Sashe 16
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
yanzu a raye, bayan tsananin da matakin da ciwonta ya haura. "Likita , Likita likita ." Jafar da Nabila suka fita da gudu suna kiran dactor, wasu nurse ne su biyu suka shigo sukayi kan ita Kalisa data sassan kare , Umar ganin bai gamsu da nurse dinta ba fita neman doctor Aisha da gaggawa Aisha ta taho gurin Kalisa, ya yin da taci karo da wannan nurse din su biyu , nan take suka ja baya suka bata guri . "Baba Yaya Kalisa mutuwa za tai." Nabila ta yi maganar tana rushewa da kuka , baba anje bata iya cewa komai ba , domin a yadda take kallon Kalisa yanzu ita ma ta cire rai , domin a halin yanzu numfashi ya gagara , cikin kokari da sanin aiki na dactor Aisha aka sawa Kalisa oxygen machine , wanda daga nan ne aka samu sauki ta koma kamar matacciya . "A gaskiya ku dauketa ku koma gida , tunda har yau fitar da ita ya gagara , nasan halin da kuke ciki , amma hakan ba yana nufin ku zuba idanu ba , domin taya Allah kiyo yafi Allah na nan , ciwonta ya wuce duk yadda kuke tunani , musamman ma cancer dake kafarta wacce take cigaba da yawo." Doctor Aisha ta yi maganar tana kallon kowanne a cikin su . Ba tare data jira wani ya ce komai ba ta fita yayin da wannan nurses din suma suka fita da fatan samun lafiya . Baba Garba ya kalli , baba anje yana cewa "Gaskiya ne wannan, duk abin da yake faruwa daga Allah ne , ya kamata mu tashi zuwa jibi a fitar da Kalisa a samo mata lafiya." Baba anje dai ta kasa cewa komai, sai wani ajiyar zuciya da ta yi mai cike da fargaba tana kallon Kalisa. "Zan je na sayar da gadon gidanmu , amma ba wani kud'i ba ne mai yawa." Umar ya yi maganar yana kallon Baba Garba Baba Garba ya mayar masa da cewa "Ni ma yau zan tafi kauye, zan tattaro duk abin kadara ta da kiyo , a siyar dasu in sha Allah." Ya mike yana cewa "Bari na tafi ba a bori da sanyin jiki , zan kuma tun-tu'bi duk mutanen kirki cikin 'yan uwa zasi wani abun." Ya aje maganar lokacin da yakai kofar fita nan sukai masa sallama da fatan alheri ajiyar zuciya Jafar ya yi tare da kallon can gefe guda idanunsa kamar zai yi kuka, sallamar da aka shigo ana yi ne ya sa ya dawo da kallon sa bakin kofa "Ahh Jibril kai ne." Cewar Umar Jibril ya gaida baba anje ,Wanda nan suma suka sami damar yi masa ta'aziyya ya kalli Kalisa dake kwance da oxygen idanu a rufe yana cewa "Allah ya bata lafiya dan annabi." Duk tare suka amsa da amin , wanda ya kalli Nabila yana sake cewa "Sannu ke ma Nabila, haka Allah yake kudurarsa , amma da wannan azzalumin Sahid ya bada kud'i n nan ai na tabbatar komai zai zo da sauki." "Haka ne ." Jafar ya fada a takaice yana kallon Kalisa yayarshi wacce bata san inda kanta yake ba kwana guda babu abinci. A lokacin Jibril ya kalli Jafar lokaci guda yana had'a kallo da baba anje yana cewa "Sahid jinin mu ne babu yadda muka iya , kuma bamu da bakin ba ku hakuri ku dauki duk matakin da ya dace dashi." Ya ciro wasu makudan kudade daga jikinshi yana ajiyewa gaban baba anje yana cewa "Wannan ku had'a ayi amfani dashi wajen lafiyarta amma babu yawa." "Allah sarki, Allah ya saka muku da alheri." Baba anje ke nan Jafar ya kai ido kan kudaden wanda kallo guda ya musu ya gane dubu dari biyu ne, Sannan shi ma ya mika godiya, shi ma Umar haka ......... Haka har wajen dare Kalisa jiki babu dadi , su ma Umar da Jafar a wannan dare suna ta kokarin samo wannan kud'i, haka bangaren baba garba kowa yana ta kokarin sa . Rayawa da kashewa duk na Allah ne, kuma duk yadda ya yi babu mai tuhuma , amma muna yiwa Kalisa fatan samun lafiya ta dawo kamar yadda take dah. Gubar Rayuwata By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta)