← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 27

Sashe 7

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) *AUTAR MARUBUTA CE* __________ _________ __________ _________ _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_ <><>< ><><><> <><><> <><><><> <><><><><> <><> Editing page 13&14 Hannayena biyu ta rike tana cewa "Tun dazu nake jiranka fa baby sai yanzu." Uncle bata rai ya yi yana cewa, "Me ya sa zaki sa wannan kayan yanzu, kin san dai bana san haka sai da daddare ko." Sakin hannayensa tai ta hardo wuyanshi , yayin da Uncle Yahaya ya ke sake kallon cikin jikinta yana ajiyar zuciya. " "Nasan kana jin yunwa muje mi wanka sannan muci abinci." Duk uncle ya kasa cewa komai kawai kallonta yake ...... kakartashi ma a halin yanzu bata da lafiya ga gidan ba kowa . Anan gidan Alaji Kabiru Zainab na falo a zaune , a lokacin Mahmud ya shigo yana kallonta kujerar da take zaune shi ma ya zauna yana cewa, "kawo mini ruwa Zainab." Ta tashi ta kawo kamar yadda ya ce tana mika masa tai hanyar d'akinta "Ina zaki zo mana." Ta juyo tana cewa, "Uhum." Murmushi ya yi mata yana cewa, "Gobe ina san zamu fita." Tasa kai tana cewa, "Allah ya kaimu ." "Kaii! Lallai ma yarinyar nan ba komai." Ya girgiza kai wayarshi ya ciro a aljihu ya nufi numbar Hauwa "Bari na kira yarinyar nan mu gaisa." Mahmud ya yi maganar yana danna kiran har ta tsinke ba a da ga ba , ya sake kira amma shiru wayar ya aje a gefenshi tare da cewa "Ai shi ke nan ." Ya kashe kujerar ya kwanta , wajen wucewar minutes 3 sai ka kira ya shigo masa , ba wata-wata ya daukin kiran "Hello 'yan mata ya kike ya gida."? Cikin muryar rashin sanin waye Hauwa ta ba shi amsa jin hakan ya sa Mahmud cewa ," Kamar baki gane waye ba KO."? Murmushi tai tana cewa, "Eh gaskiya ban gane waye ba." "To Mahmud ne." Ya fad'a kai tsaye dariya ta saki tana cewa, "Gaskiya ne wallahi ban dauki murya ba , ya kake ya gidan ya su momy."? Mahmud ya bata amsa cikin girmamawa nan su ka yi hirar da bata kai minutes 6 ba sukai sallama da juna . Yayin da Mahmud ya fara bacci bisa kujerar da ya kwanta. Tun tuni su Alaji Idris sun baro kauye sun nufo hanyar gida....... Wayar Kalisa ce ta fara ruri , hakan ya sa baba anje dake kusa da wayar tana caji ta fara kiran sunan Kalisa kafin ta iso kiran ya yanke, " Kaiii ai dady ne ya kira." Ta yi maganar tana kokarin bin kiran , sai dai kafin ta kira ya sake kira "Gaskiya aunty Kalisa girkin nan ya yi dadi." Nabila ta shigo falon tana fad'a Jafar ya harareta yana cewa, "Wannan wanne irin abinci ne tun d'azu ba a gama ba." Kalisa ta kara wayar a kunnenta tana cewa, "Hello dady har kun dawo."? Wata kakkausar murya taji tana cewa,"ke ce Kalisa."? Jin hakan ya sa duk hankalinta ya tashi " Eh ni ce ina dadyna fa." Daga can bangaren aka sake fadin ,"Sun sami accident, yanzu haka suna asubitin dake Kuje Abuja." Wani mummunan faduwar gaba taji tare da mugun jiri ya ziyarceta ta sullubar da wayar cikin mugun yanayi Duk su baba anje suka yo kanta tare da matukar damuwa da tambayoyi Daurewa tai ta basu amsa da cewa "Su momy ne sukai accident, suna Kuje hospital." Idanunta matukar ruwa suka kawo , yayin da ita Nabila ma ta bud'e bakin kuka . Jafar bai ce komai ba kawai tsaye ya yi ya kasa motsi Baba anje cikin tashin hankali ta ce da Jafar , "Jeka sanarwa Garba , ya zo yanzu mu je musan halin da suke ciki." Jafar ya fita da ker ya shiga gidan Garba , aiko yana sanar masa ya fito cikin tashin hankali, duk suka rankaya suka nufi asubitin Bayan sun je asubiti, suka sami doctor suke sanar dashi akwai wanda aka kawo sun yi accident likitan cikin far a ya kalli nurse din dake gefenshi sannan ya kallesu yana cewa, "Ai karku damu mun yi musu aiki nan da anjuma zaku gansu." "Alhamdulillah." Garba ya fad'afad'a Nurse din ce ta kalli doctor tana cewa, "Dactor ina tunanin fa , wanda aka yiwa aiki , ba su ne 'yan uwansu ba , kuma accident biyu ne ya faru yau wanda muka ansa a nan." Wani firgici suka sake shiga dajin batun nurse Likitan ya cire tabarau din sa yana cewa cikin turanci ,"Haka ne ." Ya kalli Garba ya ce ,"ku ne masu mata biyu.? wanda aka yiwa aiki. "? Cikin gagarumin matsanaicin kuka Kalisa ta ce ," No dactor mu fa kiranmu akai d'azu." Likitan ya maida gilashinsa yana cewa "Okay sorry, police ne suka kira ku , ina mai baku hakuri, ku je mutuware." Yana gama magana ya wuce Tashin hankali Mutuwaren suka ne ma cikin mummunan yanayi , suna isa suka tarar da police men . "Wai da gaske sun mutu." GARBA ya tambayi daya daga cikin police din cikin tashin hankali nan aka tabbatar musu duk sun ruga mu gidan gaskiya har driver. Nan ne fa wani kuka da zaucewa ya same su , "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'u, la'ila ha illallah...." Nabila tana fad'e cikin tashin hankali Jafar ya kalli yayarshi Kalisa dake tsaye tana kallon gawarsu kawai yaji wani kuka ya kuf ce masa ya fadi kasa yana kiran sunan Allah a sannan Kalisa ita ma ta sake fashewa da kuka ta nufi gawawwakin tana cewa ,"Kun gani momy , ku dubi Nabila da Jafar irin halin da suka shiga , ko dan haka karku mutu , ba dan ni ba , momy dan Allah wannan wacce irin mutuwa ce." Ta kwanta jikin Alaji Idris tana kuka baba anje gefe taja tana salati,tana kuka har da majina Garba kuwa Allah ya kawo masa dakewa a halin yanzu amma yana matukar tashin hankali kallon su ya yi yana cewa, "Ku yi kuka wallahi, ku yi kuka , Allah ya kawo mana jaraba." Idanunshi sun yi jajir mota suka hau tare da su domin zuwa ai musu suttura ana cikin motar ana tafiya, Garba ya ciro wayarshi ya fara sanar da mutane lokacin da ya zo kan numbar malam Shehu ya fashe da kuka yana cewa, "Yanzu su Alaji sun baro kauye lafiya, Yanzu kuma na sanar musu da mutuwarsa, innalillahi wa Inna ilaihir raji'un." Wayar ta zame a hannunshi tai kasa ya cigaba da kuka , hakan ya sanar da malam Shehu nan shi ma ya rikice ya kid'ime da jin zancen, shi ma ya sanarwa da sauran mutane ai kuwa kafin ka ce komai su ka yo zuga suka taho cikin jimami . Bayan an isa gida babu abin da ya canza na tashin hankali haka akai musu wanka , tare da dukkan abin da addini ya tanadarwa mamaci sannan aka kaisu ,wajejen magariba. Allah ya sa mu dace . Bayan idar da sallar magariba, Mahmud yana zaune yana jiran dawowar Ahmad mota yaji daga can harabar gidan, hakan ya sa ya yi sauri ya fito " Me zan gani"? Mahmud ya tambayi kanshi cikin tsananin fusata Harun ne ya fito daga motarshi yana murmushi ga Mahmud, hakan ya sake hassala Mahmud ya nufi wajen shi "Gurin wa ka zo a nan gidan? , na ce gurin waye."? Ya yi maganar cikin huci yana niyyar naushinsa cikin gadara da isa da samun guri Harun ya ce ," A'a gurin budurwata na zo mana Zainab. " Hannu Mahmud ya kai jikinsa ya sha'ke wuyansa ,"Harun zan kashe ka , ka fita daga rayuwar Zainab, ba irinka ba ce , ka lalata mini Asma'u , Zainab kuma kanwata ce ka rabu da ita Harun, wallahi ba zan barka haka kawai ba." "Kamar ya , Yaya Mahmud mene haka , ka sake shi." Zainab ta karaso tana fad'a cikin bakin ciki Mahmud ya kalli Zainab yana cewa, " Me ya sa haka Zainab, karki fad'a tarkon sa , Harun mayaudari ne , azzalumi mara tausayi , shi ne wanda ya lalata mini Asma'u." Ya aje maganar yana huci "Harun mutumin kirki ne , ba shi da wani aibu , kawai kana kishi dashi ne." Zainab ta aje maganar cikin 'bacin rai da jin haushin Mahmud. Ina jiran comment a private mara adadi fa saina jiku Share and comment and like.......... Gubar Rayuwata By Fatima Abdallaah kano (Autar marubuta) *AUTAR MARUBUTA CE* __________ _________ __________ _________ _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_ <><>< ><><><> <><><> <><><><> <><><><><> <><> page 15& 16 Wani abu Mahmud yaji ya tokare masa zuciya hakan ya sa duk ya rasa kalaman bakinsa Cikin nutsuwa da sanyin murya ya fara cewa ,"Kishi kuma , Harun Guba ne mai girma , yana da illa , Zainab karshen magana manemin maza ne ." Da sauri Zainab ta kalli Harun cikin tashin fahimtar abin da Mahmud yake fad'a hakan ya sa Harun saurin faraiwa Zainab magana ,"Wannan ba gaskiya ba ne Zainab, Mahmud ka ji tsoron Allah mene na tare maka." Wani bacin rai ne ya tokare Mahmud "Minutes biyu na baka , ka fita daga gidan nan , karka sake kula Zainab ka fita daga rayuwar Zainab." "Dakata yaya Mahmud, ba ruwanka dani , ni shi nake so , ai ba haka ya kamata ka nuna kishinka ba , kuma dan kana yayana baka da wannan damar a Rayuwata." Zainab ta fad'a cikin bacin rai Cikin mamaki da takaicin kalamanta ya fara magana "Matsayina ya wuce haka a rayuwarki, kuma ban damu da gun uban wa ya zo ba , dole ya fita yanzu, kuma ko ba komai ni na isa nayi hukunci a gidan nan ." Ya koma ya kalli Harun yana cewa, "Minutes daya na baka , wallahi idan baka fita ba sai na fasa motarka." Harun yanayin Mahmud ya razana shi , hakan ya sa ya hau mota ya fita , Zainab na kiranshi . Bayan Ahmad ya dawo Mahmud ya sanar dashi komai , tun daga Asma'u har ranar yau . Ahmad ya ce ,"Ni wallahi na yi zaton ya canja halinsa
Chapter 7 · 0% Book details