Sashe 15
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana gama maganar ya kashe wayar Tare da dukkan tashin hankali da matukar hanzari duk suka tashi , su baba anje da Garba tare da salati suna kiran sunan Allah suka tashi . Kalisa ma kana iya hangen mummunan tashin hankali a kan idanunta, cikin tsananin ciwo da fargaba tare da tashin hankali gami da juriya ta fara magana. "Mun shiga uku Jafar , ka dubi rayuwar data riskemu a bayansu momy, Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un." Ta karasa maganar cikin ciwo tana Ajiyar zuciya tare da hawaye . Yadda Umar ya kalli masoyiyarshi Kalisa duk wani tausayin ta ya kama shi , duk da bata da lafiya sannan ga baba anje ga Garba, amma tana daukar lamarin 'yan uwanta a kanta .Matsawa ya yi kusa da ita a sa'ilin da yake jin kamar ya sa hannu ya goge hawayen dake gangaro mata kana ya rungumeta ya rarrasheta . Amma ina duk ya kasa ma cewa da ita komai ya juya ya fita. Tun da lamarin ya faru babu wanda ya yi wani yunkuri , domin yadda Kalisa ta damu da lamarin Nabila duk abin sai ya sake d'aga musu hankali. Babu inda kowa ya motsa har dare ya yi , idan ka ga wani a cikinsu ya fita ,to bai wuce ya nuna damuwar shi a waje ba , sannan ya dawo , domin duk dakon kiran kidnappers din suke . Ai kuwa wajen karfe goman dare , sai ga wata sabuwar number ana kiran Jafar, hakan ya sa duk suka mayar da hankali ga kiran, sannan Garba ya ce ya saka a speaker. "Kana jina." Ha kan da aka fad'a ya tabbatar musu muryar wannan azzalumin ce ta d'azu Cikin rawar murya Jafar ya ce "Ina jin ka." "Zuwa gobe na baku, da karfe 4 na yamma, idan baku amsheta ba , zamu hada ta cikin masu bakuntar lahira gobe , Million 3 za ku aiko." Ya kashe wayar daga can bangaren . "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un, yanzu ya zami , kud'in aikin Kalisa ne kawai damu bayan fafutukar da akai aka had'a su , ina zamu sa kanmu Yanzu da Sahid ya bamu kud'i ko million dari ce ai ba wahala za tai fa." Baba anje ta yi maganar tana rushewa da kuka . "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un." Garba ya fad'a yana samun guri ya zauna Cikin rawar murya tare da fargabar abubuwan da suke faruwa Jafar ya ce "Dole a fitar da Kalisa baba Garba, tun da wannan kudin...." Kalisa ce ta dakatar da Jafar cikin ciwo tana cewa "Babu inda zani sai Nabila ta dawo , dukkan abin da aka tara dan zuwa neman lafiya ta ,a halin yanzu Nabila ce mabukaci , ita jini na ce ,dan haka kawai ku karbota Jafar." Ta aje maganar tana wani irin nishi . Baba anje kuka ta sake fashewa dashi tana neman taimakon Allah. Baba Garba ma ya kasa cewa komai , KANO Mahmud ne a zaune a falo kamar kullum, cikin zuciyar shi ya fara tunanin ya kamata ya koma gida, domin wani abokin sa ya tabbatar masa aikin da suka nema koyaushe za a iya kiransu . Zainab ce dake kwas kwas kwas da takalmi ta dawo dashi cikin hayyacinsa .ko kallon inda yake bata yi ba ta wuce ta gabanshi . Ganin suturar dake jikinta ya tabbatar masa fita za tai zama ya gyara yayin da ta kai bakin kofa tana kokarin budewa ya ce "Ina zuwa."? Wani zafin takaici ta ji a ranta " Zan je gidansu wata ne , kuma momy ta sani , ba sai ka tuhume ni ba." Duk jikin Mahmud wani iri ya masa domin ya tabbatar Zainab ba gaskiya ta fad'a masa ba , wajen Harun zata ,haka zuciyar shi ta ba shi. "A dawo lafiya". Abin da ya fada ke nan ya koma ya yi lakaf kamar ya saduda . Hakan ya sa Zainab ta fita Zumbur ya yi ya tashi kamar wanda aka tsikara ya zura wayarshi a aljihu ya fita ya bi bayanta. Yana binta a baya- a baya har tasha kwana ta nufi bayan gidansu , wanda hakan ya tabbatar wa da Mahmud abin da yake tunani, tana tsallaka titi ya ga ta doshi wani babban gidan abinci da hutawa mai suna Shuwa Love , mamaki ne ya sake rufe shi ya ci gaba da binta , wanda harta shiga ciki bata san yana bibiyarta ba . Sahun kujera number ta goma sha bakwai ta hangi Harun yana zaune yana jiranta, hakan ya sa ta nufi wajen shi cikin farin ciki. " Ohh Zainab! Wajen wannan wawan kika sake zuwa ya Allah. " Ya yi maganar cikin tsananin haushi da bacin rai . Daga inda yake labe yake hangosu ya kalli hagu da damar sa , sannan ya nufi inda suke Zainab wani yarrrr take ji duba da yadda Harun yake kallonta kamar mai shirin fada mata kah yana daga zaune "Masoyi wannan wanne irin kallo ne."? Zainab ta tambayi Harun cikin ya'ke tare da murmushi wanda lokaci guda zaka gane duk hankalinta bai kwanta da kallon ba . Ajiyar zuciya ya yi yana kokarin fara magana , sai dai kafin ya kai ga cewa komai Mahmud ya tsaya 'kyem a kansu rike da kugunsa Duk mikewa tsaye sukai suna kallonshi , ba tare da ya bari wani a cikinsu ya ce komai ba , ya fara magana "Sannu ku, ashe nan kika taho." Tare da duk bacin rai Zainab ta fara magana"Wato bibiya ta kake , amma wallahi ka bani kunya , wannan wacce irin. ".. " Shiru mara kunya." Mahmud ya fada cikin zafi da hassala, ni yayanki ne , amma ni kike fadawa wannan maganganun , saboda duk kin ga na zama wani zato . Rashin hankalinki ya wuce tunanina , kwakwalwarki ta dena aiki , kin zabi mutumin da yake da burin kashe ni ." Sauri Harun ya yi ya tari numfashin Mahmud, wanda a wannan lokaci duk mutanen dake zaune a wajen hankalinsu yana wajensu suna ji da kallon hayaniyar tasu . "Ta ya zan kashe ka Mahmud, ai ko ba komai kai abokina ne kuma yayan Zainab, ka dena min kazafi dan baka so na ." Ya yi maganar cikin muryar tausayi da marairaicewa . Hakan ne ya matukar hassala Mahmud, cikin fusata ya yi sauri ya daki kirjin Harun da hannu biyunsa , wanda sai da ya kai kasa har kasan rigarshi ya yage , sakamakon kujerar da ya bige ta rike shi . "Nasan duk abin da kike dan bamu sanar da dady ba ne , kuma wallahi yau sai ya san komai." Mahmud ya fada yana nuna Zainab da yatsa "ka fada mana, ko tsoron hakan nake ka dameni ka ishi Rayuwata, kai azzalumi ne mara tausayi." Wani saukar mari da taji a fuskarta ya sa tai shiru ta rike gurin , tana kallon Mahmud da mamakin ya mare ta . Kafin ta ce komai taji muryar Harun yana cewa "Security ga shi nan." Yana nunawa security na kula da gidan Mahmud. Suka sashi gaba domin ya fita a gurin , kawai kallon Harun ya yi , ya wuce ya fita . Share and comment............................... Gubar Rayuwata By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) No editing _______________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE* __________ _________ __________ _________ _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_ <><>< ><><><> <><><> <><><><> <><><><><> <><> Page 29 & 30 Cikin mummunan 'bacin rai Mahmud ya fito , duk ya rasa mene yake masa dadi , kawai ya nufi gida kanshi tsaye , har ya isa gida yanayin shi bai canza ba , yana shiga falo ya ci karo da Alaji Kabiru shi da Ahmad suna zaune. Yanayin yadda ya musu sallama a ciki ya sa suka tambayi mene yake faruwa . Bai boyewa Alaji komai ba , haka shi ma Ahmad ya sake bada tabbacin abin da Mahmud ya fada . Cikin bacin rai Alaji Kabiru ya kallesu yana cewa "Mutanen banza ku tashi Ku bani guri , duk kunsan da wannan baku fada mini ba saida abin ya kai haka ." Ya karasa maganar lokacin da Hajjiya ta shigo , "A yi hakuri dady , mun yi zaton zata gyara ne ." Mahmud ya bada hakuri. "Zaku bani guri ko sai na ci mutuncinku ." Suka tashi ya yin da kafin su fita suna iya jin karashen maganar tasa "Ta zo ta same ni , ina nan ina zaman jiranta ."... LEGOS Abokan Abdul Salim ne a d'akinshi suna ta shaye shayensu da bushe bushe . Wani daga cikin su da ba ya iya magana sai ya karkata baki ya ce " Kai Abdul yarinyar nan taka fa , naji an ce ta aje kato a gidanta ." Abdul na kokarin jan shisha ya ce "Ai na sani dan uwanta ne , ta fada mini komai." "Kai dama baka da kishi ai koda yake ita karuwa ina ruwanta koma waye." Mari ya ji an d'auke shi dashi , yayin da duk abokan suka razana . "Kar ka kuma kiran matar da zan aura karuwa, da yau a ce Fa'iza ba za ta aure ni ba , sai na wulakantata , amma tana sona, kar na sake ji ." Kowa yasha jinin jikinshi, su abokanshi sun sani sarai ba sanshi take ba , amma sun bari duniya ta fada masa domin ba zai yadda dasu ba . Uncle Yahaya dai asara ta tabbata , ba shi da abin yi , hatta kudin kashewa Fa'iza ke ba shi amma a haka suna shirin yin aure , ba tare da Abdul ya sani ba , Mu je zuwa Fa'iza zancen duniya ba ya buya. ABUJA Har yanzu sai dai saukin Allah, jikinta babu dadi Nabila ce rike da ita tana tsala kukan bakin ciki "Aunty Kalisa wallahi lafiyarki tafi komai a kan mene zaki bari a karbo ni , bayan bama da wasu kudaden , ke ce damuwarmu , amma yanzu bamu da wata dama." Rurutaccen kuka suke yi baki da yansu, sai dai abin da basu sani sani ba a halin yanzu Kalisa bata iya magana. Tsanani ya kai ya wuce tunaninsu , ita kanta dactor Aisha tana mamakin yadda Kalisa ta kai har