Sashe 9
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*AUTAR MARUBUTA CE*
__________
_________
__________
_________
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_
<><><
><><><>
<><><>
<><><><>
<><><><><>
<><>
Page 17&18
"Akwai wata sabuwar d'abi'a da d'alubai suka shigo da ita , wanda hakan yana jawo raini da lalacewar tarbiya, to gaskiya ba za mu yadda da wannan abin ba , kuma zamu fara hukunci a yau ga irin wannan d'alubai."
Wani fad'uwar gaba Khadija ta ji ya bugar mata zuciya, ta kalli Laila , amma ita Laila sam babu wannan yanayin a tare da ita
"Mene Uncle ya ke nufi."?
Khadija ta tambayi kanta cikin tashin hankali, Lokaci guda kuma tana tana maida hankali ga Uncle Yahaya da ya cigaba da magana.
" Laila Adam. Fito waje."
Uncle Yahaya ya yi maganar da turanci
Sai a lokacin Laila wani firgici ya sameta ,
tashin hankali ta sami kanta tare da tunani kala-kala, a kan Uncle ko dai ba lafiya yake ba .
Jin ya sake magana ne ya sa ta sake furgita ta fara takowa domin fitowa
Saman gurin ta hau tana raba idanu
"Kun san mene ta aikata." Uncle Yahaya ya tambayi d'alubai d turanci .
Suma cikin irin harshen suka ce masa "A'a."
"Yanzu zata fad'a muku abin data aikata , kuma duk wacce take shirin aikatawa, ita ma hukunci zai biyo baya ."
Shugaban makaranta dake zaune yana saurara ya ce ,"Gaskiya ne ."
Khadija wani yanayi ta shiga na matukar damuwa , haka Laila mamaki ya isheta
Takardar ya amsa wajen shugaban makaranta ya mikawa Laila Adam
Rassss taji zuciyar ta ta bada tare da wani saurin bugawa da take yi
Kallonshi tai cikin tashin hankali ba tare da ta amshi takardarba
"Karbi mana ki karanta musu abin da kika aikata." Yadda ya yi maganar cikin tsawa ya sa ta saurin amsa hannunta na rawa
a lokacin data amsa ya tabbatar mata wannan takardar data yi masa kalaman soyayya ce
"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un. mafarkina nake yi ko zahirin Rayuwata ne." Laila ta fad'a cikin zuciyarta
Wani Uncle Sani ne ya daka mata tsawa da cewa ,"Yi sauri mana bamu da Lokacin batawa zamu shiga aji."
Hannunta rawa yake sosai jikinta na 'bari ta fara bud'e takardar
bayan ta bude ta zuba mata idanu tare da kallon Uncle
Khadija kuwa Allah ne yasan abin dake ranta na bacin rai
da kakkausar murya ya ce ,"Fara mana."
Da malamai da d'alubai duk ita suke saurara ,
ta fara karanta takardar wacce ta kasa riketa da hannu biyunta .
"Assalamu alaikum my Uncle,
fatan kana lafiya kamar yadda nake bukata,masoyin raina ."
Da sauri ta d'aga kai ta kalli Uncle Yahaya da matukar mamaki da wani mummunan yanayi,
wata Aunty ce ta ce ,"Baki ji kunyar rubuta masa ba , sai kunyar karantawa cigaba dallah izina ga masu son aikatawa. "
Laila ta maida kanta ga takardar wanda hawaye suka ciko mata fal har bata iya ganin rubutun da kyau .
"Masoyina kafi na kowa , ina san ka fiye da komai, kai ne dadin duniyata kuma muradina a duk Lokacin da nake cikin damuwa kai ne nake son gani domin yayewarta ,
Ina maka san da baka tunani, son da uwa take yi wa danta, soyayya mara gushewa , abu ne mai sauki zuciya ta ta buga a kanka".
Hawaye ta share yayin da wasu masu yawa suke zubo mata suna sauka a kan takardar
idanunta sun yi jajir , jijiyoyin kanta duk sun tashi ,
ita ma Khadija ta shiga wani yanayi
" Bani da burin barinka domin kai ne mahadin zuciyata,
Rayuwata taka ce , na yi tanadin kauna da soyayya saboda kai ,
bada kwakwalwa nake son ka ba , bada zuciya nake son ka ba , da raina nake kaunar ka , Ina tunanin ka da kwakwalwata , ina rikonka da zuciya."
Kuka ta sake fashewa da shi mai matukar ban tausayi kowa ya yi shiru yana sauraranta
Khadija kuka take kamar ba gobe
Laila kam wani jiri take ji yana dibarta , tana kallon takardar idanunta amma bata iya ganin komai
Sai ji suke timmmm Laila ta fadi kasa , ko shurawa ba tai ba
Da gudu Khadija ta nufo ta tana kuka
haka malamai duk hankali ya tashi
"Dama tana da aljanu ne." Shugaban makaranta ya fad'a
Cikin tsananin fusata Khadija ta nuna shi da yatsa tana cewa, "Zaka ga aljanu , ko numfashi bata yi , Allah ya sa ta mutu."
Ta fashe da kuka
"Ke shugaba kike fad'awa wannan maganar." wani a cikin malamai ya fada
Yayin da sauran malamai suka fara kora d'alubai aji
Lokacin da malamin lafiya ya zo aka duba Laila, amma ya tabbatar musu sai an tafi asubiti
a sannan shugaban makarantar ya tabbatar ya ya yi kuskuren barin wannan abin da ya faru
Kneel down aka sa Khadija a gefe guda yayin da suke shirin kai Laila asubiti
mikewa tai Khadija ta nufi hanyar fita daga makaranta da gudu tana kuka ta nufi gidansu Laila
yayin da duk malaman mamaki ya matukar kamasu da fitar ta
hakan ya sa aka tura malamai mata biyu suka bita, domin a zatonsu aljanu ne
Bayan sun isa asubiti aka kwantar da Laila dake asubitin gwamnati ne kuma babu wadatattun ma aikata
likita daya aka samu ya yo kanta .
Khadija tana shiga gidansu Laila ta sanar da mahaifiyar ta , ita ma da sauri tayiwa Barrister waya
kafin ka ce komai sai ga shi ya dawo cikin tashin hankali
sauran malaman da suke tafe da Khadija suka nufi asubitin
sakamakon barrister Adam yana zuwa matarshi da Khadija ya dauka suka tafi .
Yana zuwa ya ga da gaske Laila ce cikin mummunan yanayi, bai ce da kowa uffan ba ya dauketa ya sata a mota .A Lokacin malaman suka ringa kokarin yi masa magana , amma babu wanda ya kula a cikinsu ya shiga mota ya nufi babban asubitin yayanshi . Suma suka bi bayan shi.
Tom ni Fatima Abdallaah kano
Ina sanar daku akwai masu yawo suna 'bata mata suna
wato ana bud'e group na batsa na iskanci ana dora novels din mu jikin wannan link ana share.
zaki shiga d nufin samun novels, tom sai ki ga ba haka ba
dan haka muna sanar d ku ba mu bane ba kuma zamu yafewa wanda suke shirin 'bata mn suna ba
A kiyaye
Kalisa ce cikin d'akin mahaifiyarsu cikin tsananin kadaici da kewa , bayan tasha kuka ta more , sannan ta zauna kan gado , wata loka dake kusa da gadon ta jawo , haka idanunta suka kai kan wasu takardu
d'ebosu tai kallo guda tai musu ta ji jikinta ya mutu , a sa'ilin data fahimci takardun gidan Hajjiya ne wanda Alaji ya bata , ta mayar ta aje
Wayarta ce ta fara ringin ta dauki wayar ba tare da yanayin ta ya canza ba ta ce ,"My Umar har ka zo."
Umar ya yi ajiyar zuciya yana cewa, "Haba My Kalisa ta ya zan yi wasa da lafiyarki , bayan an ce yau ne dactor zai zo , kawai maza ki fito mu tafi ."
Kalisa ta ce ,"Tom shi ke nan." Ta aje wayar ta fita
tana fita falo ta yi sallama dasu baba anje , suka mata fatan samun lafiya sannan ta fita , tana fita
Umar suka nufi asubitin,sakamakon ba nisa ne dashi ba , a kafa suka isa suna hira .
Doctor jamil ne zaune cikin office dinsa tare da laptop a gabanshi , a lokacin sukai sallama suka shiga . Cikin girmamawa doctor ya tashi ya taro su , sa'ilin da ya basu wajen zama
"Sannunku fa , wato Umar duk an mance damu."
Doctor Jamil ya yi maganar cikin kyakykyawan yanayi
Umar ya mai da masa da cewa ,"Kai fa ka fiye surutu dan Allah haba naga kusan kullum muna gaisawa a online. "
Jamil ya ja tsaki yana kallon Kalisa da cewa ,"Kalisa ya karin hakuri. "?
" Mun gode Allah dactor. " Kalisa ta ba shi amsa
a lokacin wata nurse ta shigo , yayin da Doctor ya kalleta tare da mika mata wata takarda yana cewa,"Ku je tare da Kalisa ai mata wannan gwaje-gwajen , yanzu fa ."
Nurse din ta amsa yayin da Kalisa ta bi bayanta .
Umar suna zaune suna hira ba jimawa Kalisa ta shigo da takardar binciken lafiyar da aka mata.
Ta mikawa dactor sannan ta zauna tana kallon Umar yana mata murmushi.
Bayan dactor ya bude sakamakon ya yi ajiyar zuciya yana kallon Kalisa .Wanda duk hankalinasu ya koma ga dactor Jamil .
A zube min comment a private mu had'u next page.
Share, like and comment.........,
Gubar Rayuwata
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)

Page 19&20
Ba editing
"Wato Kalisa zahirin gaskiya wannan ciwon naki , sai an miki aiki , domin a halin yanzu ma hunhunta ya samu matsala." Ya karasa maganar yana kallon Umar
wani faduwar gaba Umar ya ji ya bigi zuciyarsa ,
"Kuma gaskiya wannan aikin na gaggawa ne , don haka zan yi magana da dactor Aisha dake babban asubiti, zan tura ku can ." Doctor ya kuma fade
Kalisa cikin mutuwar jiki ta kalli Umar tana cewa, "Ka ga ni ko Umar , na kusan mutuwa."
"Haba Kalisa ai cuta ba mutuwa ba ce , an yi wa mutane da yawa aikin kuma sun sami lafiya dan haka kema insha Allah zaki warke , saidai aikin gaskiya akwai kud'i sosai ,duk da nasan baku da matsalar sa ."
Umar ya ce "Yanzu dai yaushe ne za mu je asubitin.".....
Ahmad ne yake wa Zainab fad'a sosai a kan Harun, amma sai kare shi take tana nuna Mahmud ne yake son bata masa suna , Ahmad saida ya matukar yi mata gargadi tare da mata barazanar sanar da Alaji abin dake faruwa duk da hakan dai har zuciyarta bata shirin barin Harun .