← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 27

Sashe 10

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kalisa har sun je wajen doctor Aisha a yau , nan ta tabbatar musu da dinbin kud'in da aikin zai ci .
Bayan sun dawo gida suka sanar da baba anje komai . Nan akai waya suka sanar da Sahid halin da Kalisa ke ciki ga kuma irin kudaden da ake bukata
Nan ya tabbatar musu ba wata matsala zai turo da kud'in
har yake sanar musu ma zai basu dukiyarsu ta dawo wajensu.
Amma har washe gari shiru , Sahid bai ce komai ba , wayarshi ma a kashe
Jafar ya je companin da Sahid yake aiki amma bai samu ganin shi ba .
A halin yanzu Laila ta sami lafiya, amma har yanzu Barrister Adam bai ce da makarantar DR.DD komai ba
Ansha matukar jinya kuma ana kansha a kan ciwon Laila , barrister yana kashe kud'i sosai
babban abin da ya ke ci masa rai wai Laila 'yarshi za a wa wannan tozarci har hakan ya jawo mata ciwon zuciya.
Rashin sanin irin matakin da zai dauka a kan makarantar ya sa har yanzu bai ce komai a kan lamarin ba .
Su ma malaman makaranta sun shiga rudani , musamman ma shugaban , yarinya ta kamu da ciwon zuciya lokaci guda , to da zuciyar bugawa tai ta mutu fa .
wannan kaddara ce ta shigo masa makaranta, kuma yadda ya biyewa Uncle Yahaya har hakan ta faru .
"Wai Khadija yaushe zaki dawo makaranta". Wata Zainab kawarta ta fad'a
Khadija ta kalleta tana ta'be baki ta ce ," Ni na bar wannan makarantar wallahi, domin dady ma ba zai takurani ba."
Zainab ta ce "To Allah ya kyauta ya bawa Laila lafiya, ni Wallahi ma abin da yake bani mamaki ashe da gaske Laila haka take son Uncle, ki dubi yadda zuciyarta ta so bugawa. ai wallahi Allah zai saka mata."
Khadija da duk kan 'bacin rai ta kalli Zainab ta fara magana, "Ai wallahi Uncle ya yi asara , kuma jira nake kawai dadyn Laila ya yi magana."
Zainab ta ce ,"Allah dai ya kyauta."
Cikin tsananin fad'a baba anje take magana
"Wannan ai wulakanci ne , haka ake yaron nan ya bamu kud'i amma har yau shiru , tun yaushe ake masa magana kuma kullum ciwon Kalisa girma yake."
Umar dake zaune a gefe guda cikin falon ya girgiza kai alamun goyon bayan abin da baba anje take fad'e
Jafar ne ya ce ,"Gaskiya kam dai Sahid bai kyauta ba kaka , to mene abin yi."
Kalisa ta ce ,"Me zai hana muje gidansu yanzu Umar, kasan babanshi abokin dady ne, kuma da zarar mun je zai masa magana. "
Baba anje ta ce "Eh gaskiya ne Umar ku tashi ku je yanzu domin wannan lamarin bana zama ba ne ."
Kalisa cike da kwalla ta kalli baba anje tana cewa ," Muna matukar godiya Baba anje , kina tsayawa da nuna damuwa a kan lamuranmu Allah ya baki.......".
Dakatar da ita tai tana cewa, "Haba Kalisa ai zan tsayawa lamarin ku bakin rai bakin fama ku amana ne gare ni . Tashi ku je kawai a dawo lafiya ."
Umar ya tashi yayin da Kalisa tabi bayanshi , sannan ta juyo ta kalli Jafar tana cewa, "Bari na tafi da mota jafar."
Jafar ya ce "To a dawo lafiya daman akwai mai a ciki ai."
Suka nufi harabar gidan ita da Umar.
Anan kuwa cikin makaranta duk kan malamai sun had'u suna tattaunawa a kan matsalolin makaranta, ana cikin haka wani mutum ya shigo a mashin
guri ya samu ya yi burki sannan ya sauka ya nufi ofishin shugaban makaranta,
ai kuwa duk malamai suna cikin office din
mutumin karasawa ya yi yana gaida shugaba, sannan ya mika masa sako ya fito , bai jira cewar komai ba ya fito ya hau mashin din sa ya tafi .
"Ikon Allah".
wani a cikin malamai ya fad'a, Uncle Yahaya ma yana zaune shugaban makarantar ya bud'e takardar
jin abin da Dr Dauda ya fad'a yasa duk hankalin malaman tashi
Cikin yaren turanci wata malama yare ta ce ," Me ke faruwa sir."
Sauran malaman kunne suka kasa domin jin amsar da zata fito daga gareshi , domin a halin yanzu suma ita ce damuwarsu
Ido ya kafa wa uncle Yahaya cikin tashin hankali, hakan ya sa Uncle tsarguwa yana cewa ,"Shugaba lafiya kuwa."
Cikin zafi shugaban makarantar ya tashi tsaye yana cewa, "Barrister Adam ya shigar damu kotu , wannan takardar tuhuma ce ." Ya karasa maganar yana cillawa Uncle Yahaya takardar
Wani tsoro da mamaki ne ya ziyarci malaman
Dr. Dauda ya zauna yana kifa kansa kasa yana cewa, "Innalillahi, yanzu sunan wannan makarantar zai baci a idon duniya , na tabbatar har mane ma labarai za su yad'a wannan case a labaransu , innalillahi wa Inna.....".
Uncle Sani ya kalli sauran malamai yana cewa," To yanzu mene abin yi , ya kamata a nemi mafita wallahi. "
Dacter ya dago kai yana magana cikin tsafi ,"To yanzu mene mafitar."
Yanayin yadda ya yi maganar suka sha jinin jikinsu , musamman ma Uncle Yahaya.

Tafiya suke cikin mota , Umar yana tu'ka su
kallon Kalisa ya yi yana cewa, "Ki ce dai gidan nasu da nisa. ga shi kauye, to ina zai aje min ke saboda rashin kunya."
Dariya Kalisa tai tana cewa, "Wallahi kuwa da nisa."
Umar ya yi tsaki yana cewa "Ai wallahi ya bani mamaki, dama fa shi dan kauye bai san arziki ba , sai ka yi masa rana ya tashi ya yi maka dare , yanzu ina amfanin wannan, garin nasu duk daji."

Wani gau suka ji wata babbar mota ta bige su , a sa'ilin da sam ba su ganta ba
hakan ya sa motar ta su ta kwace ta nufi daji
"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un, abin da suke fad'a ke nan
Umar ya bude murfin kofa
da nufin su fi ce a irin wannan gudun da motar take " Kalisa fita , fita kar kiji tsoron komai. "
Amma ina Kalisa duk ta rude rigarta ta makale
" Kai ka fita Umar ka fitaaaaaaa". Kalisa ta karasa maganar a yanayin firgici da ta ga sun kusa dukan wani dutse .
Kauuuu motar ta bigi dutse ta tashi sama , a lokacin suka fado kasa dukkansu , yayin da motar ta kama da wuta tun daga saman sannan ta fad'o kasa .
Kalisa ko shurawa ba tai ba
matukin waccen motar yana ganin haka ta faru kawai ya gudu abin sa ya bar su .Duk da shima yaji rauni .
Cikin mummunan yanayi Umar ya tashi kanshi duk jini , yana tashi ya fad'i kasa yaja jikinshi da kyer ya nufi Kalisa.
Yanayin tashin da ya yi mata ya tabbatar masa fa ta mutu bugu da kari wani karfe da ya gani a cikin gwiwarta ya tsagata .
Wani tashin hankali ne ya ziyarce sa ya kwalla ihu yana kiran sunanta da dukkan muryar da Allah ya hore masa.
Share ,like and comment...........
Gubar Rayuwata

By
Fatima Abdallaah kano
( Autar marubuta)

*AUTAR MARUBUTA CE*
__________
_________
__________
_________
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_
<><><
><><><>
<><><>
<><><><>
<><><><><>
<><>

Page 21&22

Cikin tsantsar mazantaaka Umar ya yi jarumta ya nemi mutane
Allah ya taimaa ka wasu mutane suka kawo dauki .Wanda har motar asubiti da 'yan sanda suka karaso
Yadda Umar ya ga an dauki Kalisa ya sake tabbatar masa Kalisa ta tafi ta barshi
Chapter 10 · 0% Book details