Sashe 2
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta). _________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE* __________ _________ __________ _________ _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_ <><>< ><><><> <><><> <><><><> <><><><><> <><> Editing Page 3 & 4 Number ta gani babu suna an rubuta ,"masoyiya ya kike ? ya gida Allah yasa kina lafiya." A zuciyarta tace to waye wannan ni dai nasan ba yaya Mahmud ba ne . Typing ta fara tana mayar masa da cewa ,"lafiya kalau nake amma waye ."? Harun da ganin sakonta ya zabura yana murna ya sake maida mata da cewa, "Bani da suna amma mafi yawanci ana kirana da mai kaunar Zainab." Murmushi tasa da ganin ganin sakon nashi , kafin ta sake turawa ya turo mata cewa,"Mai kaunar Zainab da fatan rayuwa da ita har abada ". Kawai Zainab tai a jiyar zuciya. " Yanzu Uncle tafiya zakai." Laila ta fad'a cikin damuwa Uncle Yahaya ya kalleta yana cewa, "Haba Laila kwana biyu ne fa , ni dai kawai idan na dawo ina san kalamaina masu dad'i." Laila tai murmushi, saida ya sake komawa gidansu ya sake sallama da kakarshi sannan ya tafi. Ita kuwa Laila sai 'ku'kewa take tana had'o masa kalamai. tana cikin yin ne Khadija tazo ta warta, aiko ta bita . Yau ma Sahid yaje gidan Alaji Idris, saidai ita Kalisa har yanzu bata jinshi a zuciyarta, kullum saidai Umar kuma ta'ki fito mana da Umar mu ganshi. Alaji Idris yana cikin a zaune, sai ga Garba nan ya shigo Alaji ya kalleshi yana cewa, "Ahh, haba Garba sai kace ba ka garin , nan da nan baza a ringa zuumunci ba ko na yi laifine." Garba da sauri da Girmamawa ya fara cewa, "Haba Alaji, wallahi babu abin da kai mini , kasan zaman birni , motar tawa ce ta lalace shi yasa ba a ganina har saida aka gyarata." Alaji Idris ya had'e rai yana cewa, "Haba Garba yanzu motar taka ta lalace amma ba za ka sanar dani ba , to mene amfanin ...." Dakatar dashi Garba ya yi yana cewa, "Haba Alaji , Yanzu ni saboda abin kunya da raashin tausayi , motar tawa ta lalace shi ne sai na jira ka gyara mini . To mene amfanin kud'in da nake hayar da ita ." Garba ya sake gyara zama cikin tausayi da girmama Alaji yana cewa, "Haba ! Ai wallahi bazan mance da abin da kai mini ba , ka kawoni birni ka bani sana'a ka ko ya mini zama da mutane, ka se mini..." Alaji Idris ya dakatar dashi yana cewa, "Karna sake jin kana fad'e , to mene 'yan uwanta kar GARBA." Garba yace ,"Gaskiya ne ." Nan dai suka gaggaisa Garba ya koma , domin gidansa yana cikin gidan Alajin daga wajen gefen gate , ya dauko shi daga 'kauye ya ba shi mota ya ara masa gida , domin Garba da Alji Idris 'yan uwa ne , mahaifinsu d'ya wanda yanzu basu da kowa. Ahmad ne zaune kan kujera , Zainab kuma na kwance kan 'kafar yayannata suna hira, hirarsu suke cikin kwanciyar hankali da farin ciki , ga shi kuma anata 'kwad'o sallama amma babu wanda yaji a cikinsu , saida Hajjiya Salima ta fito daga d'akin girki ta tsaya kansu cikin b'acin rai sannan suka san halin da ake ciki , Kafin su ce komai Hajjiya Salima ta je ta b'ud'e kofar Yaya Aminu da Yaya Mahmud ne Hajjiya ta dawo gabansu Ahmad tana cewa, "Kuna ji ana sallama amma kun yi shiru ." Zainab ta tashi kan 'kafar Ahmad yayin da Ahmad yake cewa, "Wallahi momy bamu jisu ba ko kad'an." Mahmud da ke tsaye ya kalli Zainab yana cewa, "Taya za ai kuji , kullum ba ka da aiki sai shagwa'ba wannan yarinyar." Da sauri Ahmad ya cafe yana cewa, "Haba Mahmud kasan bani da kowa , sai ita kawai , ai dole na sota na nuna mata soyayya kafin ta barni , kuma momy ta'ki haifo wasu." Dariya yaya Aminu yasa ya kallon Zainab Hajjiya ce ta kalli Ahmad tana cewa, "To aku , sai kai musu shiru ai su zauna su huta ko ." Duk dariya suka saka yayin dasu Aminu suka zauna . Aminu da Mahmud kamar 'ya'ya suke wajen Alaji Kabiru, domin dukkansu 'ya 'yan kannensa ne da suke zaune a Kaduna, wanda Yanzu sun kawo musu ziyara ne . Aka kawo musu kayan motsa baki masu da kyau suka ci suka sha, yayin da wata iska ke shigarsu suka fara hira. Mahmud ne ya kalli Zainab yana cewa, "Su Zainab'yan mata." Wani kallo ta jefa masa tana cewa, "Uhum." Wayarta ce ta nuna mata alamar sa'ko hakan yasa ta 'bud'e wayar tana karantawa,"Dan Allah my life ki amshi soyayyar da nake miki dan Allah. " Zainab ta mayar masa da , "Bana san zancen banza koma waye kai ka fito fili mana ." Su kam su Aminu hirarsu kawai suke , amma Mahmud rabin hankalinshi yana wajen Zainab da ba ta sauraransu. Harun ya dawo mata da amsa, "Idan kin shirya ina son mu had'u gobe ." "Ina zamu had'u." Ta tura masa . "Gidan abincin dake bayan gidanku da karfe 11na safe." Kawai ajiyar zuciya ta yi ta mi'ke zata shiga d'akin ta, Mahmud ne ya dakatar da ita da kiran sunanta ,"Zainab. " Ta juyo tana kallonsa sannan yace , "Ina son gobe da safe za ki rakani asubiti zan je wani aiki." Tsayawa tai tana cewa, "Gobe kuma da safe." Mahmud yace ,"Eh." Saida ta d'anyi jimmm sannan tace ,"To Allah ya kaimu." Ta shige cikin d'akinta . Yau Alaji Idris shi da Hajjiya Maryam ziyara ya kai wa wani tsohon abokinsa . a hanyar dawowa ne ya kad'e wani yaro wanda yake tafe da kakarshi , aiko hankalin Alaji ya matukar tashi sosai , hakan yasa ya garzaya asubiti da yaron , sai dai ina rai ya yi halinsa domin yaron ya rugamu gidan Gaskiya, Hankalin kowa ya matukar tashi sosai , aiko Alaji Idris ganin cewa wannan tsohuwa bata da gata yasa ya taho da ita gidansa , ta tabbatar musu yaron jikanta ne da iyayensa duk suka rasu , su kad'ai suke zama . Tare da gawar yaron ya taho gidansa , anan akai masa komai aka kaisa makwancinsa. Bayan Uncle Yahaya ya isa legos , sun yi biki , aiko suka ringa yawon bud'e ido da abokansa , a garin yawon ne Allah ya had'ashi da wata karuwa wacce ta manne masa . Yanzu haka yana zaune da wani abokinshi ranshi a matukar 'bace yace , "Ni wallahi Shu'aibu zuwa na legos bai amfane ni da komai ba sai masifa." Shu'aibu ya kalli Uncle Yahaya yana cewa, "Haba !Karka bada maza mana , kawai don yarinya ta mannema shi ne masifa , to wallahi kafin ka tafi ka amince mata kawai inba haka ba Wallahi za kai asara." Cikin haushi Uncle Yahaya ya kalli Shu'aibu yana cewa, "Wai wannan banzar yarinyar , sanin kanka ne karuwa ce , me zan samu a gunta." Dariya Shu'aibu ya kwashe da ita yana cewa, "Wallahi ina ma ni ne , ai ko ita ce zaka samu wani abu agunta kana ganin yarinya cikakkiya , ai wallahi dani take so tuni an wuce gun , kuma wallahi babbar karuwa ce , domin ko kud'in yaharta bani da shi." Dogon tsaki Uncle Yahaya yaja yana cewa, "Dama dai sona take da gaske shi ne , amma kana ji fa , wai gayyatata take na kwana a d'akinta fa." Kafin ya rufe baki ya hangota tana tahowa inda suke kawai Uncle Yahaya ya juyar da kanshi yana tsaki , hakan yasa Shu'aibu kallon inda take yana sakin baki , riga da wando tasa wanda suka kama jikinta sosai , tun daga nesa Shu'aibu yake jin kamar ya rungumota , bari ma lokacin data 'karaso bada ban ya daure ba da Fa'iza taji wani abu ,"Haba Yahaya, sai ne manka nake a cikin garin nan ." Uncle Yahaya ya yi mata shiru ko kallonta bai ba , ta sake cewa, "Na yi maka girki jazo muje ." Kallon wayarta tai dake hannunta sakamakon kiran da ya shigo, Abdul Salim , kawai ta kashe wayar tana cewa, "Da kai fa nake magana Yahaya." Uncle Yahaya yaja dogon tsaki yana cewa, "Ke ni fa babu inda zani , baza ki ta'ba samun abin da ki ke so ba , kawai dan kinga kirjinki dam -dam shi ne za ki tunanin za ki rud'eni." Ya sake jan dogon tsaki ya bar waje , shi kuwa Shu'aibu ya tsaya yana kallonta dama shi ne . Fa'iza cikin ranta tace, "To wallahi matukar na cika karuwai gaske sai na jawo Yahaya jikina, mu zuba mu gani ." A'a ni ko na ce Allah ya ba mai rabo sa'a . Uncle Yahaya a yau ya shirya ya baro legos, lokacin da dare ya yi tazo ta sami Shu'aibu, yake tabbatar mata da Uncle Yahaya ya koma Kano , aiko ta yi takaici , kawai ta amshi numbarsa ta koma. Zainab da Mahmud ne a kan hanyarsu ta zuwa asubiti, Mah.mud ya kalli Zainab wanda duk hankalinta yake kan had'uwarsu da Harun yana cewa, "Kin san wazan dubu ." Zainab tace, "A'a Yaya Mahmud." Mahmud ya jawo hannunta ya ri'ke , hakan yasa Zainab tsayawa tana kallonshi , shi ma ya kalleta yana cewa, "A haka zamu taafi." Tai ajiyar zuciya suka ci gaba da tafiya badan taso ba . Sisters kar a manta comment dina a private za a ajen. Share , like and comment......... Gubar Rayuwata By Fatima Abdallaah kano ( Autar marubuta ) _________________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE* __________ _________ __________ _________ _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_ <><>< ><><><> <><><> <><><><> <><><><><> Page 5&6 Shigarsu asubitin ke nan Mahmud ya saki hannun Zainab yana nuna mata guri yace ta zauna ta jirashi . Tsayawa tai tana kallon shi , yayin dashi kuma ya shige d'akin gwajin cuta mai karya garkuwa jiki , Zainab hankalinta ya sake tashi ta kasa zama tanata sake-sake a ranta har Mahmud ya fito tasha gabansa da sauri tana cewa,