Sashe 19
Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
, wanda hakan yake tabbatar musu babu ranta . "Me ki ke nufi ne."? Umar ya sha gabanta yana tambaya a bisa yanayin rashin ganewa " Ku yi hakuri, ta rugamu gidan gaskiya. " Aisha ta fada cikin matukar tausayi tare da fita , waje , fitar ta ke nan Garba ya shigo cikin daki ya ci karo da gawar Kalisa. Kacokan din su suka rufe ta , abin yana dukansu , Nabila ta bude fuskar Kalisa, " Haba dan Allah aunty Kalisa, ke ma kin san a'a ne , mutuwarki tashi kawai." Cikin matukar zautuwa Nabila take jawo Kalisa domin ta tashi . Ganin haka ya sa Jafar ya fara janyeta ta karfi yana kuka . A wannan lokacin Umar Allah ne kawai yasan zuciyar shi , domin kawai wasu hawaye ne suke zubo masa yayin da ya kafa mata idanu. Baba anje kawai sunan Allah take kira jikinta na rawa kamar mai shirin zaucewa . Allah sarki Garba tun da ya yi burki , ya yi mutuwar tsaye ya rungume jakar kud'in da ya zo da ita . "Haka Allah ya kadarto , amma Sahid tabbas ka cutar damu." Umar yake yin maganar lokacin da hawaye suke zuba jikin malullubin da aka rufe Kalisa "Shi ke nan . Kin barni Kalisa, kin tafi inda ba a dawowa." Ya sake fashewa da kuka yana zube gwiwowinsa a kasa cikin karyayyar zuciya. A Wannan lokacin Nabila ta fad'a jikin Kalisa "Haba dan Allah, Haba dan Allah." Tana ta kuka mai gwanin ban tausayin gaske. "Baba ya kamata mu tafi kawai." Jafar tare da dukkan rauni ya kalli Garba ya yi maganar. innalillahi wa inna'ilaihir raji'un. Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un Kowa na haka ne daman sannan mutuwa dole ce ga kowa , kawai kowa da hanyar ajalinsa . Mu dai muna addu'a ya Allah ka kashe mu bisa hanya ta addini, ka jikanmu taji tausanmu ya Allah. Haka suka koma gida ,wanda duk kafin su isa an sanarwa da kowa , domin da zarar wani yaji labarin zai kira ya sanar da wani .Haka suma mutanen kauye , abin ya girgiza su sosai . "'Yar uwata ce fa ita , da farko momy da dady yanzu kuma ita , ban yi tunanin shiga irin wannan yanayi ba , wannan shi ne Guba mafi girma da bazan mance ba a Rayuwata har ranar da Allah zai dauki raina . Allah ya jikanku aunty ku yafe mini." Maganar Nabila ke nan yayin da aka aka fito da gawar Kalisa za a tafi "Nabila ki yi hakuri kina yin salatin annabi, addu'a kawai Kalisa ke so yanzu." Cewar wata baba Ramma da ta zo daga kauye . Nabila dai ba a magana, saima lokacin da aka isa makabarta , Jafar da Umar Abin dai sai mazan wajen da suka gani Allah ya sa mu dace A bangaren Fa'iza kuwa a halin yanzu rayuwata kawai wahala take sha kullum cikin bacin rai da masifa take wa Uncle , fitowar ta daga toilet ke nan ta nufo daki tana shigo wa ta toshe hanci cikin bacin rai tana kallon uncle tana cewa "Haba dan Allah, wannan, wanne irin wulakanci ne , na ce maka duk sanda kaji kashi kana mini magana, amma sai kana yi a kwance kamar wani yaro , to wallahi na gaji , na gaji da wannan masifar gaskiya mwtss." Ta fita cikin bacin rai ta barshi a dakin A jiyar zuciya ya yi yana daga kwance ya fara cewa "Rayuwata ke nan , kasan farkon ka baka san karshe ba , wallahi alhakin Laila Adam ne wannan, alhakin ta ne , in banda haka saurayi kamar ni Yahaya da wannan cutar , Allah ka bani ikon cinye ta ." Kun ji fa uncle, sai yanzu yasan haka . Ita Laila ma a halin yanzu tana makaranta, domin Allah ya bata lafiya . Fa'iza na daga tsakar gida tana tunanin yadda za tai da Uncle ta fara jin sallama. Ranta sake baci ya yi da jin hakan , ba tare da ta yafa komai ba ta fita rai turbine . Koda Abdul ya ganta haka , sai ya tambaya ko lafiya "Ka ga dan Allah mene ya kawo ka Abdul kana bani matsala fa." Ta yi maganar da dukkan d'aga murya tare da fushi mamaki ya rufe Abdul da jin haka "Mene kuma haka ni ne fa Abdul Salim naki , mai shirin zama angonki fa." Fa'iza ta kalleshi da takaici tana cewa "Allah ya sauwake wallahi, ni ba auren ka zan yi ba , ai ba hauka nake ba mwtss." Matukar mamaki ne ya rufe Abdul , yasan Fa'iza ba za ta masa haka ba , hakan ya sa ya maida abin wasa yana cewa "Haba Fa'iza na , a dena wasa mana ." Wata muguwar harara ta buga masa tana cewa "Wasa kuma , aikin banza , ai wallahi banga abin aura a gun ka ba gara ma ka sani." "Okay haka kika ce."? Abdul ya fad'a Fa'iza ta ce " Haka kaji , kuma haka na fad'a." Ya ce "Okay shi ke nan ." Ya kama hanya ya tafi , yayin data samu damar shiga gida Tana shiga gida taci karo da wayarta ta gama ruri sakamakon kiran wata kawarta , wacce take son ta da Abdul wato Zuby wacce tun tuni ta yi aure ta tuba . "Gayyar hauka." Fa'iza ta fad'a yayin da taga ita ce ta kira. Harun ne tsaye kofar gidan malam na lado , wato anguwarsu Zainab ke nan yana tsaye yana jiran fitowar Maryam, a yadda yake yatsine fuska zaka gane cewa almajiran dake kofar gidan suke karatu sun dame shi , lokaci guda kuma yana iya saurara duba ga malam na lado yana cikin gida . Lokacin da Maryam ta sako kai zata fito ya zuba mata idanu kamar kullum , Allah ne yasan karatun kurma , amma zuciyar Harun cike take da sha'awar Maryam tana karasowa kusa da motar shi ya fara tsarata kamar kullum yana shiryata , Allah ma ya sani Maryam ta kamu da son shi , domin tun da aka masa iya ka da Zainab ya dawo wajenta ka'in dana 'in "Gaskiya nifa ina shan kalamai shi ya sa kullum kake sake shiga zuciya ta ." Cikin murya mai dadi Maryam ta yi maganar. "To baby naji , amma yaushe zamu je ki gaida momy , domin kullum maganar ki take fa, Gaskiya ya kamata ki shirya na kaiki ." Ya karasa maganar yana mata wani shegen kallo, lokaci guda kuma yana sauraran jin amsarta." Share and comment..................................... Gubar Rayuwata By Fatima Abdallaah kano ( Autar marubuta) No editing _____________________________________ Page 35 & 36 Kafin Maryam ta kai ga bude baki ta yi magana malam na lado ya fito da babbar riga da hula tare da allo da carbi . Ganin Maryam da Harun tsaye ya nufi wajensu , Harun ya yi saurin kai wa kasa yana gash she shi , bayan sun gaisa yana daga kasa Malam ya fara cewa "Kai ka sanar da iyayenka a zo anema maka aurenta , bana san wasa ." Harun ya ce "To baba in sha Allah zan sanar dasu yau ma kuwa." Malam na lado ya nufi wajen almajiransa ya zauna . Sannan Harun ya tashi yana ajiyar zuciya yana cewa "To kin ji ba , sai ki shirya kin kusa zama amarya." Ya yi maganar yana yatsine fuska , kunya ce ta rufe Maryam da jin hakan "To kinga gaskiya naji dadin jin wanna maganar ta baba , don haka gobe ki shirya zan zo mu tafi shop domin ina son faranta miki baby ." Maryam ta ce "A gaskiya zan fi kowa farin ciki Allah ya kai mu."...... Yau ne aka gudanar da addu'ar bakwai ta Kalisa Duk sun matukar jin jiki wallahi, sun rame kowannensu rashin ne yana matukar taba su , ba a gama nasu Alaji Idris ba , Kalisa ma ta zo ta tafi . To babu yadda aka iya dama kowa na haka ne . Har aka gabatar da addu'ar 40 babu abin da ya canza domin mutuwa mummunan tabo ce , wannan lamarin ya zame musu Gubar Rayuwa babu yadda suka iya. Wani mahaukacin bugun kofa Fa'iza taji ana mata , lokaci guda kuma ana cewa " Kina ina mara mutunci." A yadda taji tabbas ba mutum daya ba ne , ba kuma ta shaida murya ba duk tabi ta rude tana tunanin ita dai batai fad'a da kowa ba , bare a zo kamata , tana yin wannan tunanin ta saka hijab ta fita . Koda ta fita ajiyar zuciya ta yi ganin Abdul ne da abokanshi "Haba dan Allah mene haka." Ta yi maganar tana kallon Abdul da fuskarshi babu wani annuri . Ragowar cigari din dake hannunsa ya jefar tare da take ta , kana yana wasa da makulli da kwadon gida , wanda da gani sabo ne da ke hannunshi yana cewa "Ki tattara kayanki , zamanki ya kare , ki shiga na baki minti biyu ." Wani rass Fa'iza taji a ranta "Haba Abdul lafiya kuma."? Abdul ya kalli abokanshi yana cewa " Ku shiga jiki , domin idan ita ta shiga zata bata mana lokaci, duk ku yo wurgi da kayanta ." Cikin masifa Fa'iza ta fara cewa "Haba Abdul wannan ai cin mutunci ne ." Ba tare da ya saurareta ba ya fara cewa "Duk abin dake cikin gidannan ni na siya , dan haka abin da nasan bani na siya ba , daga akwatinta sai bahon wanka , da tukunya , ku shiga ku fito mata dasu." Babu wata-wata suka shige gidan domin aikatawa Zuciyar Fa'iza kamar ta fashe ta kasa motsi ta kasa cewa komai, tana tsaye taji an wurgo mata takalmi,wanda sai da ya sameta a goshi taji zafi wani takalmi ne mai tsini ruwan zuma ta kalli takalmin ta kau da kai , yayin da tana kau da kai idanunta suka kai inda aka wurgo mata tukunya da soson wanka da baho. Bayan su gama fito mata da kayan suka tsaya carko carko kamar masu shirin dukanta "Ya ka ce mi mata shegen duka mana." Wani a cikinsu ya fada yana kallon Abdul. Abdul ya ce "A'a ku barta kawai , domin duk