi ta hadiye duka kukan datakeji tamai murmushi tace "am fine" ahankali yana kallon idanunta batare dayasaki fuskarta ba yace "are you sure?" gyadamai kai tayi tama kasa magana kirjinta na bugawa sabida wani irin kallo dayake mata daya bambanta dana koda yaushe da sauri ta runtse idanunta gam tafara kokarin fita daga jikinshi, make mata kafada yayi yasata a kirjinshi ya kankameta yay shiru kirjinshi nawani irin bugawa, shikanshi baisan meyakejiba kawai yanaso yacire mata damuwan datake cikine, ganin ko motsin kirki takasa yasa dan bebata daman ba yasa tai shiru gabanta na faduwa tana sauraron yanda jikinshi kewani irin daukan zafi heart dinshi na beating da karfi and fast fast...
Chapter 26 · 0% Book details