← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 69

Sashe 68

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

My Aadil stop crying" kama kanshi yayi sabida yanda kanshi yawani saramai kaman zai tarwatse ya yatsine fuska cike dajin azaban sarawan kan, da sauri Aabid ya ijiye system dinshi agefe ya matsa kusadashi tareda daura hanunshi akan kanshi yace "are you okay Aadil bakada lafiya ne?

Kanka kema ciwo?" bude ido Aadil yayi ya kallai ya girgiza mai kai yace "am fine, kaina ke dan ciwo" yay maganan yana kwantar da kanshi kan kafadar Aabid yana sauke ajiyan zuciya ahankali yana tunanin flash din abu daya gani yanzun nan, shiru Aabid yayi kafin ahankali yace "wait lemme go and make coffee for you kasha, namaji u are trying to run temperature" daga kafadar Aabid din yayi, Aabid yatashi yafita daga dakin, yabi bayan Aabid din da kallo ganin ya ramemai sosai tsakanin jiya da yau kaman mai tunanin wani abu, sake lumshe ido yayi yana tunanin Hamida data dagulamai lissafi gabaki daya.

Ko kadan baimaji shigowan Aabid ba saidai karan ajiye mug yaji akan table din gaban kujeran hakan yasa ya dago kai ya kalli Aabid din daya ijiye mug din yana nazarin shi, zama yayi kusada Aadil din yana mikamai wayar dayake hanunshi yace "are you sure you are okay Twin" gyadamai kai yayi ahankali batare daya iya furta wata kalma ba, dafamai kafada Aabid yayi yace "stop thinking about the past Aadil, karungumi kaddara duk yanda tazoma you have us and u have your beautiful wife, matarka yarinya ce tagari, kagode ma Allah kawai and move on okay we are all here to support you, this is a second chance Allah yabaka make use of it, ga wayanka nan Mami tabani nakawo ma" karban wayan yayi ya rungume a kirjinshi yana kallon Aabid din wasu siraran hawaye suka zubo ta gefen idanunshi da sauri Aabid yarikeshi cikeda damuwa sosai kaman zaiyi kuka yace "kaga tell me wats wrong with you, you are driving me crazy Dil, am so worried" girgiza mai kai Aadil yayi yace "i don't know Bid, bansan meke damuna ba, but deep down inaji ajikina kaman zan mutu anytime soon" chak Aabid ya tsaya yana kallonshi ko kyafta idanu bayayi maganganun shi ya mugun dakanmai zuciya bana wasaba, kallonshi Aadil yake ganin yanda yayi yasa yabude baki zaiyi magana asanyaye Aabid ya daura hanunshi kan bakin nashi yana kallonshi cikin daure fuska yace "are you mad eh Aadil?" yay maganan yana kaimai duka a kafada idanunshi natara hawaye, yace "are you mad eh?

Mesa kakemin maganan mutuwa?

And wayafadama yanzu zaka mutu Allah shine masanin gaibu, i just got you back karka karamin maganan mutuwan ka idan kasake bazan karama magana ba kaji ko" yay maganan hawaye na gangaromai daga ido gyadamai kai Aadil yayi yana kokarin tsayar da hawayen dake fitomai daga ido rungumeshi Aabid yayi yamai kiss a goshi yace "koma mekakeji u are not alone, we going to go through it together Aadil, kaine kadai dan uwan daya ragemin yanzu banson in rasaka" ahankali Aadil yace "me too Bid" "let's go out, zomuje muyi many many things outside and have fun zakaji dadin jikinka, tashi jeka shirya kazo" kallon fuskar Aabid din yayi ahankali yamika ma Aabid din hannu hakan yasa Aabid din yabi hanunshi da kallo kafin yasa nashi acikin hannun ya kalli Aadil din kaman yanda yake kallonshi, a natse Aadil din yace "meke damunka?

Something has been bothering you i can feel it a zuciyata kana cikin matsala wat is it wat is the problem?

Your problem is our problem ko Bid we are one, you've been thinking tun jiya banso kamin karya just tell me menene?

Meke damunka?"
Girgizamai kai Aabid yayi yana danne zuciyarshi dankar ya fahimci komi game dashi, ahankali yace "bakomi kaina keta ciwo last night saisa nai wani iri" kafeshi da ido Aadil yayi dan bai yarda da maganan shi ba ko kadan hakanan zuciyarshi taki natsuwa taki aminta da maganganun, ganin yanda Aadil din ke kallonshi yasa yatashi da sauri yay bathroom yana tafiya ahankali yace "lemme shower kaje ka shirya kaima" yabude kofar bathroom din ya shiga yarufe, binshi da kallo Aadil yayi dan yanda yayi yanzu yakara tabbatar mai da wani abune ke damunshi ba ciwon kaiba da sauri yatashi sabida yanda yaji zuciyarshi taki natsuwa ya shiga duba dakin, pillows din gadon ya daddaga amma baiga komiba, side drawer ya bubbude nanma baiga komiba, wayar Aabid din daya gani akan gado ya dauka yana budewa yaga ba password hakan yasa ya shiga dube duben wayan amma baiga komiba harzai ajiye wayan yaga watsapp message ya shigo daga Dr Sham "get well soon" da sauri ya shiga watsapp din yabude Dr Sham din, maganan Aabid ya gani kafin reply din Dr Sham " _na am fine now Dr i took d drugs"_ da sauri ganin baida lafiya ne da gaske yasa yay scrolling sama dan yaga meke damunshi, idanunshi ne ya sauka akan maganan Dr yace _"you haven't told me the problem, Hussain u are too young to be suffering from heart disease!"_ wani irin faduwa gabanshi yayi ganin heart disease da sauri ya zauna kan gadon yana dafe kirjinshi dake bugamai way too fast, ya shiga reading chat din ahankali daya bayan daya.
_"i used to be a bad boy Dr, inabin mata, ina shan alcohol sometimes su kadaine abinda nakeyi idan rage tunanin dan uwana barin ma idan yana tsaka da ciwo, kullum kuka nake in rasa kwanciya hankali sainaje nasha giya sanan zan manta, my brother, my twin brother is not okay almost every every month saiya kwanta a asibiti, my brother is my life ina sonshi sama da komi aduniyan nan idan kacire iyayen mu, wata rana a Lagos nahadu da yarinyar da i fell for her at a glance, My Jewel!

My Amatullah!"_ chak Aadil ya tsayar da karatun jin sunan Amatullah ahankali ya furta sunan Amatullah, dan yaji su Mum sun kira yarinyar nan na dazu Amatullah, cigaba da karatun yayi..
_"my Hamida!"_ tsayawa Aadil yay chak kanshi yawani irin sara yana ganin flash din fuskar Hamida a idanunshi tanamai murmushi tana kiranshi "My Aadil, stop crying to" dafe kanshi yayi ganin yasoma tuna da yacigaba da karanta message din da kyar.
_"I saved her lokacin datai drowning a ruwa, Dr Sham i love her, i just fell for her naturally, inasonta sosai with all the fiber in my body with all my soul, i love Hamida with all my mind, my heart and soul, and right then bayan nakaita asibiti i confess my love for her cus i understood she was d one for me, mine, dudda she was afraid of me i get to understand that she's a girl that hardly get comfortable around men lemme say mutane ma in general, bayan mun rabu, yan uwanta sunzo sun tafi da ita i was dreaming about her, babu randa zanyi barci na farka banyi mafarkin my Jewel ba, unfortunately my brother as well fell in love, he fell for her as well, funny right yanda twin brothers fell for mace daya, cikin ciwonshi bama tareda ya ganta ba tun amafarki yafara sonta"_ tsayar da karatun Aadil yayi kanshi na saramai komi na dawomai kadan kadan ya dafe kanshi dakemai zafi sosai kaman an kunna wuta.
_"maganan shi alokacin shine take me to she!

She!

Bid she!
Chapter 68 · 0% Book details