← Book details Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 27

Sashe 6

Gubar Rayuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

By

Fatima Abdallaah kano
( Autar marubuta )

*AUTAR MARUBUTA CE*
__________
_________
__________
_________
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_
<><><
><><><>
<><><>
<><><><>
<><><><><>
<><>
Page 11&12
Zainab ganin yadda kallon ya mata
auyi , ya sa ta ta fara tsarguwa , ta kasa zama daidai .
"Harun lafiya kuwa kake mini irin wannan kallon."
Murmushi ya yi mara kunyan yana cewa, "Haba Zainab akwai abin da nake son sanar dake ."
Zainab murmushi ta yi tare da gyara zaman mayafin dake jikinta tana cewa, "To ka fad'a mini mana baby."
"Tom fatan kin shirya ji domin kalmar tana da zafi."
"Zafi kuma."
Zainab ta fad'a cikin mamaki
"Ina san ki."
Zainab ta kau da kai tana dariya
yayin da Harun ya ce ,"Ba fa abin dariya ba ne , Ina jin san ki a raina kamar zai fasa zuciya ta ya fito , Ina kaunar ki da dukkan yakini da sadaukarwa, fatan zan same ki cikin girmama soyayya ta da bata kulawa."
Ya karasa maganar yana duban cikin idanunta
"Ni ma ina san ka Harun , soyayyar da uwa takewa yaronta , soyayyar da bata da karshe kuma bata da misali , domin kai din Rayuwata ne ."
Murmushin farin ciki ya yi da jin wannan batun na Zainab
hakan ya sa ya fara fadin , "Gaskiya naji dadi Zainab amma ina mai sanar dake cewa Gobe zan yi tafiya zuwa gida wato garin Tiga zan gaida iyayena, domin fa kinsan anan gidan kanin ummanmu nake."
Murmushi ta yi Zainab da ya matukar kara fito da kyanta tana ce masa , "Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya , a kuma gashshemin da Umma ta."
"Karki damu my baby za su ji gaisuwarki Sarauniyar soja."
Ya yi maganar yana sara mata , ita kam ta yi masa dariya
Bayan malamin lissafi ya fita daga ajinsu Khadija
Ajin ya rufe da surutu yayin da wasu suke yin bitar lissafin
Laila ko rubutun ma batai ba ta yi tagumi idanunta sun kawo ruwa
Khadija ce ta dungureta tare da cewa ,"Haba Laila Adam mene yake damunki ne ."
Laila ta kalli Khadija tana cewa, "Wallahi ke ma kinsan Uncle ne , wallahi ina son shi , amma yanzu duk ba ya kulani , ko gani na ba ya yi , so yake ya juya mini baya , wallahi ina san uncle Khadija."
Khadija ta ce ,"Kuma babu abin da kika yi masa ."
Laila ta ce ,"Babu abin da nai masa Khadija, duk fa ya juyan baya."
Khadija ta ce ,"To ki bari anjuma ki same shi mana ."
Laila cikin fushi da bacin rai tace wallahi ko ganina fa ba ya san yi ."
Khadija ta ce ,"Tabbb ki ce dai akwai matsala. "
Yanzu dai Uncle Yahaya ko d'ar ba ya ji idan zai tafi hotel wajen Fa'iza
Domin kafin ya tafi makaranta ma ya sanar da kakarshi cewa ba zai kwana a gida ba yau , domin akwai aikin da zai , haka ta yi masa addu'a tare da fatan alheri....
Duk iyalan Alaji Idris zaune suke suna karyawa cikin farin ciki , domin Allah ya sauki Alaji Idris lafiya ya kammala azumi
wajen kwana uku ke nan
"Hajjiya kin san yau ne fa zami tafiyar nan zuwa kauye , da safiyar nan zamu tafi domin kinsan gari ne mai nisa kuma hanyar ba kyau ne da ita ba ."
Hajjiya Maryam ta ce ,"Alaji ke nan , ai na fika zumudi , domin tun dazu nasa Musa driver ya wanke mota , kuma ya zuba duk kayan abincin da za a kai musu."
Alaji Idris ya yi dariya yana cewa, "Eh lallai ki ce abin na yi ne , amma baba anje ba za ki ba ne ."?
Hajjiya tayi dariya tana cewa" Tabb ka ji Alaji da zance , baba mai jikin tsufa ina zata wannan garin , ai kam tayi zazzabi."
Dariya baba anje ta yi tana cewa, "Gaskiya kam ku je Allah ya dawo daku lafiya , ina nan dasu Nabila."
Jafar ya ce ,"Ai ko dai baba ki yi zamanki wannan garin ba abin zuwa ba ne kuma kauye ne."
"Ka ci gidan ku. Ina ce dangin ku ne ." Hajjiya ta yi maganar
Kalisa ce ta zumburo baki tana cewa, "Ni dai ina san zuwa momy."
Hajjiya ta ce ,"Ai na sani Kalisa danta Jafar da Nabila baza ai zumunci ba .
Alaji Idris ya mike da cewa ,"Hajjiya ki tashi mu shirya ina san har na dawo naje office. "
Ya shige ciki .
Bayan duk sun shirya suka fito harabar gidan
Duk suna musu a dawo lafiya
"Baba dan Allah karki bari yarannan su fita yawo , a kula dasu."
Hajjiya tai maganar cikin girmamawa tare da shigewa cikin mota
Sukai sallama suka tafi
yayin dasu kuma suka koma gida
Bayan wajen minti goma da fitarsu , sai ga GARBA ya shigo
Suke tabbatar masa Alaji sun tafi kauye
Garba ya koma yana takaicin rashin ganinsu domin ya basu sako zuwa wajen Shehu .
Bayan sun fito break Laila ta nufi staff don ganin uncle Yahaya
aiko yana zaune suna hira da wasu tsurarun malaman wanda duk kusan sa'anninshi ne
yana ganin Laila ta shigo ya had'e rai , hakan ya sa Laila Adam tasha jinin jikinta da 'ker ta karasa wajen shi ta tsuguna
Tun kafin ta kawowa ranta ta yadda za ta masa magana taji yana cewa, "Tashi ki tafi baki ganni da malamai ba ne."
Sau dubu nawa yake kiranta a gaban malamai ,amma yau yake wannan maganar, abin da ya zo mata kai ke nan
Cikin nutsuwa ta kalli cikin idanunshi da fuskar maraici ta fara magana da turanci ."Uncle dan Allah, wallahi na matukar damuwa da kai , mene na yi maka ."
Uncle Yahaya ya tashi ya fita waje
wani abu taji ya turnuke mata zuciya ta kalli sauran malaman wanda duk hankalinsu ba ya kanta , sannan ta tashi ta fita
Uncle yana can gefe yana waya ga dukkan alamu koma wayar me yake da mace yake yi
Laila ta sawa zuciyar ta wannan maganar
zafafan hawaye ne suka zubo mata , hakan ya sa ta kasa daurewa ta nufi aji tana kuka , kafin ta karasa ta ci karo da Khadija
"Mene ya faru kuma".? Khadija tai tambayar tana jawota jikinta
cikin kuka Laila ta fara magana ," Khadija kin san ya nake son uncle kuwa , me ya sa yake min haka , ni ce fa Lailanshi , wallahi zuciya ta zata buga a kan shi , zan tarwatsa zuciya ta idan ya rabu dani. "
Duk d'alubai sai hankalinsu ya fara yowa kansu
"Mene yake damun Laila?
waye ya dake ta?
Me ya faru ?...."
Sunata tambaya da turanci yayin da wasu suke yin Hausa
Khadija ta kallesu tare da basu amsa guda cikin yaren Hausa "Bata ta lafiya ne."
Suka mata fatan lafiya wasu suka bar wajen , Khadija ta ja Laila suka koma aji
"Wata kila fa Uncle wannan kalaman naki ne basi masa ba."
Khadija ta fad'a
Laila da idanun kuka tace ,"To ai sai ya fad'a mini ko , zan yi wa Uncle kalaman da ban taba yi masa ba na ba shi , matukar bai dawo yadda yake ba to ya dena sona, kuma Khadija ciwo ne zai kashe ni."
Khadija tai ajiyar zuciya tana takaici .
Kalisa da Nabila ne suke girki yayin da baba anje take daki shi kuma Jafar yana falo
"Aunty tin d'
zu gabana yake fad'uwa wallahi."
Nabila ta yi maganar
Kalisa ba tare da tace mata komai ba ta nufi wayarta sakamakon kiran Umar da ya shigo .
Saukarsu Alaji Idris cikin kauyen driver ya fito da kayan abincin yana shiga dasu cikin babban gidan .
Sai ga yaran gari riiiiiiii sun nufo Alaji domin basu dari bibbiyun da ya saba basu duk zuwa , aiko sai da ya sallami kowanne yaro , sannan ya samu nutsuwa
Malam Shehu ya yi musu jagora cikin mutunci da tarbar arziki zuwa cikin gidan , kowa kuma sai murna , kafin ka ce komai a kawo musu nau'ikan abinci daga kowanne sashi na gidan , dambu fate , dashishi, dahuwa, da dai sauran su da dama sun ci sunsha sosai kafin matan gidan Alaji ya sallamesu
sun yi matukar farin ciki .
Uncle Yahaya ana tashi daga makaranta ya wuce wajen Fa'iza
Zaune take cikin wata mara kunyar doguwar riga fara shara-shara , bayan wannan rigar jikinta babu komai data sanya domin kana hango dukkan surar jikinta , bayan ma dai Fa'iza karuwa ce to 'yar iska ce ta gaske
waya take yi da wata kawarta ," Aisha ya kike so na yi da Abdul ne dan Allah, ni fa wallahi bazan aure shi ba ai na fado."
Fa'iza tai maganar cikin fada
hakan ya hassala Aisha ta fara cewa ,"Sannu sara ,idan banda Abdul Salim wane yake sonki da gaske, to kuwa wallahi sai ki dena ci masa kudi , ki fada masa gaskiya, ai wallahi ma shi ne zai rufa muki asiri , to wallahi kiji tsoron Allah kiyi aure , ni yanzu tunda na samu masoyin gaskiya nayi aurena ba abin dana rasa."
Fa'iza ta ce "Ke ni zan kashe waya ai gobe zan dawo." Ta kashe wayar tana tsaki
A lokacin Uncle Yahaya ya turo kofa ya shigo
Fa'iza ta mike domin taro shi ."
Share, like and comment..............
Gubar Rayuwata
By
Chapter 6 · 0% Book details