← Book details In Bani Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 69

Sashe 61

In Bani Book 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ina Bid?" chak daga Big Mum har Baba Suleman suka tsaya suna kallonshi ganin for the first time in life sunga Aadil yay magana batareda kanshi yay rawa ba batare da miyau ya zuba daga bakinshi ba and magana ba childish magana daya sabayi ba yana turo baki a shagwabe yana fari da ido yana lankwasa kai yana make kafada, tashi Big Mum tayi tafada kasa cikin so much happiness tai sujjada kafin ta tashi tafashe da kuka sosai tana kallon Aadil din dake binta da kallo, kawai takasa holding tears nata back ne, sake zama tayi ta matso kusada Aadil din sosai taima fuskarshi kyakkyawar cupping tace "Aadil, Aadil am I dreaming kaine Aadil, Aadil u are fine kaji sauki wayyo Allah na Yaya am so happy today, kalli Aadil dinmu fa, Alhamdulillah, ya rabb i can't wait to tell kanwata this good news dasu Baffa" tai maganan tana wani irin rungume Aadil dayay shiru yana kallonta kaman mai tunani yanason gano wani abu, karasowa cikin dakin Baba Suleman yayi ya zauna adayan gefen side din Aadil din yana kallon Aadil din today is such a good day hanun Aadil din yakama yarike, hakan yasa Big Mum tace "kagane shi Aadil?" juyodakai yayi ya saukar da manyan eyes dinshi akan fuskar Baba Suleman din ya kafeshi da manyan milky eyes dinshi yana kallo ahankali yace "Uncle" wani irin ihun dadi Big Mum tasakeyi tana goge hawayen datakeyi nonstop tana kokarin ciro wayarta daga jaka da sauri Baba Suleman ya fizge wayan yace "babu wanda zaki fadamawa saidai su ganmu mun da Aadil din kawai, lemme go an call Dr yazo yaduba shi" tashi yayi daga kan gadon daidai zai juya yay wurin kofa idanunshi suka sauka akan Hamida dayagani idanunta biyu tana kallonsu hawaye nafita daga gefen idanunta tana kallonsu da sauri Baba Suleman yace "H...Hamida" yay maganan yana karasawa wurin gadon cikin tsananin farin ciki da sauri Big Mum ta mike tsaye jin sunan da Baba Suleman yakira, karawasa gaban gadon Baba Suleman yayi ya tsaya yana kallon Hamidan ahankali yace "Hamida kin farka?" kafin ma tabada amsa big mum takaraso wajen tana Share kwalla tace "daughter na, Hamida na kintashi" da kyar Hamida ta iya ta gyadamata kai sabida bones dinta dake mata ciwo sosai daidai lokacin Aadil yamike tsaye ahankali yana yatsine fuska ya cizge karin ruwan dake hanunshi ya yar, singlet da 3quater dayagani kan gadon ya dauka yadaga kafa ahankali yay hanyar kofar dakin dayagani wanda ya kyautata zaton na bathroom ne, yanda Hamida tabishi da kallo batare databa Big Mum amsar tambayanta ba yasa Big Mum da Baba Suleman suka juya atare dan suga metake kallo haka, ganin Aadil ne yatashi yana tafiya yabude bathroom ya shiga yasa big Mum tace "Yaya akira mana Dr yakamata yasan sun farka beside Hamida doesn't look good, meke miki ciwo daughter?" fita Baba Suleman yayi dan zuwa kiran Dr, ahankali batare datai magana ba Hamida ta nuna mata fuskarta da jaws dinta alamun su kemata ciwo, a forehead big Mum tamata peck cikin tsananin son yarinyar tace "don't worry zakiji sauki kinji, Maman ki kullum saita kira taji yaya jikin ki, i know she will be very happy idan taji kin farka" shigowa Baba Suleman yayi tareda Dr da nurses guda biyu, kana ganin su kaga larabawa, da farin ciki gabaki dayansu suka shigo suna tambayan ina Aadil Baba Suleman yace "ya shiga bathroom wanka" Dr ya shiga duba Hamida daidai lokacin Aadil yafito daga bathroom din sanye da white single da 3quater ajikinshi yana tafiya ahankali, tafi duka Dr da nurses din suka fara suna kallonshi suna murna ganin patient dinsu yatashi strong and healthy, dan kallonsu yayi kafin ya dauke kai yakarasa yazauna akan wani plastic chair dan yagaji da kwanciya Hamida tabishi da kallo, so kawai take yamata magana koma ya kalleta amma yaki, saida aka gama dubata sanan Dr yaduba shi, babu wata matsala tattare da shi sai rashin kuzari wanda dazaran yaci abinci zai dawo normal, har Dr zai fita Baba Suleman yace "yaushe za'a sallame mu Dr?

Munkosa mutafi gida dasu" dariya Dr yayi yace "i just want to run two scans for Amatullah once d result is clear and fine zanyi discharging naku yau, but before then amata wanka zan turo dietitian yazo yaduba su yafadi abinda zasu iyaci" murmushi Baba Suleman yayi looking satisfy da service dinsu yace "angode Dr" fita Dr yayi nurses biyedashi hakan yasa Big Mum yaye lullubin jikinta ta ijiye akan gadon da jakar hanunta tace "bari naje nahada miki ruwa mai zafi sosai ko kyaji dadin jikinki nazo muje muyi wankan, dan bude ido Aadil yayi kadan ya kallesu kafin yasake lumshe ido abinshi ya kishingida, shiga bathroom Big Mum tayi tahada ruwa sanan ta dawo dakin takama hanun Hamidan tace "yauwa tashi muje daughter na" ahankali Hamidan ta tashi tana yatsine fuska gashin kanta yakara barbajewa ta sauko da fararen kafafunta kasa ta zauna tana runtse ido sabida yanda jikinta ke ciwo bana wasaba kaman Big mum zatai kuka tace "sorry kinji" huta saimu tashi, kai ta gyadama Big Mum tadan saci kallon Aadil dahar lokacin idanushi ke lumshe kaman wanda yay bacci, hanunta da kafadarta bigmum takama tace "yauwa muje" saukowa tayi daga kan gadon ta mike tsaye da kyar jikinta na rawa kaman zata fadi hawaye ya gangaro daga idanunta sai sannu Big Mum take mata takaita gaban bathroom din tabude bathroom din suka shiga, yatsine fuska Aadil yayi dan surutun Mami na damun brain dinshi yabude ido kadan yana kallon kan gadon data tashi daga kai kafin yasake lumshe idon, basu jima da shiga bayin ba Big Mum tafito tabude wardrobe din dakin taciro free plain gown na cotton black mai kama da rigan da sauran abubuwan dasuke bukata da ribbon takoma bayin, sunbata almost 20min sanan suka fito yanzu tafiyarta yadanfi nada dan tanayi ahankali rigan jikinta yamata kyau yakara haskata, big Mum ta zaunar da ita akan gado zama tayi ahankali, daidai lokacin dietitian din ya shigo da abubuwan da zasuci bigmum ta karbi na Hamida Baba Suleman yakarbi na Aadil, sanan Dr yace "Hamida tagama da wuri za'a mata scanning" to Big Mum tace "ta shiga bama Hamida abincin" da kyar ta iya ta karbi abincin tanaci ko kadan batajin dadin komi ganin yanda ko kallonta Aadil bayayi bama ya magana ya lumshe ido kaman mai bacci, tana gamawa nurses suka shigo suka fita da ita dan zuwa scanning big Mum tabisu.

Sai wajen la'asar aka dawo d ita komi is fine babu wani complication, bakaramin dadi su big Mum sukaji ba nan aka basu sallama bayan Baba Suleman yagama clearing komi na bill, big Mum kuma ta shiga hada kayayyakin su she can't wait to see Mami's face dana Aabid idan sukaga new Aadil not baby Aadil.
Chapter 61 · 0% Book details