← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 27

Sashe 24

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Editing
_________________________________________
Page 41 & 42
Hankalin Harun duk yabi ya tashi
ganin yadda wasu abokanshi da dama an turo musu sakon ni da yake tabbatar zasu tafi training amma shi Harun bai ga wannan sako ba ko tuntuba, hakan ya sa yake bibiyar inda matsalar take .
Anan ma Umar Allah ya ba shi sa'a sai dai ba ya so ya tafi training ba tare da yaga yadda kotu za tai ga Sahid ba ,
sai dai jafar ya tabbatar masa babu abin da zai gagare shi , tun da suna da kwararran lauya , ga kuma baba GARBA shi ma ya zo.
Haka dai Umar ya hakura ya tafi kaduna ba tare da ya so ba.
Maryam ce ta fito da gudu daga daki tana sheka amai , tana gama amai ta malale a wajen tana shure-shure .
Haka cikin gaggawa mahaifiyar ta , ta kira malam na lado suka tafi asubiti.
Yadda alakar Harun da surayya take , lokacin da yake sanar da ita matsalar da ya samu , har an tafi training babu shi , ya roki surayya alfarma data mika takardunshi ga mahaifin ta ambassador, domin ya yi magana da lu'utanal a kan shi.
Haka kuwa aka yi surayya ta karba , domin a halin yanzu ma takardun suna hannun mahaifin ta , amma har yau bai samu damar magana da lu utanal ba .
Allah sarki Maryam, lamarin dai har yanzu babu dadi , malam na lado da babarta sun shiga damuwa , haka dai dactor ya sa akai mata gwaje-gwaje , daga bisani ta samu bacci
Lokacin dasu Hajjiya, matar Alaji Kabiru da zainab suka zo dubata , har suka dawo bata farka ba, Zainab dai ta ji tausayin kawartata tana kuma mata fatan samun lafiya..
Fitowar ambassador ke nan daga gidansu Surayya,
ya hau mota rike da wasu takardu a hannunshi, sannan driver ya ja mota suka tafi .
Ambassador sake kallon wannan takardun na hannunshi ya ke yi , lokaci guda kuma yana sake mamakin yadda saurayin 'yar tashi Harun ya zama mai irin wannan mummunan hali da lu'utanal ya sanar masa.
Wanda lokaci guda yana sake tuna maganar da tafi tsaya masa a rai , da lu'utanal ya fada kamar haka .
"Lokacin da Hauwa ta zo min da zancen, sai da muka bibiyi rayuwar shi , muka tabbatar da zargin da ake masa sannan muka hana shi wannan dama , irin Harun mummunan tashin hankali ne zamansu cikin al'uma, kuma bugu da kari mu kara ba su gwarin gwiwa tare da basu aiki irin na soja , ambassador hakan ba mai faruwa ba ne."
Ambassador ya yi ajiyar zuciya bayan tunanin da ya gama .
Har suka isa cikin gida, ambassador jefi jefi abin yana damunshi , daga karshe yana shiga cikin gidan ya zauna a falo
Yadda matarshi ta ganshi haka , ya sa ta fara tambayar ko lafiya, nan take ya sa ta kira masa surayya.
Bayan surayya ta zo ya mika mata takardun Harun yana cewa
"Ki maza ki kira wannan yaron ki ba shi , kar na sake jin komai daga gare shi , hatta mu'amalar ku na wargaza ta."
Dauuu ta ji gabanta ya fadi
"Rabuwa da Harun kuma yanzu." Surayya ta fad'a a cikin ranta

ta kalli ambassador tana cewa cikin harshen turanci , "Dady me ya sa kuma ? Me yake faruwa."?

Nan take ambassador ya sanar wa da Surayya komai , da irin binciken da lu'utanal sukai a kan shi , har suka haram ta masa aikin soja."

Surayya ta yi matukar mamaki da jin hakan , abin ya matukar d'aure mata kai.

Tashi ta yi ta shiga daki da nufin kiran Harun ,

Amma sai ta fasa , ta kira Hauwa ta ce ta zo tana ji ranta.

Bayan Hauwa ta Harun Surayya ta sanar mata halin da take ciki , nan Hauwa ta sake tabbatar mata da waye Harun, ta tabbatar mata yaudara ce ta kawo shi, babu yadda Surayya ta iya ,

Ta kalli Hauwa tana cewa, "To yanzu mene abin yi Hauwa."

Hauwa ta ce , "Ki kira shi ya zo."

Ko awa daya Harun bai 'ba ta ba ya karaso
Ya shigo yayi parking da motar shi , sannan ya dauki waya ya kira Surayya.
"Ya zo."
Surayya ta yi maganar sa'ilin da ta kashe wayar tana kallon Hauwa.
Hauwa ta ce , "Ta shi mu je."
Surayya ta kwashi takardun suka fita .
Tun da ya hango su ya fara washe baki domin a lissafinsa
Surayya zata gabatar masa da kawarta ne , ya sa suka taho tare .
Suna karasowa Surayya ta sake had'e ranta , ammo sam Harun bai lura da hakan ba, domin yadda ya ga kawartata Hauwa zazzafa ya sa hankalin shi ya koma kanta yana kallonta sama da kasa.
Yadda Surayya ta lura da hakan ya sa ta sake jin tsanarshi ta kuma yadda da abin da aka fada mata.
Lokaci guda ya maida kallon shi ga Surayya yana cewa
"Annurin Rayuwata, barka da fitowa."
Tasssssss Ya ji saukar mari a fuskarshi
Da gigicewa da tsananin jin zafin marin da mamaki ya kalli Surayya , hannun shi dafe a kuncinsa .
Cikin turanci Surayya ta fara magana, "Kalle ni da kyau mayaudari, azzalumi ,na tsaneka Harun ."
Ta d'ago hannunta na hagu da ta rike takardun ta watsa masa
Sannan da yaren Hausa ta cigaba da cewa , "Sai ka kwashe su , kuma kai da aikin soja har abada. Allah ya mana tsari da kai yi waje ."
"Haba Surayya waya shiga tsakaninmu haka , ban yi muki komai ba , amma...."
Kafin ya karasa maganar ta sake shara masa mari tana cewa, "Matukar baka fita a gidan nan ba ka sake magana sai na sa an kulle ka."
Harun matukar mamaki ya rufe shi ya kasa gane dalili, idan ma shi mayaudari ne ta ya ta sani. Abin ya d'aure masa kai sosai.
Ya durkusa ya d'ebi takardunsa ya shiga mota ya tafi .
Surayya ta yi ajiyar zuciya tana kallon Hauwa.
Malam na lado yana Cikin tashin hankali , jikin Maryam babu kyau , gida suka koma sakamakon tabbatarwar likita cewa Maryam tana da ciki , sun shiga tashin hankali sosai
Tana matukar jin jiki sosai ko magana bata iya wa amma haka Malam na lado ya tsaya a kanta yana mata tsawa yana tambayar wanda ya yi mata ciki .
"Maryam yanzu wannan shi ne abin da zaki bar mana , cikin shege gidan malam guda." Mahaifiyar ta ta karasa maganar cikin kuka
"Wallahi kin bamu kunya kin cutar damu."
Maryam cikin radadi tana kuka tana kokarin magana ta fara neman yafiyarsu tana sanar dasu ba ba halinta ba ne ba kuma lefinta ba ne.
"To waye ya yi miki ciki Maryam." ?Malam ya tambaya cikin zafi .
Maryam tana gumi cikin jinya tana kuka ta fada musu yadda Harun ya yaudare ta .
"Lallai wannan yaron baisan gidan da ya zo ba , zan kuwa nuna masa ni Malam na lado malumtata ba a banza take ba."
Cikin huci ya karasa maganar
"Wallahi baba sam ba zan yi abin da zai cutar daku ba , daga karshe ake tabbatar min haka halinshi yake , ya yaudari mata da yawa, dah nasan zanga irin wannan ranar da na kashe kai na kafin ta zo."
Maryam ce ta yi maganar tana kuka , yayin da mahaifinta ya yaji duk tausayinta ya kamashi.
Haka ma mahaifiyarta ita ma ta fashe da kuka tana rarrashin Maryam.
"Allah ka gani na yi kokarin tsare amanar da ka bani ta Maryam, amma ga yadda ka tsaro lamarin ka."
Malam na lado ya fada cikin matukar rauni
Sannan ya kalli Maryam yana cewa, "Shi ya sa naso ya turo iyayensa , amma tabbas na yi sakaci , na yi babban kuskuren da bazan yafe wa kaina ba."
Share and comment...........................

Gubar Rayuwata
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)

Editing
Chapter 24 · 0% Book details